Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel
Assalamu Alaikum, Malam ni dalibi ne a Polytechnic, Jigawa. Ina karanta fannin “Information Technology” ne. Malam ina so ka ba ni shawara ta yadda zan habbaka karatu na. Aliyu Adamu Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aliyu. Ina maka fatan alheri, kuma Allah sa abin da ake kan nema a dace, ya zama mai […]
Assalamu Alaikum, Malam ni dalibi ne a Polytechnic, Jigawa. Ina karanta fannin “Information Technology” ne. Malam ina so ka ba ni shawara ta yadda zan habbaka karatu na. Aliyu Adamu
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aliyu. Ina maka fatan alheri, kuma Allah sa abin da ake kan nema a dace, ya zama mai amfani gare ka da al’umma baki daya. Fannin Kimiyyar Sadarwar Zamani wani fanni ne mai muhimmanci kamar sauran fannonin ilimi. Duk da cewa wasu malamai na ganin muhimmancin fannin ya dara sauran fannoni, sanadiyyar dogaro da shi da sauran fannonin ilimi suke yi wajen sabunta su da habbaka su da mayar da su masu kaifi wajen samar da fa’ida. Ga dalibi dake karantu a wannan fanni, yana da kyau ka lazimci karatu. Ma’ana ka fadada karatunka sosai, kada ka rika dogaro ga abin da ake karantar da kai a aji kadai. Na biyu, ka rika kwatanta abubuwan da ake karantar da kai a aji. Na san yanayin makarantunmu ba lallai ba ne a ce akwai isassun na’urorin gwaji (Practical Facilities). Wannan ya sa dole dalibi da ke karatu a wannan fanni ya zama ya mallaki kwamfuta wacce da ita zai rika aiwatar da karatunsa. Abu na uku, duk abin da aka karantar da kai, ka tabbata ka nakalce shi sosai kafin ka zarce zuwa gaba. Ma’ana, idan malami ya karantar da ku wani sabon fanni ko bangaren ilimi, idan ba ka fahimci karatun ba, ka fadada bincike ciki har sai ka fahimta. Idan abin ya kure maka ka samu malamin don ya yi maka karin bayani. Ka sani, bambancin wannan fanni da fannin likitanci kadan ne. Ma’ana da zarar ka gama karatu, to ana daukarka a matsayin wanda ya san “komai” ne a fannin.
Abu na hudu, ka juri hakuri da juriya. Wadannan su ne sinadaran nasara a fagen rayuwa baki daya. Abu na biyar, ka mallaki littattafai, musamman kan bangarorin da ke bukatar aiwatar da su a aikace. Duk wani bangaren ilimi da ake bukatar aiwatar da shi a aikace, to, dole ne ka nakalce shi, ka iya shi a aikacen. Wannan zai ba ka kwarin gwiwa wajen ci gaba da karatu, kuma ba za ka ji wata nakasa ba a zuciyarka a duk sadda aka danganta kwarewa gare ka a fannin. Abu na shida kuma na karshe, shi ne ka lazimci mu’amala da fasahar Intanet wajen neman karin sanayya. Tabbas a baya nace ka yawaita karance karance da mallakar littafai. Wadannan abubuwa ne biyu masu wuyar sha’ani ga dalibi rago, sai da dagewa. Abin da kuwa zai taimaka maka cikin sauki shi ne sabo da iya mu’amala da fasahar Intanet a matsayin wata kafa ta karuwar ilimi. A nan ne za ka mallaki littattafai masu dimbin yawa cikin sauki da araha (idan ma saya za ka yi), a nan ne za ka samu hanya mafi sauki wajen kara fahimtar abubuwan da ake karantar da kai. Domin za ka samu bayanan dalibai ‘yan uwanka da ke wasu kasashen wadanda ke karatu a fanni irin naka, da irin abubuwan da ake karantar da su. Idan ma aikin gida aka ba ka kana iya samun hanyar warware mas’alolin cikin sauki. Ina maka fatan alheri, kuma Allah Ya sa ka dace a dukkan lamurranka na rayuwa, amin.
Salamun alaikum, da fata Baban Sadik da iyalansa na cikin koshin lafiya. Wai shin tsakanin nau’in babbar manhajar “Android Kitkat” da “Lollipop” wacce ce mafi inganci? Bugu da kari, tsakanin wayoyin Google da na Samsung, wanne ke kan gaba? Na gode. Mathew Garba Daga Kaduna.
Malam Mathew barka ka dai, kwana biyu ashe kana nan. Da farko dai, nau’in babbar manhajar “Lollypop” ita ce ke kan gaba wajen sabunta da armashi sannan ta fi kayatarwa wajen abubuwan da ke sawwake wa mai waya mu’amala da bayanai. Domin ita ce aka fitar gab da karshen shekarar 2014. A bangaren kyale-kyale ma “Lollypop” ta doke “Kitkat” nesa ba kusa ba. A ka’idar kimiyyar sadarwa, idan ba kuskure aka samu ba, dukkan sababbin manhajoji sun fi na bayansu inganci da kayatarwa. A wani lokaci akan samu kuskure wajen kira ko gina manhajar, kamar yadda ya faru tsakanin “Windows bista” da “Windows dP.” Windows dP ce tsohuwar yayi, amma wajen inganci da kayatarwa, ta fi Windows bista. Shi ya sa ma ko tsawon rayuwa bista ba ta yi ba aka canza ta da Windows 7. Amma idan ba matsala aka samu ba, duk sabon yayi ya kamata ya dara tsohon yayi.
Na biyu, ban san me kake son sani ba dangane da wayoyin Google (Google Nedus) da na Samsumg. A halin yanzu babu wani kamfani da za a ce wayoyinsa ne suka dara na kowane kamfani inganci. Domin kowane kamfani na da wani bangare na musamman da ya kware wajen kayatar da wayoyin da yake kerawa, wanda kuma sanadiyyar hakan ya dara sauran. A bangaren babbar manhaja, wato Android, tabbas na kamfanin Google sun dara na kamfanin Samsung. Domin asalin babbar manhajar tasu ce, kamfanin Samsung na aron lasisi ne kawai a wajensu. A daya bangaren kuma, idan muka yi la’akari da gamewa, da shahara, da ingancin gangar-jiki waya (Hardware), kamfanin Samsung ya shallake na Google nesa ba kusa ba. Domin a jerin kamfanonin waya yanzu a duniya, kamfanin Samsung ne a kan gaba. Kamfanin Google na can kasa ne a layi, saboda ba abin da suka kware a kai ba kenan, sannan ba su jima da shiga harkar ba. Da fatan ka gamsu.
Assalamu Alaıkum Malam da fatan kana lafıya. Wannan karon ina so ka yı mana bayanı akan yadda ake aiwatar da cinikı ta Intanet ne. Sannan ta yaya ake iya aiko wa mutum abin da ya saya har inda yake? Sannan sai ka sanar mana fa’ida, da kuma matsalolin cinikayyar in mutum zai yi, a matsayın kasuwancı. Na gode Allah ya ba da lada. – Umar Zuma
Wa alaikumus salam, Malam Umar barka da warhaka. Da farko dai ka gafarce ni sanadiyyar tsaiko da aka samu wajen amsa tambayarka. Wannan ya faru ne sanadiyyar yawan shagulgula, kamar yadda daga baya ka karanta. Wannan tamabaya taka na taba amsa makamanciyarta a baya, illa dai ban fadada ba ne sosai. A takaice dai, tsarin aiwatar da kasuwanci ta hanyar Intanet yana da fuskoki daban-daban. Ya kuma danganci hajar da kake da ita kake son tallata wa duniya. Sannan ya danganci inda kake; ma’ana hajar na bukatar aika wa wanda ya saya a zahiri ne, ko dai ta hanyar sadarwar Intanet?
Ko ma dai mene ne, ga duk wanda ke son aiwatar da kasuwanci ta Intanet, dole ne ka mallaki shago, ma’ana mahallin da za ka baje hajarka don masu sha’awa su gani. A nan za ka bude shafin yanar sadarwa kenan, wato “Website.” Idan ba ka da hali, akwai wuraren da ake baiwa masu hajoji damar tallata hajojinsu, sai ka bi ta wadannan hanyoyi. Sannan kana bukatar zuba bayanai kan kowace haja, domin ba kiranka za a rika yi a waya ko aiko maka Imel don tambayar irin aikin da hajarka ke yi ba. Kowace haja dole ne ka zuba bayanai masu isarwa kanta, wadanda za su ja hankalin mai saye. Sannan ka sa bayanai kan hanyoyin da za a bi wajen biyanka idan an tashi bukatar hajar. Wannan na nufin za ka bude taskar ajiya ta musamman kenan da banki. Idan masu sayan hajar ba su takaitu ga Najeriya kadai ba, dole ne ka yi bayanan hanyoyin da za a rika bi wajen biya. Sannan dole ne ka yi bayanin hanyar da za ka rika aika wa masu saye da hajarsu. Idan haja ce bayyananniya, dole a tanadi hanyar karbar bayanan adireshinsu don aika musu. A karshe, dole ne ka yi rajistar kamfani, wanda da shi ne za ka bude taskar ajiya a banki. Duk abin da ya faru da kamfanin za a yi zance ba da kai ba. Kamar yadda tsarin dokar cinikayya na zamani yake.
Dangane da fa’ida, wannan tsari ne mai kyau. Domin zai rage maka kashe kudi. Na farko dai ba ka bukatar biyan kudin shago, sai dai kudin adana maka shafukanka na Intanet, wanda ba zai kai na shago zahiri tsada ba. Na biyu, idan har ka samu kwastomomi, ba ruwanka da tayi; farashin da ka sanya wa hajojin kawai za a rika biyanka. Abu na uku, ko kana kwance kana bacci a kan gadonka, shagonka na can a bude, kasuwarka a farke take kowane lokaci. Idan muka koma wajen matsaloli, abu na farko wanda zan kira kalubale, shi ne samun amincewar mutane har su sayi hajarka. Idan ba wadanda suka sanka ba, to dole ne ka yi ta tallata hajar ta hanyoyi masu yawa, masu isarwa kuma (irin su Facebook da Whatsapp da sauransu). Ka sani, sai mutane sun samu amintuwa da kai kafin su sayi hajarka a Intanet. Wannan ke nufin za ka kashe kudi masu dimbin yawa kenan wajen tallata hajar. Sannan dole ne ka rika sabunta bayanai a shafinka. Wannan ke nufin za ka rika ciyar da lokacinka kenan mai tsawon wajen yin hakan. Da dai sauran abubuwa masu dimbin yawa da sai ka shiga harkar za ka tarar.
Salaamun alaikum, yaya aiki kuma yaya iyali? Da fatan suna cikin koshin lafiya. Allah Ya kara basira. Don Allah Baban Sadik wadannan litattafan da ka fada, a ina za’a same su kuma meye farashinsu? Ina son a turo mini ta Imail dina: [email protected]. Ka huta lafiya. – Shamsuddeen Kabir.
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Shamsuddeen, da fatan kana lafiya. Zai dace ka kira ni sai mu yi bayanin yadda zan aika maka. Littattafai ne dake cikin kwamfuta, zan iya aika maka su. Sai dai idan kana bukatar wadanda aka dabba’a (Printed Copies), wadannan kuma sai ka saya ta shafinsu da ke Intanet. A Najeriya ba a cika samun littattafan ilimin kwamfuta wadanda aka dabba’a cikin sauki ba, sai a birane irin su Legas, da shagunan sayar da littattafai dake manyan jami’o’inmu. A takaice dai, kana iya kira na sai in maka bayani. Idan ka gamsu da wadanda nake da su, ba zai yiwu a aika su ta Imel ba, saboda nauyinsu. Kuma zai iya yiwuwa inda kake babu yanayin Intanet mai karfi a can. Da fatan ka gamsu.