Amsoshin sakonnin masu karatu (5)

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah Ya albarkaci zuriya da karin basira.  Rokona shi ne: da fatan za ka tattara dukkan kasidun da ka gabatar a kundin littafi na musamman don amfanin masu karatu.  – Jamilu Aliyu, Lafiya, Nassarawa: 08036927722Wa alaikumussalam, Malam Jamilu na gode da addu’o’i, Allah saka da alheri. A halin yanzu dai akwai […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (5)

Cibiyoyi masu taimaka wa kamfanonin sadarwa yada tsarin sadarwarAssalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah Ya albarkaci zuriya da karin basira.  Rokona shi ne: da fatan za ka tattara dukkan kasidun da ka gabatar a kundin littafi na musamman don amfanin masu karatu.  – Jamilu Aliyu, Lafiya, Nassarawa: 08036927722
Wa alaikumussalam, Malam Jamilu na gode da addu’o’i, Allah saka da alheri. A halin yanzu dai akwai kundin dukkan kasidun a shafinmu da ke Intanet, wanda adireshinsa ke saman wannan shafi. Dangane da abin da ya shafi buga littafi na musamman kuma sai nan tunani kan haka zai tsayu. Allah sa mu dace baki daya, amin.
Baban Sadik ya damina?  Shin, akwai wata illa ga lafiyar masu makwabtaka da tushen na’urar da ke janyo yanayin sadarwa na kamfanin NITEL (ko MTN) ne, musamman ga mata masu juna biyu da kananan yara?  –  Ali Fancy, Garko, Kano: 08111740080
Malam Ali Fancy, wadannan cibiyoyi masu taimaka wa kamfanonin sadarwa yada tsarin sadarwar kamfanin wayarsu sun kasu kashi biyu ne: akwai na farko, wadda ke janyo tsarin sadarwar, wadda ke yada maganadisun sadarwar rediyo, wato “Radio Wabes.”  Wannan nau’i shi ne wanda aka ce yana taimakawa wajen yada cutar sankara (cancer), saboda maganadisun lankarki na rediyo da yake bazawa a muhallin da yake, wato “Electromagnetic Radiation.”  Ire-iren wadannan, galibi ba a dirke su a cikin unguwa ko gari ko maraya, sai dai a bayan gari, ko a saman tsaunuka, kusa da unguwa ko gari ko mahallin da ake so su samu wannan tsarin sadarwa na wayar salula. Wannan ya sa ba a ajiye shi a kusa da jama’a.  Kuma aikin hukumar sadarwar kowace kasa ne ta rika lura da inda kamfanonin sadarwar wayar salula ke ajiye ire-iren wadannan cibiyoyi. Shi ya sa ma yana daga cikin ka’ida, dole sai da wani jami’in Hukumar Sadarwa ta kasa (kamar National Communication Commission, a Najeriya misali) kafin a dirke cibiyar a ko’ina ne.
Na biyun kuma shi ne wanda aikinsa bai wuce yadawa ko baza wannan tsarin sadarwa, don hana shi cushewa a bangare daya. A wasu lokuta a unguwa ko gari, za ka ga wani bangare ya fi wani bangaren garin daidaituwar tsarin sadarwa. Idan haka ta kasance, alama ce da ke nuna cewa akwai matsalar cushewar tsarin sadarwa a wani bangaren garin ko unguwar.  Irin wannan cibiyar sadarwar ita ce za ka gani a girke a unguwanni misali.  Shi wannan, a cewar masana, ba ya haddasa wata matsala ga lafiyar mazauna wannan wuri.  Domin aikinsa shi ne yadawa ko baza tsarin sadarwar, ba wai ya janyo shi ta amfani da sinadaran maganadisun lantarki ba.  Shi ya sa suke kiransa “Cell Signal Booster.”  Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Abba, barka da kokari. Tambayata ita ce: yaya zan yi in mayar da sakonnin tes da aka aiko mini zuwa ma’adanar katin SD, wato “SD Card” ko “Memory Card?”  –  Abu Ja’afar, Usman Ibrahim Nadabo, kankara: 07068353836
Wa alaikumussalam, barka dai Baban Ja’afar. Ya danganci irin wayar da kake amfani da ita.  Idan Nokia ce sai dai ka yi amfani da masarrafar Nokia PC, wacce ke taimakawa wajen adana dukkan bayanan mai waya daga wayar zuwa kwamfutarsa ko wata ma’adana.  Idan kuma waya mai dauke da babbar manhajar Android ce, sai ka samu wata masarrafa (Application) na musamman don yin hakan. Daga cikin manhajojin da ke taimakawa wajen yin hakan a saukake akwai masarrafar kamfanin Middle Idea Studio mai suna “Super Backup,” wacce za ka iya samu a cibiyar masarrafai da ke wayar, wato: “Google Marketplace” da kowace wayar Android ke zuwa da ita.  In ba haka ba, da wahala a samu wayar dabke iya bayar da damar kwashe sakonnin tes daga waya zuwa katin ma’adana cikin sauki. Abin da galibi ake iya yi cikin sauki shi ne kwashe lambobin waya daga ma’adanar wayar zuwa katin SIM ko katin ma’adana, wato “Memory Card.”  Sai a gwada a gani. Da fatan dan bayanin da na yi zai gamsar.
Assalamu Alaikum Baban Sadik, a gaskiya muna godiya da irin wannan fadakarwa da kake yi mana a kan hanyoyin sadarwa.  A gaskiya, sai dai mu yi ta yi maka fatar alheri; Allah Ya kara maka lafiya.  Sannan kuma wannan shi ne sakon farko da na taba aikowa, duk da cewa na fi shekara ina bibiyar wannan shafin, sai dai ban samu damar aiko maka sako ba sai yau.  Don haka Allah Ya saka da alheri.  Sai ka ji ni da tambayoyina nan gaba.  –  Usman, Gumel, Jigawa: 08055762828
Wa alaikumus salam, Malam Usman barka ka dai. Na gode matuka da wannan sako naka. Allah saka da alheri, kuma ina sauraron sakonninka na tambayoyi. Allah sa mu dace baki daya, amin.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki?  Allah Ya taimaka, amin. Don Allah ina son a yi min bayani ne kan kayayyakin lantarki masu amfani da fasahar Android, musamman wayoyi; meye amfaninta ne a cikinsu?  –  Mu’azu Funtua, Katsina: 08106067660
Wa alaikumus salam, Malam Mu’azu barka dai. Kalmar “Android” na ishara ne zuwa ga babbar manhajar wayar salula na kamfanin Google da ke taimaka wa wayar salula aiwatar da aikin da duk mai waya ke son ya yi da ita.  Wadannan aikace-aikace sun hada da: kunnawa da kashewa; da kira da amsa kira; da aikawa da karbar sakonnin tes; da rubutawa da goge sakonnin tes; da taskance bayanai na murya, da rubutu da hoto da kuma hoto mai motsi, wato bidiyo.  Bayan haka, wayar salula ce kadai ke amfani da wannan babbar manhaja ta Android. Nan gaba ake sa ran bayyanar kwamfutar tafi-da-gidanka mai dauke wannan babbar manhaja.  Da fatar ka gamsu.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, akwai wata kasida da ka taba rubutawa wajen shekaru biyu da suka gabata, wacce ke magana kan halittar sama da kasa kamar yadda Allah Ya fada a kur’ani da kuma na Malaman Kimiyya.  In da hali don Allah a turo mini da kasidar ta wannan adireshin nawa: [email protected].  –  Mujaahid Naseer Kudan: 07035311650
Wa alaikumus salaam, barka dai. Sai ka duba jakar Imel dinka, na turo maka kasidar. Allah amfanar da mu baki daya, amin.
Assalaamu alaikum Abban Sadik, yaya kokari?  Allah Ya kara maka basira, amin.  Tambayata ita ce: mece ce cikakkiyar ma’anar wadannan haruffa?: CNN, da WWW, da IRS, da PIN?  Allah Ya ba ka ikon amsawa, amin.  –  Rahinat, Kano: 08107370941
Wa alaikumus salam, da fatan ana lafiya.  Haruffan CNN cikakkiyar lafazin shi ne: Cable News Network.  Haruffan WWW kuma na ishara ne ga World Wide Web.  Haruffan IRS kuma haruffa ne da ke nufin abubuwa da yawa, amma wanda ya fi kusanci da harkar kimiyyar sadarwar zamani shi ne: Information Retriebal System.  Haruffan PIN kuma na ishara ne ga Personal Identification Number.  Da fatan kin gamsu.
Assalaamu Alaikum Baban Sadikk, da fatan alheri mai yawa a gare ka. Me ya sa iska da ruwa mai iska da ake yi suke da sunannaki.  Kuma yaya ake bambance su, misali: Tornado, Katrina, Rita, Wilma, da sauransu?  Don Allah ina bukatar bayani.  –  Ummu Haidar, Gombe
Wa alaikumus salam, a gaida Ummu Haidar, da fatan ana lafiya.  Wadannan sunaye da kike ji da gani, sunaye ne da Malaman kimiyya masu bincike suke bai wa nau’ukan guguwa ko mahaukaciyar iska da ta taba samuwa a wasu sasannin duniya.  Kalmar “Tornado” dai wata irin mahaukaciyar guguwa ce mai da’ira daga fuskar kasa har ta kere zuwa gira-gizai, da karfi.  Sauran sunayen da kika ambata kuma nau’ukan irin wannan iska ne da suka taba faruwa a wurare daban-daban.  Malaman kimiyya kan ba su sunaye ne don tantancewa a bangaren kasa, ko jiha, ko zamani, ko kuma yanayin iskar da irin barnar da ta yi.  Da fatan kin gamsu.