Amsoshin Tambayoyi

Na sha ruwan sabuwar rijiya. Bayan awanni kadan sai na kama zawo. Wai da ma akwai matsala ce idan aka sha ruwan rijiya? Daga Malam Ashiru, Katsina   Amsa: Eh, kwarai ai mun sha fada a nan. Ai irin rijiyoyinmu wadanda ake yi kusa da salga ko sokawe, (wadanda ba su wuce nisan fiye da […]

Amsoshin Tambayoyi

Na sha ruwan sabuwar rijiya. Bayan awanni kadan sai na kama zawo. Wai da ma akwai matsala ce idan aka sha ruwan rijiya?

Daga Malam Ashiru, Katsina

 

Amsa: Eh, kwarai ai mun sha fada a nan. Ai irin rijiyoyinmu wadanda ake yi kusa da salga ko sokawe, (wadanda ba su wuce nisan fiye da kafa 50 ba) kuma wadanda ba su yi zurfi sosai ba (wadanda zurfinsu bai kai kafa 100 ba) kuma ba su da marufi, duk ba rijiyoyin da za a sha ruwansu ba ne. Za su iya kawo maka ciwon ciki da gudawa da zazzabin typhoid da atuni da sauran cututtukan da gurbataccen ruwa kan iya jawowa in dai aka sha su kai-tsaye ba a tafasa ba. Ka ga kamar rijiyar burtsatse wadda ake cewa tuka-tuka, ana amfani da wannan ilimin ne wajen gina ta. Za ka ganta a rufe da karfe, kuma tana da zurfi sosai, ga shi kuma ba a gina ta kusa da salga ko wani ruwan kwata. To ita wannan za a iya shan ruwanta, zai iya fin ma na famfo tsabta

 

Na ji ka ba da wata amsa a kan ciwon sanyi. To masu amfani da dakunan ba-haya na jama’a su ma za su iya kamuwa da cututtukan sanyi?

Daga Dauda Mani

 

Amsa: A’a ciwon sanyi sai a tsakanin mutum da mutum ake dauka ba a jikin wani abu kamar bayan-gida ba. A bayan-gida tabbas za a iya kwasar cututtuka amma ba kwayoyin cututtukan sanyi ba.

 

Wai da gaske ne akwai mutanen da ba sa yin hutu wato tusa?

Daga Babangida Yusuf, Nafada

 

Amsa: A’a sai dai a halin rashin lafiya. Wato ba lafiya ba ce rashin yin tusa, tunda akwai iska a ciki wadda ko dai mu hadiye ko kuma abincin da muka ci ya samar da ita. To dole ciki da hanji su fitar da wannan iska idan ba haka ba a yi ta samun kumburin ciki. Iskar da ke saman ciki a fitar da ita ta hanyar gyatsa, wadda ke can cikin hanji kuma ta hanyar hutu.

 

Wai da gaske ne zuma tana iya maganin in’ina? Kuma wane sinadari ne a cikinta ke da maganin?

Daga A.B Barmo, Abuja

 

Amsa: Za ta iya mana tunda a addinance an fada cewa maganin abubuwa ne da dama, duk da dai a likitance binciken sinadaran da kan yi wannan aiki bai zo nan ba tukuna

 

Wai me ke kawo jikin mutum ya rika bashi-bashi ko da kuwa ya yi wanka?

Daga D. R. Z

 

Amsa: Zufa wato gumi shi ke kawo jikinmu ya yi ta tashi, ko da kuwa ka yi wanka. Tunda ka san koda ka yi wanka idan ka sake shiga rana ko wuri mai zafi za ka yi zufa.

Ke nan abin da zai hana ka zufa za ka shafa a wuraren da kake yawan zufar. Idan ka yi wanka ka goge jiki da mayani ka tsane tsaf, sai ka samu wani abu mai tsane zufa da hana zufa ketowa kamar hoda ko roll-on ka shafa. Hoda kamar dustin powder, roll-on ma mai kyau mai busar da fata ba jabu ba.

 

Ni kuma jikina yakan yi zufa ne a bangare guda, wani lokaci bangaren dama wani lokaci bangaren hagun ne kan yi. Ko akwai matsala ke nan?

Daga Usman D. Gombe

 

Amsa: A’a ba matsala. Wannan ma bambancin halitta ne ba ciwo ba.

 

Shin wanka da ruwan zafi zai iya yin illa ga jiki?

Daga Khalil Muhammad

 

Amsa: A’a sai dai idan tafasasshe ne.

 

Ina yawan fita fitsari da dare, domin nakan fita sau 7 zuwa 8 a dare. Na je asibiti an duba ni an mini gwaje-gwaje an ce ba ni da wata matsala. Ina magani?

Daga Jibril Abba, Birnin Kebbi

 

Amsa: A’a haba, ko sau 3 kake tashi fitsari a dare, a ina za a ce lafiya lau ballantana sau 7. Ai ko jariri da wuya idan yana jika mayani sau bakwai a dare. Ka koma likitan da ya duba ka ka ce ya ba ka takarda zuwa wani asibiti na gaba da wannan.

 

Ni ma ina yawan yin fitsari amma da rana. Domin nakan yi sau 7. Ko mene ne matsalar?

Daga Jibrin Aliyu, Kano

 

Amsa: A mafi yawan lokuta, ba kamar tashi fitsari da dare ba, yawan fitsari da rana musamman a yanayi na sanyi ko na damina, ba a cika daukarsa ciwo ba, sai ya dore ya kai lokacin zafi. Don haka ka bari ka gani zai ragu ko kuwa.

 

Ni idan ina cin abinci kawai sai in ji na datse harshena ko lebena. Wannan matsala ce?

Daga Ahmad N.

 

Amsa: A’a ba za ta zama matsala ba, tunda ko masu iya magana kan ce ai tsakanin harce da hakori ma akan samu sabani, wato hakori ya taune harshe. Sai dai idan abin yakan faru kusan kullum ne za a iya cewa akwai matsala, wadda kafin ka nemi magani, ya kamata ka fara da kula wajen cin abinci a rika tauna a hankali a hankali tukuna a gani ko zai daina.

 

Wai da gaske ne cin goro yana da illa?

Daga A.B.M

Amsa: Eh, to watakila saboda sinadarin caffeine da ke ciki shi ya sa ba a ma so a rika yawan ci. Domin shi abin da sinadarin caffeine ke sawa ke nan, wato naci. Shi ya sa za ka ga yawa-yawan masu ci sun kasa bari saboda wannan sinadari. In ban da wannan sinadari ba ma ganin akwai wata illa a goro.

 

 

 

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna