Amsoshin tambayoyi

  Me ke kawo juyawar da a cikin mahaifa? Idan ya fara yaya za a yi? Daga Nasir G., Kano Amsa: A’a ba wata matsala ba ce juyawar da a mahaifa, domin ai mai rai ba ya rasa motsi. A jariran da ke ciki ma ai har ma da wasa ban da juye-juye. Ba wata […]

Amsoshin tambayoyi
Amsoshin tambayoyi

 

Me ke kawo juyawar da a cikin mahaifa? Idan ya fara yaya za a yi?

Daga Nasir G., Kano

Amsa: A’a ba wata matsala ba ce juyawar da a mahaifa, domin ai mai rai ba ya rasa motsi. A jariran da ke ciki ma ai har ma da wasa ban da juye-juye. Ba wata matsala babba ba ce, wasu kalilan ne juye-juye nasu kan sa cibiya ko mabiyiya ta nade musu wuya ko su zo a gicciye ko kuma a jirkice lokacin haihuwa, maimakon su zo da ka.

Me ke sa jarirai kukan dare? Ni nawa ba ya da lafiya amma duk da an ba shi maganin da likita ya rubuta ba ya dainawa. Sai kuka mai cin rai.

Daga Yahya Tsamaye

Amsa: A’a ai ko babba ne ciwo ya kama shi sai ya ji jiki, ya kuma yi ’yar jinya ballantana dan jariri. Kukan alama ce ta cewa ciwo na cin sa, ko kuma yana jin yunwa. Magunguna sai dai su dan rage wani abu kafin ciwon ya bar jiki gaba-daya. Ai shi ya sa za ka ji an ce maka magungunan da aka ba da na kwanaki kaza ne, ba na kwana guda ba. Don haka sai fa kwanakin magungunan nan sun cika ko sun kusa cika ko sun ma kare sa’annan za a ga canji. Idan bayan kwanakin da aka diba din ba ka ga canji a lafiyar jaririn ba, to ku koma asibitin.

Kawai dai abin da za ka yi shi ne ka taya uwargida rarrashinsa, sa’annan ku tabbatar ba yunwa a tare da shi, kuma ko me aka ba shi yana zama a ciki ba ya amayo shi, kuma yana karba, domin idan ba ya karba, ko yana amayo shi to da alama sai an kai da kwanciya a asibiti da karin ruwa da sinadarai, domin magunguna ba za su yi aiki ba idan babu sinadaran abinci a jiki.

Yarinya ce mai ciwon kurajen fuska masu tsanani. Don tsananinsu ko fita ba ta son yi saboda kurajen. Shi ne muke neman shawara.

Daga Siyama A. Katsina

Amsa: Eh, dama ai kurajen fuskar mataki-mataki ne, akwai marasa tsanani, akwai masu matsakaicin tsanani, akwai masu tsanani. To idan kurajen fuska suka yi tsanani har ba a son fita, tabbas abin sai ya kai ga likitan fata wanda zai ba da wasu magunguna masu karfi, wadanda ba kasafai za ki je kyamis a ba ki su ba. Su irin wadanda za ki je kyamis a ba ki su irin na shafawar nan ne, kuma a kuraje marasa tsanani ne akan shafa su baje. Don haka ke nan sai kin nemi asibiti wanda suke da likitan fata ya duba ta.