Amsoshin tambayoyi

Tambaya: Cikin azumin nan kare ya cije ni, wurin bai yi wani jini sosai ba. Da na tambaya sai aka ce ai karen ana kai shi allurai don haka kada in damu ban yi komai a kai ba. shi ne nake neman karin bayani da fatan ba matsala. Amsa: Kare na daya daga cikin dabbobin […]

Amsoshin tambayoyi

Tambaya: Cikin azumin nan kare ya cije ni, wurin bai yi wani jini sosai ba. Da na tambaya sai aka ce ai karen ana kai shi allurai don haka kada in damu ban yi komai a kai ba. shi ne nake neman karin bayani da fatan ba matsala.

Amsa: Kare na daya daga cikin dabbobin gida masu hadari, idan aka yi la’akari da yadda siffar yatsunsa masu farata da hakoransa masu kaifi suke. Haka nan a dabbobin gidan ma ba dabbar gidan da ta kai kare illa ga lafiya. A mafi yawan lokuta ke nan karnuka kan zama hadari babba idan ba a kulawa da abincinsu da kiwon lafiyarsu. A wasu lokutan ma ko an ba su abinci, sukan iya raunata mutane – musamman yara idan sun tsokane su. Kare kan iya yakushi kuma yakan iya yin cizo. Idan ya yi yakushi zai iya sa kwayoyin cuta irin na bakteriya (kamar tatanas da sauransu) a wurin ciwon. Idan kuma mahaukacin kare ko wani karen daji ya yi cizo gaskiya ne ba fadar mutane ba ce kawai, zai iya sa wata kwayar cutar bairos wai ita rabies, mai shiga kwakwalwa ta sa ciwon tabin hankali, wadda a mafi yawan lokuta takan kai ga rasa ran mutum. Ita wannan kwayar cuta a yawun/miyau karen take ta yadda idan dai kare na dauke da ita, da ya yi cizo ya fasa wuri ko yaya yake, in dai jini ya fito, to kwayar cutar kan shiga jinin wanda aka ciza, ta tafi kwakwalwa. Ko da kare bai sa kwayoyin cuta a wajen da ya ciza ba, kuma bai sa ciwon rabies ba, babban cizo kan iya wawake naman wurin da aka ciza, hakan ya nakasa mutum.

Alamomin cizon kare ke nan a mafi yawan lokuta bai wuce tsagewar fata da naman wurin ba. A wasu lokuta tsagewar fatar kan yi girman da jini zai yanke ya yi ta zuba. Daga baya ne wato bayan kamar kwanaki biyar ko mako guda, idan wata kwayar cuta ta shiga jiki daga wannan tsaga ake ganin alamun ko mene ne ya shiga. Idan kwayar cuta ta shiga akan iya samun zazzabi. Idan kuma kwayar rabies din ce ma da zazzabi za a fara, bayan kamar kwana goma da cizon. Idan kwayar rabies ce daga zazzabi sai a ga mutum ya fara samun ciwon gabobi, ciwon wuya ko sankarewar wuya da kidimewa da saurin firgita. A wadansu akan samu alamun hauka sosai, a ga mutum kamar ya zautu, yana sambatu. Da yawansu ba sa son taba ruwa ko kuma idan an sa musu ruwa su shide. Wadansu ma har haushin kare za a ji kamar suna yi.

To kai naka yadda abin yake shi ne tunda ka ce karen gida ne da sauki, kuma masu karen sun ce maka ana yi masa allurar kariya daga cutar rabies.To idan wadanda za ka iya yarda da su ne, za ka iya yarda, amma idan ba za a iya yarda da su ba, yana da kyau su nuna maka shaida wato takardar cewa karen na karbar wannan allura loto-loto. Idan ba su nuna takardar shaida ba abin da ya fi shi ne a je asibiti wanda aka ciza ya karbi allurar riga-kafin kwayar cutar.

Ranar Ba Da Jini ta Duniya

Yau Juma’a hukumomin lafiya suka ware domin tallata gudunmawar ba da jini, wadda ake kira Ranar Ba Da Jini ta Duniya. Wannan rana ce ta musamman da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) takan ware a duk shekara domin tunartar da mu amfani da  muhimmancin ba da jini domin taimakon gaggawa ga marasa lafiya a asibitocinmu. Taken wannan rana a bana ita ce ‘Lafiyayyen Jini Domin Kowa.’ Wato a bana an sadaukar da ranar ce domin tuna wa jama’a irin yadda alkaluma ke nuni da cewa har yanzu mace-mace sanadiyyar zubar da jini ko karancin jini za su iya shafar kowa, walau ta wajen haihuwa ne, ko ta wajen hadurran ababen hawa ko a wuraren tashin hankali na yake-yake da ta’addanci.

Makasudin wannan tunatarwa ita ce ta zaburar da mu a daidaikunmu musamman maza majiya karfi masu lafiya mu rika daurewa muna lekawa dakunan ajiyar jini a asibitoci mafiya kusa da mu domin ba da jini dan kadan. Mutum bai sani ba cewa zai iya sanadin ceto ran wani ta wannan hanya. Namiji lafiyayye yana da jini kusan lita 5 zuwa 6 a jikinsa a kowane lokaci da ke zagawa sassan jiki, kwatankwacin galan guda ke nan. Wanda ake diba bai wuce rabin lita ba, wato daya bisa goma ko daya bisa sha biyu na jininsa wanda hakan ba zai sa masa wata matsala ba sai dai idan dama ba ya da cikakkiyar lafiya.

Akwai sauran fa’idojin yin hakan ba ma ga wanda aka bai wa ba, a’a har wanda ya samu ya bayar. Fa’idojin da mai bayarwar zai samu sun hada da:

  1. Gwajin kyauta na ciwon hanta da na ciwon kanjamau
  2. Taimaka wa bargo sake daura niyyar sabunta kwayoyin jini yadda ya kamata
  3. Rage jajayen kwayoyin jini ga wadanda nasu yakan yi yawa haka kawai a wasu lokutan (polycythaemia).
  4. Samun natsuwa da annashuwa idan mutum ya san ya karar da wani da zai amfanu ga wannan jini

A likitance wadanda za su iya ba da jinin sadaka su ne:

  1. Namiji dan shekara 18 zuwa 65, wato ban da tsoho ban da yaro
  2. Masu dan kumari kadan wadanda nauyinsu bai gaza kilo 50 ba, domin kada mutum ya suma, a je ana neman a kara masa jinin shi ma. Domin an sha samun haka
  3. Wanda ba ya wani zazzabi ko mura da sauransu
  4. Wanda ba a yi wa wani aikin tiyata ba a cikin watanni shida da suka gabata
  5. Wanda bai ba da jininsa ba a cikin watannin shida da suka gabata
  6. Wanda shi ma ba a kara masa jini ba a cikin shekara guda da ta gabata
  7. Wanda bai da ciwon Suga ko Hawan jini ko Asma ko Sikila da makamantansu

A wasu kasashe mata ma kan iya ba da jini amma ban da irin kasashenmu tukuna. Ana bukatar mai ba da jini ya dan sha wani dan abu mai ruwa-ruwa kamar lemo ko madara ko da zai maye gurbin abin da za a ja a jikinsa, sa’annan ya kwanta na tsawon minti 15 ya dan huta bayan an ja jinin.

 

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna