Amsoshin sakonnin masu karatu (A1)
Sakonninku… A yau ga mu dauke da wasikunku da kuka aiko ta hanyar gajeren sakon waya (tes). Wadanda aka aiko ta hanyar Imel duk na amsa su. Bayan haka, akwai wadanda aka aiko ta hanyar tes na amsa nan take, wadanda ban samu amsawa ba ne na kawo su don amsa su. Har wa yau […]
Sakonninku…
A yau ga mu dauke da wasikunku da kuka aiko ta hanyar gajeren sakon waya (tes). Wadanda aka aiko ta hanyar Imel duk na amsa su. Bayan haka, akwai wadanda aka aiko ta hanyar tes na amsa nan take, wadanda ban samu amsawa ba ne na kawo su don amsa su. Har wa yau zan kara maimaitawa: Duk tambayoyin da suke maimaitattu ne, ban kawo su ba; na goge su. Sai a yi hakuri.
Salaamun alaikum Baban Sadik, yaya himma? Don Allah ka yi mana cikakken bayani a kan yadda Gwamnatin Najeriya ta ba kamfanin Isra’ila kwangilar sirrinta na yanar gizo-gizo. Gaskiya bayanin da ka yi mana a gidan rediyon BBC bai gamsar da mu ba. Mun ji kamar kana goyon bayan wannan lamari ne. – Musa Kaliyos, Kofar Yamma, dambatta, Kano: 08066988910
Wa alaikumus salaam, Malam Musa ba haka lamarin yake ba. Idan na fahimce ka kana nufin kwangilar da gwamnatin tarayya ta baiwa wani kamfani da samar da masarrafa ko manhajar taje bayanai ta hanyar sadarwar Intanet. Watakila ba ka saurari shirin da kyau ba. Sashen Hausa na BBC da suka yi hira da ni kan wannan lamari sun bukaci in sanar da masu sauraro ne kan wannan tsari, da yiwuwar hakan a Najeriya, da kuma cewa ko idan an tashi yin hakan, za a ci nasara. Na kuma nuna cewa wannan tsari ne da zai ci kudi mai dimbin yawa, da lokaci, da kuma kwarewa. Sannan dole ne hukuma ta tabbatar wasu ’yan siyasa ba za su yi amfani da wannan tsari wajen aiwatar da leken asiri a kan jam’iyyun adawa ba. Har wa yau na nuna cewa, maimakon gwamnatin tarayya ta dauki wannan makudan kudi wajen aiwatar da wannan shiri, me zai hana a tafiyar da su don samar da ababen inganta rayuwar talakawa. Domin babu tabbacin shirin zai yi nasara, don abu ne da ke daukar lokaci, kuma yana bukatar hadin gwiwa tsakanin hukuma da sauran kamfanonin sadarwa, wanda yin hakan ba tare da matsala ba yana bukatar jajirwa. Duk cikin abin da na fada, babu abin da ke nuna ina goyon bayan shirin tarayya kan lamarin.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Ina fatan kana lafiya tare da ’yan uwa da abokan arziki. Ina son a yi mini karin bayani kan wadannan abubuwa guda biyu, wato: “Network Interface Card,” da kuma “Ethernet Card.” Sannan kuma mene ne bambancin da ke tsakaninsu wajen aiki a cikin kwamfuta? – Uncle Bash, Jimeta-Yola, Adamawa: 07037133338
Wa alaikumus salaam Uncle Bash, da fatan kana lafiya. “Network Interface Card” ko NIC a gajarce, ita ce na’urar da ke taimakawa wajen aiwatar da sadarwa a tsakanin kwamfutoci, a gajeren zango ne (Local Area Network) ko a dogon zangon sadarwa (Wide Area Network) ko kuma ta tsarin sadarwar wayar iska ne (Wireless Network) ko kuma ta tsarin sadarwar fasahar Bluetooth. Wannan na’ura tana jone ne da babban kundun kwamfuta, wato Motherboard. Kwamfutocin zamanin yau suna zuwa ne da wannan na’ura a hade cikin kundun kwamfutar, sabanin na zamanin baya, wadanda sai an saya an sa idan kwamfuta ba ta zo da na’urar ba, ko idan ta lalace sai a sayi wani a sanya mata. Kalmar “Ethernet Card,” kamar yadda ka rubuto, duk ma’anarta daya ce da wacce ta gabace ta. Ko dai ka ce “Network Internet Card,” ko “Network Interface Controller” ko “Network Adapter,” ko “Ethernet Card,” ko kuma ka ce “Ethernet Adapter,” duk abu daya ne, bambancin suna ne kawai. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Shin, mene ne bambancin wadannan kalmomi a tsarin sadarwa: “Internet,” da “Intranet,” da kuma “Edtranet.”? – Uncle Bash, Jimeta-Yola, Adamawa: 07037133338
Wa alaikumus salaam. Da farko dai, kalmar “Internet” na nufin tsarin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci, wanda ke haddasa su yin ‘magana’ ko ‘mu’amala’ da juna a ko ina suke a duniya. A gajarce akan kira wannan tsari da suna giza-gizan sadarwa ta duniya, wato: World Wide Web ke nan a Turance. Wannan tsari na sawwake wa kwamfutoci ne mu’amalar sadarwar ta hanyar wayar iska da ke tsakanin kwamfutocin. Wannan sadarwa na yiwuwa ne ta hanyar adireshin IP, wato “Internet Protocol” ke nan. Wanda lambobi ne na musamman da kowace kwamfuta ke da su, kamar yadda kowannenmu a duniyar yau yake da lambar wayar tarho. Kamar yadda ba a samun mutane biyu masu wayar tarho iri daya, haka ba ya yiwuwa a samu kwamfutoci biyu masu lambar IP iri daya.
Kalmar “Intranet” kuma na nufin tsarin sadarwa ne a tsakanin kwamfutoci da ke zangon sadarwa guda daya. A takaice dai gidan yanar sadarwa ne da ke killace a zangon sadarwar wani kamfani misali, wanda ake amfani da shi don aiwatar da sadarwa a tsakanin ma’aikatan wannan hukuma ko kamfani ko ma’aikata. Misali, hukumar Babban Bankin Najeriya na iya mallakar gidan yanar sadarwa a ofishinsa, wannan aka killace shi ga ma’aikatan hukumar kadai. A tsarin “Intranet” babu wanda zai iya gani ko mu’amala da bayanan da ke cikin shafin sai ma’aikacin hukumar. Killataccen gidan yanar sadarwa ne.
Shi kuma “Edtranet” tsarin sadarwa ne tsakanin wani kamfani ko hukuma da abokan huldarta. A wannan tsari, sai wanda yake da suna (username) da kalmar izinin shiga (password) a gidan yanar zai iya shiga, ya ga bayanan da aka tanada masa, don aiwatar da sadarwa ko hulda tsakaninsa da masu gidan yanar sadarwar. Bambancin da tsakanin wadannan kalmomi guda uku dai a bayyane yake; Kalmar Intanet ta kowa da kowa ce, kana iya shiga a duk sadda ka so. Kalmar “Intranet” kuma sai ma’aikacin hukumar, ko wanda ke aiki a hukumar da ta tanadi shafin yanar gizon. A karshe, kalmar “Edtranet” kuma sai ga abokan hulda. Wannan shi ne bambancin da ke tsakaninsu. Abin da ke hada alaka a tsakaninsu kuma shi ne, dukkansu gidajen yanar sadarwa ne, masu dauke da bayanai; hanyoyin shiga da mu’amala da su ne kadai ya bambanta su. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, kwanakin baya na ga amsar da ka ba wani mai karatu da ya nemi a ba shi adireshin gidan yanar Musulunci inda zai aika tambaya. Ina so ka taimake ni da wannan adireshin. – Yakubu Amin: 08069225655
Wa alaikumus salaam. Lallai an yi haka. Gidan yanar sadarwa da na ba shi na Turanci ne da Larabci, duk da cewa ya bukaci na Hausa ne, wanda na ce a halin yanzu babu wani shafi sananne, sai ya nemi shafukan manyan malamanmu ya aika musu da tambaya, in sun samu hali suna iya amsawa, musamman wadanda suke Dandalin Facebook. Ga adireshin da na ba shi: www.islamka.com. Allah sa a dace, amin.
Salaamun alaikum, da fatan alheri da samun babban rabo a duniya da lahira. Don Allah ina son in san hanyar da zan bi wajen ajiye “Notes” da na karanta a Intanet, domin idan na ajiye a kan ma’adanar waya ta (Phone Memory) sai ya nuna min alamar tambaya (?). Ka huta lafiya. – Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama kuarters, Kano: [email protected]
Wa alaikumus salaam, Malam Yahuza ban san me kake kokarin yi ba. Kana nufin gajerun bayanai da kake rubutawa a wayarka? In su ne, ai da zarar ka rubuta su sun tabbata ke nan a ma’adanar wayarka. Sai dai in wadanda aka aiko maka ne, ko su ne ma, in har suka shigo cikin wayarka har ka samu damar karanta su, sun tabbata ke nan a ma’adanar wayarka. Idan kuma wani abu daban kake nufi, sai ka yi bayani iya gwargwado. Ina sauraronka.
Assalaamu Alaikum, ko gaskiya ne wai idan kana sa wayar salula a aljihun gaba kuma ana kiranka, wai za ka kamu da cutar sankara (Cancer)? – Isyaku M. Rimi: 08067444471
Wa alaikumus salam, Malam Isyaku, a gaskiya ban da masaniya kan wannan lamari. Ire-iren wadannan jita-jita sun sha maimaituwa a bakunan mutane kan cewa wayar salula na fitar da wasu sinadarai na maganadisun lantarki masu illa da ka iya haddasa cutar sankara. Wadannan jita-jita ba su da tushe a binciken kimiyya ko likitanci. Don haka idan har akwai wani abu da kake ji sanadiyyar hakan, to ina ba ka shawara da ka tuntubi likitanka don karin bayani. Allah sa mu dace, amin. Da fatan ka gamsu da ’yar gajerar amsar da na bayar.
Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah a aiko mini da kasidar Tsibirin Bamuda zuwa Imel dina da ke: [email protected]. Ka taimaka. – 08095023202
Wa alaikumus salaam, Malam Suleiman, lallai na tura maka wannan kasida mai shafuka goma. Sai ka duba jakar Imel dinka ka saukar ka amfana da abin da ke ciki. Allah sa a dace.
Salaamun alaikum Baban Sadik, ina roko a turo mini kasidar Tsibirin Bamuda zuwa Imel dina: [email protected].
Wa alaikumus salaam, Malam Muhammad tuni na tura maka wannan kasida. Sai ka duba akwatin Imel dinka don saukarwa. Allah sa a amfana da abin da ke ciki.
Salaamun alaikum, ina godiya matuka a gare ka. Allah Ya saka maka da alheri. Babu abin da za mu ce sai dai godiya, Allah Ya raya maka ’ya’yanka. Na ga kasida ta shigo mai taken: “Haske da Yadda yake Samuwa a Kimiyyance.” Na gode. – Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Kano
Wa alaikumus salaam, Malam Yahuza ni ma ina godiya matuka da irin addu’o’inku masu albarka da kuke aikowa. Allah albarkace mu baki daya, amin. Na gode.