Amsoshin tambayoyi: A kan ciye-ciye?
Na kasance mai yawan shan sukari, domin ko shayi zan sha sai na sa sukari da yawa. Ko hakan akwai matsala? Daga Haruna U. Hadeja da Aliyu Bala Amsa: Eh, mu a likitance ba kyau irin wannan dabi’a saboda sukari zai iya yawa a jiki. Mukan ce a sha daidai misali, amma ba da […]
Na kasance mai yawan shan sukari, domin ko shayi zan sha sai na sa sukari da yawa. Ko hakan akwai matsala?
Daga Haruna U. Hadeja da Aliyu Bala
Amsa: Eh, mu a likitance ba kyau irin wannan dabi’a saboda sukari zai iya yawa a jiki. Mukan ce a sha daidai misali, amma ba da yawa ba. An sha irin wannan tambaya a nan amma wadansu ko ba sa ji ne, ko suna so a ce ba matsala ce, ba mu sani ba? Mu dai iyakacinmu mu fada, amma dauka ba dole ba ne.
Shin yawan shan gahawa (coffee) yana da fa’ida ga jiki, domin ina yawan shansa.
Daga Hussaini Kadarko Katsina
Amsa: Kai ma an sha amsa irin wannan tambaya taka, inda aka ce duk abin da aka ce ana cinsa ko ana shansa, ko da ruwa ne kuwa, in dai ya wuce kima to maimakon amfani sai dai ma ya sa illa. Don haka saisaici shi ne ake bida a irin wadannan kayan sha.
Ina tambaya nce kan madaran sukudaye da fashon, mene ne amfaninsu ko illarsu a jikin dan Adam?
Daga Abdulkadir Ikeja, Legas
Amsa: Na dai na san kayan maye ne, kuma kayan maye ba sa yi wa jiki komai sai illa komai karancinsu, komai yawansu.
Yawan shan ruwa da yawan fitsari matsala ce ga lafiya?
Daga Khalifa Pandogari
Amsa: Af, ga shi kuwa a can mun ce ko yawan shan ruwa ba lafiya ba ne, ballantana a ce ga yawan fitsari. Ai zance ya kare sai an binciki lafiya.
Fitsari sau biyu a rana fa, akwai matsala?
Daga Yakubu Mukhtar
Amsa: A’a ba matsala.
Shin ko ana cin ganyen gwaza da ganyen rogo? Domin mu zubar da su muke a bola
Daga Ilyasu Wakili Akuyam
Amsa: A’a ni ma ba na ci Malam Ilyasu sai dai shi gwazan da rogon, amma ba ganyensu ba. Ka san cin kayan ganye a wasu lokuta al’ada ce. Za ka iya zuwa wani gari ka tarar ana ci, amma dai ina jin ba a kasar Hausa ba, tunda da ana ci da tsoffin garinku sun ce ku daina zubarwa. Amma fa watakila akwai wani sirrin magani a ciki, domin duk wadannan ganyayyaki idan ka lura da yawa-yawansu, in ma dai abinci ne ko magani, wato kadan ne za ka ji an ce guba ne. Irin wannan ilimin sanin sirrin ganyaye sai masu hada magunguna walau na gargajiya ko na asibiti, ba likita ba.
Wai da gaske ne idan aka hada dafaffen kwai da ayaba aka ci yanzun nan za a mutu?
Daga Fauziyya Habib Moriki
Amsa: A’a ban taba ci ba ballantana in sani, amma dai a Intanet an nuna alamun shaci-fadi ne, wadansu da yawa sun ce sun ci ba su mutu ba. Kin san amma fa ci-maka takan bambanta daga wani zuwa wani. Wani idan ya ci wannan hadin zai iya kwana lafiya, wani kuma sai dai kwanan asibiti watakila saboda cikinsa ba zai iya sarrafa abin da aka gamza masa ba. Ala aiyi halin dai abin da mukan ce shi ne, kowa ya san mene ne bai karbi cikinsa ba, ya guje shi.
Shan magarya fa tana da fa’ida ga jiki ko illa?
Daga Zubairu Sule-Tankarkar
Amsa: Eh, kwarai da muna yara mun sha magarya sosai amma ba na jin ta taba ba mu wata matsala, sai ma wankin ciki da mukan ji tana yi mana tunda tana da sinadarin fibre. Amma fa watakila wani ba ta karbe shi ba.
Mene ne amfanin muruci a jikin dan Adam?
Daga Mustapha Abdussalam
Amsa: Shi ma muruci da mun ci shi sosai, shi ma kamar wankin ciki yake da tsane maiko a ciki, domin shi ma yana da sinadarin fibre mai yawa. Sai dai shi ma watakila ba kowa ya iya cinsa ba.
Shekarata 21 amma na kasance ba ni da kiba, shi ne aka ba ni shawara in rika shan hadin kunun waken soya da gyada da dawa. Shi ne nake neman karin bayani a kan wannan hadi.
Daga M.K
Amsa: Hadin Tom-Brown ke nan in ji ’yan boko, hadi ne mai kyau, zai kara wa wadanda ba su da jiki jiki daidai misali, ba kiba ba, domin kada ki bidi kiba ciwo ne.
Me yake sa mutane sirara su fi masu kiba lafiya?
Daga Aminu Muhammad
Amsa: Haka ne saboda ai kibar ita kanta ma ciwo ne mai jawo wasu cututtukan.
Yawan yin hutu ne ke damuna amma sai na yi alwala zan yi Sallah, domin sai na yi kamar sau 10. Shi ne nake neman magani.
Daga Husna Kaduna
Amsa: In dai sai kin yi alwala kadai kike jin wannan, ba ko da yaushe ba, to ba likita za ki nema ba, Malami za ki gayawa. Malami ba boka ba fa, ba kuma mai maganin gargajiya ba, Malamin addini sosai. Idan kuma a mabambantan lokuta ne ba sai lokacin Sallah ba kike samu to asibiti za ki bangaren kwarraru a kan ciki wato bangaren GIT
Me ke sa ganin jiri ne, idan an dade kwance ko zaune an mike sai jiri?
Daga Lawal S.
Amsa: Abubuwa da dama wadanda ke nuni da rashin lafiya za su iya kawo wannan. Ko hawan jini ko karancinsa, ko ciwon kunne, ko wasu magunguna duk za su iya sa haka. Mai samun wannan yana bukatar ganin likita.