Amsoshin tambayoyi
Wane irin ciwo ne kuma kuke kira da fistula. Me ke kawo shi. Yaya alamominsa suke? Daga M. Sulaiman, Lagos Amsa: Fistula na nufin huda da ta hada wasu sassan jiki biyu, abubuwan da ke wannan sashe su rika shiga daya sashen su kawo matsala. Misalansu su ne hudar da kan hada babban hanji da […]
Wane irin ciwo ne kuma kuke kira da fistula. Me ke kawo shi. Yaya alamominsa suke?
Daga M. Sulaiman, Lagos
Amsa: Fistula na nufin huda da ta hada wasu sassan jiki biyu, abubuwan da ke wannan sashe su rika shiga daya sashen su kawo matsala. Misalansu su ne hudar da kan hada babban hanji da karamin hanji, ko mai hada babban hanji zuwa kan fata, ko mai hada hanyar fitsari da ta haihuwa (yoyon fitsari). Wadannan hudoji a cikin jikin mutum yawancinsu ciwo ne sanadinsu. Cututtukan za su iya zama dalilin wasu kwayoyin cuta ko kari ko wani abu da ya dade a wuri yana gogar wani sashe na jiki, kamar kan jariri. Akan iya samu ma a matsayin akasi ko wani kuskure bayan an yi wa mutum wata tiyata kamar idan karafunan aikin suka huda wani wuri bisa kuskure.
Mene ne amfanin miyau a jikin mutum? Kuma shin idan ya taru a bakin mutum tofar da shi ko hadiyewa ya kamata a yi?
Daga Jamilu M. Adamu
Amsa: Miyau yana da alfanu da dama ga jikin dan Adam. Kashi 95 cikin 100 na miyau ruwa ne, sauran kashi biyar majina. Idan miyau ya dauke wa mutum a baki ai ko hadiya ba zai iya yi ba saboda tsananin bushewa. Wato ke nan miyau yana aikin jika baki da makoshi. Sa’annan miyau yana da sinadarai a cikinsa na kashe kwayoyin cuta a baki. Har ila yau miyau yana da sinadarai a cikinsa masu iya narkar da wasu nau’o’in abinci.
Idan miyau ya taru a baki duk yadda ka yi da shi ba laifi ba ne, ko hadiyewa ko tofarwa. Laifin shi ne idan an tofar da shi a bainar jama’a domin za a rika yi wa mutum kallon kazami.
A likitance ko akwai wani amfani cin danyen nama?
Daga Basiru Danbazazzagi
Amsa: A’a ba wani amfani, sai dai ma illa ko ciwo da hakan zai iya jawowa a likitance.
Me ke kawo ruwan ido idan mutum na karatu? Kuma ko akwai hanyar kariya?
Daga Ado Lawal Kutama
Amsa: Yawanci ruwan ido yayin karatu na nufin raguwar karfin shi idon ke nan. Abubuwan da kan kawo raguwar karfin gani kuma yawanci ba a iya kiyaye aukuwarsu, wadannan su ne gado da tsufa. Don haka ba maganar a ba ka hanyoyin kariya ba ce wannan, maganar awon ido ce da magani ko gilashi.
Abu daya da aka san yana iya kawo dusashewar gani (amma da dare) wanda za a iya karewa shi ne ciwon dundumi, wanda karancin bitaman na rukunin A ke kawowa, kuma a yanzu ba a jin duriyarsa, saboda sinadarin bitamin din ya wadata, akan samu a kayan ganye irin su karas, latas da alayyahu. Kai har ma sa wa ake a fulawa da man gyada domin kowa da kowa manya da yara, birni da kauye su samu.
Yau shekara biyu ke nan ina cikin tafiya sai na ga wani duhu ya gitta. Tun daga nan ba na son haske. Ina kuma jin ciwon kai da masassara. Na je asibiti an ce mini zazzabin maleriya ne. Ko haka alamun maleriya yake?
Daga Aliyu G
Amsa: Eh, to watakila akwai zazzabin maleriya din a jikinka, amma wannan batu na gittawar duhu da rashin son haske yana kama da alamomin matsalar ido ne, shi ma ya kamata a ba shi mahimmanci, a je asibitin ido a bincike shi.
Ko shan maganin mura mai zafi da daci a kalla sau uku a wata yana iya kawo matsala ga lafiyar mutum?
Daga Abdulkadir Isa Legas
Amsa: Eh, yawan shan wasu abubuwa ko magungunan da ba likita ne ko ma’aikacin lafiya ya rubuta maka ba za su iya kawo matsala ga lafiya. Wanda likitan ma ya rubuta maka yana iya kawo matsala idan aka dade ana sha, wato yaya aka kare da shi, ballantana wanda ba shi ya ce ka sha ba. Akwai wannan rubutu a baya da muka yi a kan wannan maudu’in mai taken ‘Yadda magunguna kan illata jiki’. Ka neme shi ka karanta ka gane wa kanka.
Akwai wasu kayan hadi na abinci da akan yi amfani da su kamar ka fi tsami da sukarin. Shin ko suna da amfani ga lafiya?
Daga Abdullahi Umar Shuwaki
Amsa: A kimiyance dai gishiri da sukari da dangoginsu ne aka fi so a yi taka-tsantsan da su a cikin abinci, wato ba a so a rika sa su da yawa, kuma ba a so a ce an yi girki ba a sa ba, wato ka ga ke nan sai an saisaita. Yawanci duk wani kari na abinci yakan bi bayan dayan biyun nan ne. Wato sukarin zai iya bin bayan sukari, shi kuma dan tsami da sauran ire-irensu kamar magi, daddawa, kanwa da gauta da sauransu za su iya bin bayan gishiri. Kai ma ina ga ya kamata ka nemi rubutunmu a kan ‘amfanin kayan hadi na abinci’ domin ka kara samun bayani.