Amsoshin tambayoyi: Ciwon gabobi

Idan ina gudu lokacin atisaye kirjina na bugawa da sauri-sauri, kuma ni ba tsayawa na yi ba da atisayen. Ko akwai matsala? Daga Ayyuba Yahaya, Kano da Abba Lakata Amsa: Eh, idan mutum na gudu na atisaye zuciyarsa za ta rika bugawa da sauri mana, ba wani abu ba ne, don har yakan iya kai […]

Amsoshin tambayoyi: Ciwon gabobi

Amsoshin tambayoyi: Ciwon gabobi

Idan ina gudu lokacin atisaye kirjina na bugawa da sauri-sauri, kuma ni ba tsayawa na yi ba da atisayen. Ko akwai matsala?

Daga Ayyuba Yahaya, Kano da Abba Lakata

Amsa: Eh, idan mutum na gudu na atisaye zuciyarsa za ta rika bugawa da sauri mana, ba wani abu ba ne, don har yakan iya kai bugu 200 cikin minti guda. A ka’ida idan mutum na zaune ba gudu yake ba bugun zuciya ba ya haura bugu 100 cikin minti guda. Sai idan wannan bugu ya haura 200 ko haki ya ki sakin mutum, ko kirji ya fara ciwo, shi ne za a ce akwai matsala.

 

Ni ciwon gabobi ne da ni wanda idan ya tashi ba na iya tafiya. Na taba yin jinya a wani asibiti amma da aka sallame ni na dawo sai matsalar ta sake dawowa. Yanzu ma mahaifiyata na da irin matsalar. Ko shin ana iya gadon irin wannan ciwo ke nan?

Daga Aliyu Ibbi, Taraba

 

Amsa: Eh, ana iya gadon cututtukan matsalolin gabobi, musamman ma ciwon sanyin kashi na rheumatism. Su matsalar wasu asibitocinmu shi ne rashin cikakken bayani. Mutum ya kwanta ya yi jinya amma ba a gaya masa ko me ke damunsa ba. In dai ciwon sanyin kashi ne haka zai rika yi yana tashi yana kwanciya, wato dole sai dai ka dauwama kana shan magani ke nan.

 

Wai da gaske ne mai hawan jini ba ya warkewa sai dai mutu-ka-raba?

Daga M.B.S Gaye

 

Amsa: Eh, kuma a’a. Eh, saboda hawan jinin nau’i-nau’i ne. Idan na gado ne, wato iyaye da kakanni suna da shi, zai wahala ya tafi. Idan wani abu ne ya kawo daban, kamar kiba ko cin gishiri ko ciwon koda, idan aka dauki mataki aka rage cin gishiri, aka rage kiba, ko aka yi maganin ciwon kodar, to, zai tafi.

 

Da dadewa an taba yin tambaya a kan wankin ciki sai ka ce babu wani abu mai wankin ciki. To amma yanzu na ji kana magarya na wanke ciki. Shi ne ban gane ba.

Daga Matar B.Z, Kaura-Namoda

 

Amsa: E, cewa muka yi kada wani ya rude ku da maganin wanke ciki domin akwai nau’o’in abinci masu wannan aiki cikin sauki ba sai an nemi magani ba. A mafi yawan lokuta ciki na wanke kansa da kansa amma akwai nau’o’in abinci da za su iya gaggauta hakan. Misali idan mutum ya kwana biyu bai je bayan-gari ba, idan ya sha lemon bawo da abin da ke cikinsa, ko ya ci magarya, ko wani ganye mai yawa, zai wahala ya kwana bai zaga ba. To irin wannan muke nufi, shi ya fi a kan a ce sai an sha magani domin maganin zai iya yin illa.

Amma idan likita ne sosai ya rubuta, ba mai magani a titi ba, ba komai. Domin akwai lokutan da cikin kan iya cushewa ya kasance kowane irin kayan ganye ko na ’ya’yan itatuwa aka ci ba ya saki, sai magani.

 

Mene ne amfanin ganyen shuwaka?

Daga Ramatu Musa, Lafiya

 

Amsa: Kamar sauran ganyaye tana hana cushewar ciki, sa’annan masu maganin gargajiya suna maganin zazzabin maleriya da ita.

 

Ina da ciwon basur ne wanda ya ki jin magani. Sai wani likita ya ce mini sai dai a yi tiyata. To amma tsoro nake ji domin na ji ana cewa sau da dama idan aka yi wa mutum tiyata mutuwa ake ba a nasara.

Daga Sabi’u A. Kano

 

Amsa: To ashe ciwon ba cinka yake sosai ba ke nan in dai har ka gwammace ka zauna da shi da a yi maka aiki. Rai da mutuwa a hannun Allah suke, idan ka yi tawakkali za a ci nasara. A kiyasin likitanci ba a sa lissafin tiyatar basur cikin tiyata masu kisa ma. Akan sa tiyatar zuciya da ta matsalar mama da ta makoshi ko ta hujewar hanji a cikin lissafin, amma ba tiyatar basur ba, domin karamar tiyata ce.

 

Ni kuma gyada nake ci a kullum da safe har sai da ta sa ni kiba. Ina mafita?

Daga Al-Amin Muhammad

Amsa: Kwarai gyada na iya sa kiba kuwa idan aka nace mata kullum. Watakila kai sabo ne a wannan shafi da za ka san wannan shafi ba ya shiri da masu nace wa abu daya a kullum ya kasance sai an ci. Mafita idan za ka iya bari ka rika ci jefi-jefi, idan kuma ba za ka iya bari ba to…

 

Idan ina da ciwon gyambon ciki zan iya shan magani a kullum ko da ciwon bai motsa min ba?

Daga Shazali A. Kano

Amsa: Eh, ai da ma magungunan warkar da ciwon olsa ana ba da su ne mutum ya sha a jere na tsawon makonni ko watanni har sai ya warke, koda kuwa ya ji sauki to yadda aka ce din nan ana so mutum ya karasa wa’adin magungunan. Idan mutum ya gama wannan wa’adi a wasu lokuta zai iya jin tashin acid, zai iya shan na kwantar da acid kamar na ruwa din nan mai minti. Amma bai kamata a sake sawo irin wadancan magunguna manya da aka rubuta na watanni ba, ba da sanin likitan da ya fara rubuta su ba.

 

Ko cin duma da mutane kauye ke yi ta hanyar kwado yana jawo ciwon gwaiwa kamar yadda wadansu suke fada?

Daga Mahadi A. Da Idris, Kazaure

 

Amsa: A’a a likitance aikin karfi ko yawan tari ko ma dai duk wani abu irin wannan da kan sa takura ko pressure a wajen kugu shi ke kawo gwaiwa ba cin wani nau’i na abinci ba.

 

Nakan ji jikina na jana wato shocking idan na taba wani abu kamar tufafi ko bango. Ko ciwo ne?

Daga Maikudi 94 Bichi

 

Amsa: A’a ba ciwo ba ne bambancin halitta ne. A hannayen akwai maganadisu wato caji akasin wanda ke bangon ko tufafi ne shi ya sa suke janka. Wato idan aka samu positibe a hannunka aka kuma samu caji negatibe a tufafin idan ka taba zai iya janka ko ma ka ga dan tartsatsin haske. Yawan murza hannaye kafin taba wasu abubuwa da ka san suna janka zai sa cajin ya bace.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno