Amsoshin Tambayoyi
Ni ma ina da yarinya wadda idan tana barci komai sanyi sai zufa ta karyo mata a goshi. Ko hakan matsala ce? Daga Dan Tanin Yelwa Amsa: A’a ita ma wannan ba matsalar lafiya ba ce, bambancin halitta ne, misali kamar masu jiki sukan samu haka. Don haka idan tana da dan jiki, kai ko […]
Ni ma ina da yarinya wadda idan tana barci komai sanyi sai zufa ta karyo mata a goshi. Ko hakan matsala ce?
Daga Dan Tanin Yelwa
Amsa: A’a ita ma wannan ba matsalar lafiya ba ce, bambancin halitta ne, misali kamar masu jiki sukan samu haka. Don haka idan tana da dan jiki, kai ko ma ba ta da shi za a iya samun haka. Idan da a ce idan tana barcin jikewa take da gumi shi ne za a iya cewa akwai matsala, amma zufa a goshi kawai ba matsala.
Ina da juna biyu wata tara kuma hoton scanning ya nuna na kusa haihuwa. Zan iya yin doguwar tafiya, in yi wanki, in yi surfe saboda in samu motsa jiki?
Daga Hannatu M.
Amsa: Eh, duk da ana so a rika motsa jiki sosai a karshen ciki domin samun saukin nakuda, ba a so motsa jikin ya yi yawan da zai sa ciwon jiki ko ma haihuwa kafin lokacinta ba shiri. Don haka a kullum za ki iya yin daya kadai daga cikin abubuwan da kika lissafa, amma ba duka ba.
Shin mai irin jini AA wanda bai da ciwon sikila zai iya auren mai AS, wato mai rabin sikila?
Daga Muhammad, Kano
Amsa: Eh, wannan ba matsala, domin a cikin ’ya’yansu ba za a samu mai ciwon sikila ba, sai dai masu rabin ciwon da wasu lafiyayyu. Su kuma ’ya’yan masu rabin ciwon su ne za a ce ba za su auri wani ko wata mai rabin ciwon ba, don kada su yada ciwon a jikokinsu.
Masu lafiya ma, wato AA za su iya auren masu sikila wato SS tunda su ma a ’ya ’yansu ba za a samu masu sikila ba sai dai masu dauke da rabin ciwon. Su a nan dukkan ’ya’yan ne za su samu rabin ciwon (AS), wato ba lafiyayyu (AA) ba.
An ce raba da ke sauka a gida tana da illa ga yara. Ko haka ne?
Daga Nasir Kainuwa Hadeja
Amsa: Eh, haka ne, ba a so gida ya cika raba da yawa, ko kuma ya bushe da yawa. An fi son tsaka-tsaki, wato danshi daidai-wa-daida, domin dukkansu rabar da bushewar wurin za su iya sa mura da cututtukan huhu irin su asma da sauransu.