Amsoshin sakonnin masu karatu (7)

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina fatan kuna lafiya.  Don Allah wai wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android ta kasar Sin da wacce ba ta kasar Sin ba, wacce ce ba ta saurin cinye bayanai idan ana shawagi a Intanet da ita? Wa alaikumus salam. Ai batun cinye bayanai ko saurin zaftare bayanai sanadiyyar […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (7)

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina fatan kuna lafiya.  Don Allah wai wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android ta kasar Sin da wacce ba ta kasar Sin ba, wacce ce ba ta saurin cinye bayanai idan ana shawagi a Intanet da ita?

Wa alaikumus salam. Ai batun cinye bayanai ko saurin zaftare bayanai sanadiyyar shawagi a Intanet ba matsala ce ta wayar salula a karan-kanta ba.  Wannan ya ta’allaka ne ga nau’in tsarin da kake kai na kamfanin waya.  Idan babu wani tsari na musamman da kake kai, za su rika zaftarar kudin da ke katinka ne kai tsaye.  Amma idan akwai wani tsari (Data Bunble Plan) da kake kai, sai a rika zaftara daga adadin bayanan da aka tanada maka, ba daga kudin katin wayarka ba.  Don haka ka sani, zaftarar kudin katin waya da ake yi kai tsaye ya ta’allaka ne ga rashin tsari da mai waya ya kasa shiga. Ko kuma yana kan tsari, sai adadin bayanan da aka ba shi ya kare, a nan kam muddin yana da kudi a katin wayarsa, daga ciki za a ci gaba da zaftara.  Sai ka kiyaye. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum, yaya aka ji da jama’a?  Na karbi lambarka ne don in maka godiya, saboda zaburar da ni da ka yi wajen saba mini da fasahar Intanet sakamakon jin bayananka a shirinka na Sunnah Tb.  Na kuma fara zaben ajiye muraja’a don Intanet.  Ni daliba ce a Higher Islamic School da ke Gombe.  Baban Sadik, Allah saka maka da gidan aljanna, amin.  Daga Ummu Yusuf.
Wa alaikumus salam yaa Umma Yusoof. Ina godiya ni ma matuka da wannan jinjina. Allah amfanar da ke ta wannan hanya da fa’ida mai inganci da alfanu gare ki da al’umma baki daya.  Sai a yi hankali a yayin da ake mu’amala da fasahar Intanet da ma sauran hanyoyin sadarwa na zamani. Allah wuce mana gaba, amin.

Assalaamu alaikum warahmatullah, Allah kara basira, amin.  Bayan haka, na cire ma’adanar wayata ne daga wayar, daga baya da na tashi mayarwa sai wayar ta nuna mini: “Unformated Memory.”  Da na matsa kuma don in yi ‘formatting’ sai na ga an ce: “Delete All Data to Format,” aka sa “Yes or No” sai na matsa, sai aka sa “Operation Failed.”  dalibinka: Musa Adam, Mile 12, Legas.
Wa alaikumus salam Malam Musa.  Ta yiwu a karon farko da ka cire katin ma’adanar wayarka akwai kwayar cutar wayar salula a ciki, ko kuma bayan ka cire, ka sa a wata waya wacce ke dauke da kwayar cuta (birus), shi ya sa a karon karshe da ka zo mayarwa wayar ta ce allambaram ba ta san wannan ba.  Ko kuma, a sadda ka tashi cirewa daga wayar ko daga wata wayar da ka sa bayan ciro ta daga wayar farko, ta yiwu katin ma’adanar a bude yake a wayar, sai ka nemi cirewa ba tare da ka rufe bayanan da ka budo ko ka zuba mata ba.  Wannan zai sa bayanan da ke cikin katin su gurbace (Corrupt).  Idan kuwa suka gurbace, to babu yadda za a yi wayar ta fahimce su balle ta ba su ma’adana a cikinta.  Shi ya sa ta ce maka sai ka goge katin kafin ya yi amfani.  Nan gaba sai a kiyaye.  Kada a rika cire katin ma’adanar waya (Memory Card) ba tare da ka’ida ba.  Duk sadda kuma katin ma’adanar waya ke bude, ko bayanan cikinsa na bude ne, aka yi yunkurin cire shi daga wayar, ba tare da an rufe bayanan ba, to za a samu matsala. Da fatan ka gamsu.

Salaamun alaikum Baban Sadik, dubun gaisuwa da fatan alheri zuwa gare ka.  Tambayata ita ce: ina da wayar salula kirar “Samsung” kuma ina amfani da layin MTN na kasar Ghana.  Idan na yi yunkurin shiga manhajar tambaya ta “Google Search” sai a rubuto mini: “735 Failure to kuery DNS.”  To don Allah ka yi mini bayani, me ya sa ake rubuto mini wannan bayani?  Daga: Sirajiddeen, Ghana.
Wa alaikumus salam, barka Malam Sirajiddeen.  Wannan na daga cikin tangardar sadarwa da ake samu tsakanin kwamfuta ko wayar salula mai neman bayanai daga wata kwamfuta ko Uwar Garke (Serber) da ke dauke da bayanan da ake nema.  Cikakken lafazin “DNS” na nufin “Domain Name Serber” ne.  Duk sadda ka rubuta adireshin wani gidan yanar sadarwa daga waya ko kwamfutarka, za ta je ga kwamfutar da ke dauke da wannan gidan yanar sadarwa ne, dauke da bukatarka, a irin yare ko harshen da kwamfutoci ne kadai ke iya fahimta a tsakaninsu.  Idan ta mika mata wannan sako, sai waccan kwamfuta ta yi nazarin sakon, wanda ke dauke da adireshin gidan yanar sadarwar, kafin ta bayar da abin da ake bukata.  Idan aka yi rashin sa’a sakon bai je da kyau ba, ko kuma ita kanta kwamfutar da ke dauke da gidan yanar sadarwar na fuskantar wasu matsaloli na cikin gida, sai nan take ta turo wa kwamfuta ko wayar salularka wannan sako, cewa ta gaza wajen amsa bukatar da aka tura mata.  Wannan harshe ne ko yaren kwamfutoci, wanda masana harkar sadarwa tsakanin kwamfutoci ne ke iya fahimta.  Amma a duk sadda haka ta sake kasancewa, ka sake rubuta adireshin ka sake turawa, a hankali shafin zai bude.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, ina maka fatan alheri kuma Allah kara karfin gwiwa, amin.  Baban Sadik tambayata ita ce: meye amfanin wadannan kalmomin da ke cikin “Settings” na “Opera”: “Protocol” da “http” da kuma “Socket.” Shin, su ma suna da muhimmanci ne a cikin masarrafar “Opera”?  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Kano.
Wa alaikumus salam, Malam Yahuza.  Da farko dai, “Opera” masarrafar lilo ce ko shawagi a shafukan Intanet ta hanyar wayar salula ko kwamfuta.  Ita ce manhaja ko masarrafar da ke nemo maka shafin da ka bukata a Intanet.  Wadannan kalmomi na ishara ne ga ire-iren kayayyakin aikin da take tinkaho da su.  Kalmar “Protocol” na nufin “ka’ida ce ginanniya irin ta sadarwa tsakanin na’urorin sadarwa na zamani.”  Kalma ko gungun harafin “http” kuma shi ne: “Hypertedt Transfer Protocol,”  wato “ka’idar sadarwa mai aikin nemo shafukan Intanet masu dauke da rariyar likau ke nan.”  Idan ka shiga shafinka na Facebook misali, duk wata alama da za ka matsa ka ga an budo maka shafi na bayanai ko hotuna ko bidiyo, to rariyar likau ce, wato “Hypertedt Link.”  Sai kalmar “Socket,” wacce ke nufin “mahada tsakanin na’urorin sadarwa biyu, ko hanyoyin sadarwa biyu, ko kuma tsarin sadarwa guda biyu; da mai karba da mai bayarwa.”  Wadannnan tsare-tsare duk suna da muhimmanci, in ma ba su ba ne kashin bayan wannan masarrafa ta Opera gaba daya.  Su ne masu taimaka mata nemo shafin da kake bukata daga wayar salularka zuwa inda shafin yake.  Su ne masu hada wayarka da dukkan wata na’ura da ke son hada alaka tsakanin wayarka da ita a babin sadarwa.  Sannan su ne masu budo maka shafuka masu mashigi, daga inda kake zuwa wani shafi, cikin latsawa ko matsawa guda.  Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum, da fatan Allah Ya sa Malam Baban Sadik yana lafiya.  Don Allah ina so a taimaka a sanar da ni yadda ake shiga tsarin nan da ke ba da damar mu’amala da fasahar Intanet na tsawon wata guda a Naira dubu daya kacal, a wayar Tecno D5, Android.  Kuma, ita ma wannan wayar ana sa mata wasu “Settings” ne don yin mu’amala da fasahar Intanet?  Na gode, Allah Ya kara budi da basira da taimako a kasn dukkan lamarinka, amin.  Daga: Babani A. Garba, Malam-madori, Jigawa.
Za mu ci gaba