Amsoshin tambayoyi daban-daban

Yadda za a gane magani na jabu Da gaske ne akwai magungunan asibiti da ba sa aiki? Domin wadansu sai su yi rashin lafiya a yi ta magani amma jiya-i-yau Daga Imran Yunusa Amsa: Kwarai kuwa da gaske ne Mallam Imrana domin kuwa a kasar nan ta mu akwai kasuwannin boge na hada magunguna, sa’annan […]

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Tantance Magani

Yadda za a gane magani na jabu

Da gaske ne akwai magungunan asibiti da ba sa aiki? Domin wadansu sai su yi rashin lafiya a yi ta magani amma jiya-i-yau

Daga Imran Yunusa

Amsa: Kwarai kuwa da gaske ne Mallam Imrana domin kuwa a kasar nan ta mu akwai kasuwannin boge na hada magunguna, sa’annan kuma akwai magunguna na jabu da akan shigo da su kasuwanninmu daga waje. Ka ga matsalar fuska biyu ne ma da ita kenan.

Wato ban da kwayoyin maye da aka addabemu da su, akan shigo da jabun magunguna daga kasashe kamar na Sin da India da Pakistan. Wasu ba jabu ba ne kai-tsaye sai dai a ce ba ingantattu ba ne dari-bisa-dari. Wato a kwayar magani maimakon a sa magani dari-bisa-dari sai a sa arba’in-bisa-dari, sauran kuma a cike da wata hoda kamar garin alli, ko rogo ko fulawa ko ma sitachi kawai.

To idan haka magani yake kuwa ka ga ba zai samu galaba akan wani ciwo ba. Magungunan da aka fi samun jabu a cikinsu su ne magungunan da muka fi amfani da su, wato magungunan ciwon zazzabin maleriya da na tafot. To amma a yanzu abin ya fara ma wuce wadannan.

Kai ko a makon nan kungiyar masu kula da ciwon ido na gilakoma a kasar nan sun yi korafi a kan wani maganin digawa na gilakoma da ba ya aiki, wanda hakan ta sa kamfanin da ke hada maganin a kasashen Turai ya ce a janye duk magungunan daga kasuwa saboda ya yi bincike ya ga an gurbata kasuwar maganin tasa da na jabu.

Da ma can dai hukumar killace abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC ta samar da wani tsari da take kira Mobile Authorisation Serbice (MAS) inda a jikin duka kwalayen magungunan da akan yi a kasar nan da ma wadanda akan shigo da su takan yi wata lamba da za a kankare kamar a katin waya, idan aka kankare sai a aika lambobin da aka gani karkashin wurin a wata lamba da sukan rubuta a kasan lambobin. Idan maganin jabu ne za a turo maka sako cewa jabu ne, idan kuma gangariya ne za a turo maka sakon cewa gangariya ne. Wannan aikin kyauta ne domin ba za a caji ko kwabo a wayarka ba.

To idan mutane suka dauki wannan tsari aka ci gaba a haka za a samu raguwar magungunan jabu. To amma idan ba a bin wannan tsari ana sayen magunguna kai-tsaye ba bincike ana amfani da su, za a karawa masu gurbata magunguna karfin-gwiwa. Magungunan da ba a ga irin wannan maki ba sai an tambayi masu kyamis dalili.

Me yake kawo mutum ya rika yawan fitar da iska alhali ba wani kumburin ciki?

Daga A.A Sani, Bauchi

Amsa: Cin abinci mai samar da gas kamar su wake da doya da rogo su ne ire-iren abincin da sukan sa mutum ya rika yawan fitar da iska

Yin wanka da ruwan zafi yana da amfani ga lafiya ko kuwa?

Daga Khalil M.A

Amsa: Eh, idan lokacin sanyi ne ba.

Ni kuma idan na ci abinci babu barkono sai in ji abincin ba dadi. Ko yawan cin barkono zai iya mini illa?

Daga Faisal Usman Mayo Belwa

Amsa: Akwai wadanda idan suka ci barkono yana musu illa a ciki su rika samun zafin ciki, akwai kuma wadanda ba sa samu. Idan kai ma ba ka samun zafin ciki to ba komai, amma idan kana samun zafin ciki to ka daina ci.

Idan na yi wani aiki sai kirjina ya rika zafi. Amma idan ban yi wani aiki ba ba ya mini zafi. Ko hakan matsala ce?

Daga Amira K.A.U

Amsa: Eh, matsala ce wadda ya kamata a je a bincika

Namiji ne dan marainansa daya. Wannan matsala ce ko a’a?

Daga: Sabo Alheri

Amsa: Eh, da matsala. Da ma akan haifi wadansu da maraina daya a ciki, daya a waje. Yawanci idan aka duba mutumin a asibiti akan gano dayan a cikin ciki. Idan ma ta kama za a iya sauko da shi.

Ni dai a kowane lokaci idan na ci abinci komai dadinsa sai na yi amai shi ne na ga wannan lamba a jarida. Ina so a taimaka.

Daga Musa B.N

Amsa: A’a a asibiti ne za a iya taimaka maka a duba ka a gano ko mene ne matsalarka. Nan kawai karin bayani za a iya maka

Me ya sa duk lokacin da na ci gauta sai cikina ya yi ciwo tun ina yaro har yanzu. Mene ne maganinsa?

Daga Yarima A.

Amsa: Watakila gauta bai karbi cikinka ba ke nan. Magani shi ne sai ka daina ci ka huta.

Da gaske ne miyar kuka tana bata harshe da kwakwalwar mai shanta?

Daga A.B.A, Karmo

Amsa: A’a ba gaskiya ba ce, ai kuka na daya daga cikin abincin Malam Bahaushe mai dimbin amfani saboda sinadaran bitaman iri-iri da ke cikinta

Shekara 12 ke nan da shan magungunan ciwon TB. Da na gama na koma an sake aunawa babu ciwon amma har yanzu ban maida jikina ba. Shi na ke neman magani.

Daga Muhammad S. Agege

Amsa: A’a ina ganin abinci mai kyau mai gina jiki za ka lazimci ci idan kana da hali, ba magani za ka nema ba tukun

Ni hakorana ne ke yin baki domin yawan shan shayi. Shin ko akwai matsala?

Daga Ilya Daiyabu

Amsa: Eh, akwai matsala mana, tunda ga shi har yawan shan shayi ya fara bakanta maka su. Watakila ba ka kula da su sosai ne, domin akwai masu shan sigari ma ba shayi ba, in ka ga hakoransu fari fat ba ka ce suna busa hayaki ba saboda yawan kula.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50