Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel (3)
Assalamu alaikum, yaya aiki? Na ga wata waya mai suna: Tecno F7, ina so in saya, amma don Allah ina so a ba ni shawara kafin nan. Kuma akwai wata waya nokia N1, an ce ba ta da SIM da kuma rediyo shin gaskia ne? Na gode – Isa Salisu Wa alaikumus salam, aiki Alhamdulillah. […]
Assalamu alaikum, yaya aiki? Na ga wata waya mai suna: Tecno F7, ina so in saya, amma don Allah ina so a ba ni shawara kafin nan. Kuma akwai wata waya nokia N1, an ce ba ta da SIM da kuma rediyo shin gaskia ne? Na gode – Isa Salisu
Wa alaikumus salam, aiki Alhamdulillah. Shawara dangane da Tecno F7, ban san me kafi bukata a jikin waya ba balle in san irin shawarar da zan ba ka. A tare da haka, waya ce mai kyau, tana dauke da babbar manhajar Android, mizanin ma’adanar waya 4GB, da ma’adanar wucin-gadi (RAM) 1GB. Sannan kaifin kemara dinta 8MP ne. Tana da kemara a goshinta mai dauke da kaifin 2MP. Na’urar sarrafa umarninta (Processor) na da inganci. Sannan za ka iya sa mata karin ma’adana ta MMC har zuwa 32GB.
A bangaren Nokia N1 kuma, kamar yadda ka ji, ba wayar salula ba ce, domin ba ta dauke da na’urar siginar rediyo, balle katin SIM. Na’urar Sarrafa bayanai ce. Tana dauke da tsarin sadarwa na wayar iska, wato Wireless LAN (WLAN) na zamani. Ma’adanarta da ta zo da ita ta kai mizani 32GB, sannan ma’adanar wucin-gadi (RAM) 2GB ce. A takaice dai na’ura ce ta sarrafa bayanai da mu’amala da bayanai, amma ba wayar salula ba ce. Idan kana son mu’amala da Intanet, da kallon bidiyo da sauraron sauti da saukar da manhajoji da masarrafai masu kayatarwa da ilimantarwa, to, za ta iya maka, iya karfin da aka ba ta. Amma aiwatar da kira ko karban kira, ba da ita ba, wai gada a makabarta.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Ko yaushe muna maka addu’ar fatan alheri dangane da karuwa da kai da muke yi. Allah saka da alheri. Baban Sadik ina so ka kara wayar mini da kai ne game da tsarin ‘Google+’. Ta yaya zan aika wa wani sako ta Google+? Daga Abdulazeez Adamu Fira, Birin-Fulani, Nafada, Gombe.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulazeez. Shafin “Google +” shafin dandalin abota ne na kamfanin Google Inc dake Amurka. Yana da kamaiceceniya da Facebook ta wasu bangarori, amma galibin tsare-tsarensa sun sha bamban da na Facebook. Idan kana son aika wa mutum sako ta wannan shafi kana iya yi ta hanyoyi da dama. Hanya ta farko ita ce tura masa sakon kai tsaye a shafinsa, idan har akwai abota a tsakaninku kenan. Ma’anar sakon kai tsaye, ita ce: “Pribate Message,” ko “Inbod,” kamar yadda ake fada a dandalin Facebook. Hanya ta biyu, kana iya aika masa ta jakar Imel dinsa, wato Gmail kenan. Domin duk wanda ka gani da shafi a Google +, to lallai yana da adireshin Gmail. Sabanin shafin Facebook da za ka iya amfani da kowane irin adireshin Imel ne ko ma lambar waya, a Google + sai ka yi rajista da manhajar Imel na kamfanin Google mai suna Gmail. Da zarar ka yi rajista da Gmail, to, kana iya mallakar shafukan Google da dama, kyauta. Hanya ta uku ita ce, kana iya aika masa sako ta hanyar shafinsa kai tsaye, ko ka yi ta’aliki kan sakon da ya rubuta a shafin ko wani abu makamancin hakan. Da fatan ka gamsu.
Assalamu Alaikum. Na gaida Baban Sadik da irin ayyukan da kake yi wajen taimakon jama’a ta hanyar karuwa na ilimi. Tambaya nake da ita. Na farko, ina da kwamfutar tafi-da-gidanka (Laptop) mai dauke da babbar manhajar “Windows 7.” Ina son in loda mata nau’in “Windows 8.” Wasu hanyoyi zan bi don tabbatar da ba a samu matsala ba? Tambaya ta biyu: shin, zan iya sayo babbar manhajar “Windows 8” irin wanda ‘yan kasuwa suke sayarwa na loda mata, ba wata matsala? Da fatan zan samu amsoshinsu. Daga Bilyaminu D Sulaiaman, Bauchi.
Wa alaikumus salam Malam Bilyaminu, da fatan kana lafiya kai ma. Zan fara da tambayarka ta biyu. Idan na fahimceka sosai, kana nufin irin wadanda ake sayar da su a kan titunan biranen kasarmu kenan. Wadannan nau’ukan manhajoji tabbas suna da kyau a karan kansu, sai dai kuma hanyar da ake bi wajen samar da su, ina nufin masu sayar da su kenan, haramtacciyar hanya ce. Shi ya sa idan ma ka saya ka loda wa kwamfutarka, muddin za ka yi mu’amala da fasahar Intanet a kan wannan babbar manhaja da ka saya ta wannan hanya, dole kamfanin Microsoft zai gane. Wannan zai sa ka ga kwamfutar ta fara sanar da kai cewa: “Wannan babbar manhajar ba ta asali ba ce…” a duk sadda ka kunna ta. Daga baya ma suna iya hana ka mu’amala da babbar manhajar; idan ka kunna sai ta kulle kanta, ta ce ka nemo mai kyau ta asali ka sa.
Hakan ya faru ne saboda masu sayar da su na bin haramtacciyar hanya ce wajen samar da su da yada su. Su kuma suna samun kasuwa ne saboda asalin wadanda ake sayarwa na asali daga kamfanin Microsoft suna da dan karen tsada. Idan kana bukatar nau’in Windows 7 Starter wanda mutum 1 ko 3 za su iya amfani da ita, gangariya mai kyua, dole sai ka kashe sama da dubu 30 a Najeriya! A takaice dai amfani da ire-iren wadannan manhajoji, duk da lalurar tsadar masu asali ko gangariya, yana dauke da matsaloli, sannan ba lallai ba ne ka samu biyan bukata cikakkiya. Wannan shi ne abin da ya kamata ka fahimta a farko.
Dangane da loda wa kwamfutarka wata babbar manhaja bayan wadda take dauke da ita, wannan shi ake kira “Dual Booting,” idan guda biyu ne, idan manyan manhajoji uku ne a ce: “Tripple Booting.” Kafin yin hakan, zai dace ka lura cewa, kowace babbar manhajar kwamfuta tana da ka’idojin mahalli da take bukatar a cike su kafin a loda wa kwamfuta ita. Wanann shi ake kira “System Rekuirements.” Ba kowace kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows 7 ake iya loda mata Windows 8 ba, sai an yi la’akari da tsarinta. Me ye mizanin babbar ma’adanarta, wato: “Hard Disk Dribe?” me ye mizanin ma’adanar wucin-gadi (RAM) da take dauke da ita? Sannan meye mizanin na’urar sarrafa umarni (Processor) da ke kwamfutar? A talakance, ana bukatar mizanin ma’adana 15GB zuwa 20GB. Ana bukatar mafi karancin mizanin ma’adanar RAM 1GB zuwa 2GB. Sannan ana bukatar kwamfutar ta kasance da na’urar Processor 1Ghz zuwa 1.5Ghz. Wannan a talakance kenan.
Idan ka tashi loda mata Windows 8, bayan ka tabbatar da cancantar mahallin da babbar manhajar za ta zauna a ciki, dole ne ka raba babbar ma’adanar gida biyu, wannan shi ake kira “Disk Partitioning.” Idan sauran filin da ke babbar manhajar ya kai 100GB misali, sai ka yanki 60GB don baiwa Windows 8. Akwai manhajoji da za ka iya amfani da su wajen yin hakan; wadanda suke cikin kwamfutarka da wadanda za ka iya saukarwa daga Intanet. Sai ka kintsa bangaren da ka yanko daga ma’adanar, wato: “Disk Formatting” kenan. Idan ka gama da wannan bangare, sai ka sanya faifai ko ma’adanar da ke dauke da babbar manhajar Windows 8 din, ka kashe kwamfutar ka sake kunna ta. Idan ta fara kunnuwa, za ta dan dakata idan ta ji alamun faifan CD/DbD a cikinta, sai ta ce maka: “Press Any Key to Boot from CD/DbD ROM.” Da zarar ka ga wannan sako, sai ka latsa kowane maballi daga allon shigar da bayananka, wato “Keyboard” kenan. Daga nan za ta budo maka ma’adanar kwamfutarka, wato “Hard Disk Partitions,” ta tambayeka inda kake son loda wannan babbar manhajar. Ka lura, za ka ga “Local Disk (C) – Windows 7” da “Disk (D) – sunan da ka ba bangaren…” misali. Ka zabi Disk D, tunda shi ne bangaren da ka yanko daga uwar ma’adanar. Kada ka zabi “Local Disk (C),” idan ka yi haka za a goge wannan babbar manhajar ta Windows 7, don ita ce dauke a ciki. Sai a kula da kyau. Idan ka zaba, sai ka bar mata sauran ayyuka. Za ta saukar da dukkan bayanan da take bukata daga wannan faifan CD/DbD zuwa wani bigire na wucin gadi (Temporary folder) da ke cikinta. Za ka ga tana sanar da kai cewa: “Loading System Files…” ko wani abu makamancin hakan.
Da zarar ta gama saukar da bayanan da take bukata, za ta sake kashe kanta, ta kunna kanta nan take. Kar ka taba ta. Kada ka yi mata katsalandan; ka bar ta kawai, ita za ta ci gaba da sarrafa kanta. Tana gama kunnuwa sai ta fara loda babbar manhajar. Wannan zai dauki lokaci, ya danganci mizani da kuzarin kwamfutar. Kai dai ka rika lura da bayanan da take bayyanawa a shafin fuskarta kawai. Za ta kashe ta sake kunna kanta akalla sau 3, kafin ta je marhalar da za ta nemi bayanai daga wajenka. Idan ta kai wannan marhala za ka gane, domin abu na farko za ta bukaci ka zabi kasar da kake. Sai ka gangara kasa wajen harafin N, ka zabi Najeriya. Sai harshe, sai nau’in tsarin allon shigar da bayanai (Keyboard Settings). Sai kwanan wata, sai lokaci…da dai sauran bayanai. Idan ta gama karbar bayanai daga wajenka ma za ta sake kashe kanta ta kunna kanta. Daga nan za ta ce maka: “Wait…Setting up your desktop for the first time…” ko wani sako makamancin wannan. Da zarar ta gama wannan aiki, sai ta kaika shafin farko, wato: Desktop kenan.
Wannan bayani ne a takaice, a gajarce, a talakance. Idan ba ka da sanayya kan halayya da tsarin kwamfuta, ka kai wa kwararru don su yi maka. Ka sanar da su abin da kake so, da yadda kake son abin ya kasance. Wannan bayani na yi maka ne don ya haskaka maka hanya. Da fatan ka fahimta kuma ka gamsu.
Salamun alaikum, don Allah ina da tambaya. Da yawa na lura idan na bude Group a Dandalin Facebook idan aka aika sako, nakan ga ana cewa: “Mutane kaza sun gani”, wato “20 Seen,” misali. To don Allah ya ya zan yi in cire wannan sakon sanarwar, don a daina nuna cewa “20 people saw this?” – Mahmoud Abdullahi
Wa alaikumus salam, Malam Mahmoud, wannan sako da kake gani daga tsarin shafin ne, kai da kake da Zaure a Dandalin Facebook ba za ka iya cire shi ba. Kada ka mance, wannan sako wata hanya ce ta karin sanarwa ga duk wanda ke cikin Zauren. Sannan hanya ce har wa yau da hukumar Facebook ke bi wajen taya mai shafin lura da ayyukan dake gudanuwa a zauren. Idan ba ka so, kuma kai ne da zauren, sai dai ka yi hakuri. Zuwa yanzu dai, ban san wata hanya (duk da na kwana biyu ban yi nazarin sababbin tsare-tsaren Facebook ba) da hukumar Facebook suka tanada don cirewa ko hana wanan sako bayyana ba. Sai dai watakila nan gaba. Domin a kullum suna aiwatar da sauye-sauye kan shafin. Ta yiwu nan gaba idan suka samu korafe-korafe da dama daga wajen jama’a su samar da hanyar cire sakon. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Allah Ya kara basira, ameen! Wai don Allah ta ya ya zan bude Laptop dina da ta kulle; idan na kunna ga abin da take rubutawa: “GRUB LOADING STAGE 1.5. GRUB LOADING, PLEASE WAIT…” Allah Ya sa a dace, amen. Daga Nuruddeen Umar, Katsina.
Wa alaikumus salam Malam Nuruddeen, barka da warhaka. Duk da cewa ba ka yi bayanin hakikanin abin da ya faru ba; wace irin babbar manhaja ce a kwamfutar? Idan guda biyu ce, wani iri da wace iri? Sannan me ya faru kafin ka samu wannan sako? Abin da nake iya fahimta shi ne, kamar kana da manhajojin kwamfuta nau’i biyu ne a kwamfutar; da Windows, ko dai Windows dP ko Windows 7. Sannan da babbar manhajar kwamfuta nau’in Linud; ko dai Backtrack, ko Kali Linud, ko kuma Ubuntu zubi na 8 (bersion 8.04). Sannan, idan zan kara hasashe, watakila kana son cire nau’in Linud din ce, don komawa kan Windows da ka saba da ita. A tunanina wanan shi ne kusa da abin da zai iya kasancewa.
Da farko dai wannan sakon matsala (Error Message) da kake samu shi ake kira “Error 17” idan nau’in Ubuntu ce. Idan kuma nau’in OpenSuse ce, ana kiransa “Error 22.” Hanya mafi sauki wajen warware wannan matsala, in har so kake ka cire wancan babbar manhaja ta nau’in Linud, wanda sanadiyyar hakan ka kasa shiga Windows dinka, kana iya amfani da faifan CD/DbD mai dauke da babbar manhajar nau’in Windows din da kake amfani da shi, don gyara matsalar. Sai ka sanya faifan da ke dauke da babbar manhajar a kwamfutarka, ka sake kunna ta. Da zarar ta ji faifan CD/DbD din a cikinta, za ta yi yunkurin farkawa ta bangarensa, daga nan sai ka gyara matsalar. Bayan ka gyara Windows din, sai ka yi amfani da “Windows Partition Manger” don goge wancan bangaren ma’adanar dake dauke da babbar manhajar Linud.
Wannan gajeriyar shawara ce wacce na gina ta kan hasashe da na yi a sama. Idan ba ka da sanayya kan halayya da tsarin kwamfuta, kana iya kaita wajen masu gyara ka bayyana musu matsalar, a aikace, don su gyara maka. Da fatan ka fahimta.
Baban Sadik na ji bayaninka akan Facebook yanzu a Sunna Tb. Amma ina so na fahimci yadda ake bude Group? Sannan mene ne alakar Youtube da Facebook? – Sa’ed A. Sa’eed
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sa’eed. Idan kana bukatar bude shafin Group a Dandalin Facebook, ka je shafinka, ka gangara kasa kadan daga hagu, za ka ga inda aka rubuta: “Create Group,” sai ka latsa. Za a kaika inda za ka tsara yadda kake son shafin ya gudanu. Daga sunan shafin, zuwa maudu’in da za a rika tattaunawa a ciki, da kuma matsayin kowane mamba wajen aika sako, da dai sauransu. Dangane da asali da gudanuwa, babu wata alaka a tsakanin shafin Youtube da Facebook. Abin da ya hada tsakaninsu kawai shi ne, kasancewarsu shafukan abota ne. Shafin Youtube na kamfanin Google ne, a daya bangaren kuma, shafin Facebook na kamfanin Facebook ne, dukkansu a Amurka. Da fatan ka gamsu.