Amsoshin tambayoyi daban-daban

Ni dalibar kimiya ce. Ina so a bambance mini wadannan sinadarai na jiki wato hormones da enzymes Daga A. Danfuloti   Amsa: Dukansu sinadarai ne da ke kamanceceniya da juna, domindukansu jikine ke sarrafasu idan yana bukatar a yi wani aiki. Masu ba da umarnin fara wani aiki a jiki su ne hormones, wato masu […]

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Ni dalibar kimiya ce. Ina so a bambance mini wadannan sinadarai na jiki wato hormones da enzymes

Daga A. Danfuloti

 

Amsa: Dukansu sinadarai ne da ke kamanceceniya da juna, domindukansu jikine ke sarrafasu idan yana bukatar a yi wani aiki. Masu ba da umarnin fara wani aiki a jiki su ne hormones, wato masu trigger a fara aikin,su kuma enzymes su ne sinadaran da ke saukaka aikin wato shi ne za ki jiana ce musu catalysts. Misali a yanzu lokacin azumi idan jiki ya yi awanni da dama bai ji an samasa abinci ba, to zai bukaci a hada sukari daga abincin da aka ajiye a hanta ko a teva ko a koda, domin jiki ya yi amfani da shi kafin a sha ruwa. Sinadari mai ba da umarnin haka shi ne hormone na glucagon. Da ya ba da umarni sai a fara aikin, amma kafin a samar da sukarin sai an sarrafa abincin da aka ajiye din mataki da yawa. To a kowane mataki, akwai sinadarin enzyme daban mai saukaka aikin, ta yadda idan babu su ba za a iya samar da sukarin ba. Duk wannan aiki na faruwa ne a cikin dukanin kwayoyin zarra na cell da ke cikin hanta ko koda ko teva a lokaci guda. Ba wannan kadai ba duk wani abu da jiki zai yi ko motsi ne sai an bi wadannan ka’idojin. Misali sinadarin hormone na acetycholine shi ke ba da umarnin aikin motsa tsokar jiki, inda sinadaran enzymes da yawa za su shigo su taimaka a saukaka aikin.

Wani bambanci kuma tsakaninsu shi ne shi sinadarin hormone sai an aikashi daga wani sashe na jiki zuwa wurin da zai ba da umarnin, su kuma enzymes a nan cikin kwayar cell suke. Misali, shi glucagon da ke ba da umarnin sarrafa suga, daga nane-bango wato pancreas ake sakarsa a aikashi ta jini wurin da zai yi aikin. Sa’annan a sunayensu ma za ki iya bambance su. Yawanci (ba duka ba) sunayen sinadaran hormones suna karewa ne da -one ko -on ko -ol, su kuma sunayen sinadaran enzymes suna karewa ne da -ase, kuma sunayen sun fi na hormone tsayi.

 

Ni idan na ci taliyar indomi da dare to fa har gari ya waye a ranar ba zama sai zagawa. Mece ce shawara?

Daga Murtala Muhammad Kaduna

 

Amsa: Watakila cikinka ne bai karve Ka ba duk da dai cewa ba ka fadi ko tana maka haka da rana ba. Ni idan ni ne sai in daina cin taliyar da dare sai dai ko da rana idan ba ta lalata cikin.

 

Na saba kwana a shago kowane lokaci, amma kwanan nan da zafi ya yi yawa na fito waje na kwana sai na tashi da mura me zafi, sai mutane suke cewa hasken farin wata ne yake sa wa. Idan hasken ne yake sa wa a bamu hanyoyin da za mu bi mu kare kanmu.

Daga Khaleefa Umar R/Lemo

 

Amsa: A kimiyyance kwayoyin virus da canjin yanayi ne kan iya sa mura. A likitance babu hanyoyin kariya daga mura tunda babu hanyar da za a kiyaye canjin yanayi ko kamuwa da kwayoyin virus, kuma mahalukin da zai ce maka bai tava mura ba, walau ta kwayoyin cuta ko ta canjin yanayi. Su kwayoyin cutar suna iskar da muke shaka, don haka sai dai a daina shakar iskar idan ana so a kiyaye kwayoyin wanda ka san ba zai yiwu ba.

 

An ce karas ana masa taki da bayan-gida, in gaske ne hakan ba zai haifar da cutuka ba?

Nasiru Kainuwa Hadejiya

 

Amsa: Kwarai amfani da taki mai ba-haya zai iya janyo matsalar cutuka mana irinsu kwalara da typhoid da atini, tunda karas ba dafa shi sosai yawanci ake ba kafin a ci. Idan ma aka dafa sosai amfanin na iya mutuwa. Idan ka san gonar da ake wannan ta’annati sai ka daina sayen kayan lambunsu ka kuma kai rahotonsu ga hukumomi

 

Na dauki tsawon shekaru uku ina bayan gida da jini. Shin wannan wace irin matsala ce?

Daga Aliyu A. Tsanyawa

 

Amsa: Akwai ire-iren binciken da ya kamata a maka a tantance dalili, domin akwai abubuwa kamar uku zuwa hudu da za su iya jawo irin wannan matsala taka. Sai ka daure ka je babban asibiti likita ya duba

 

Mahaifiyata ce dunduniyar kafarta ke mata ciwo idan tana tafiya. Da ta taka kamar na tsawon mintuna 10 sai ciwo. Wannan shi ko matsala ce?

Daga Isa A. Shani

 

Amsa: E, matsala ce, ita ma sai ta samu babban asibiti an duba kafar an yi aune-aune da gwaje-gwaje watakila ma har da hotuna.

 

Ina da aboki mai yawan tari domin ko barci ba ya iya yi domin yawan tari. Ya sha magunguna har ya gaji shi ne nake neman masa shawara

Daga Yakubu Musa, Jega

 

Amsa: Watakila sai ya je an auna kirjinsa da jininsa majinarsa, an kuma dauki hoton kirjin kafin a san wane irin tari ne. Da alama da ka ake shan maganin. Idan aka gano takamaimai dalili, da an ba shi maganin musabbabin matsalar abin zai lafa

 

Hakorina ne ya yi kogo yana mini ciwo. Na je aka ba ni magani amma bai daina ba. ko mene ne mafita?

Daga Aminu Isyaku Kafur

 

Amsa: Mafita ita ce a cike maka ramin a asibitin hakori.

Wai me ke kawo ciwon yatsa ne da kan kumbura ya yi ta zogi? Ko shin ana gadonsa? Kunshi da ake yi a gargajiyance da gaske zai iya maganceshi?

 

Shi idan ya kama mutum tun da wuri me za a yi kafin abin ya yi nisa?

Daga Husaini Danjari, Katsina

 

Amsa: Idan na fahimta kana nufin ciwon kakkare. Kwayoyin cuta ne kawai ke shiga karkashin fata a hannayen da ba a yawan tsabtacewa, su kawo wannan zogi da kumburi. Idan haka ta faru har yanka wurin ake a fitar da diwa kafin a ba da magani. Ba mu sani ba ko lalle yana magance kwayoyin cutar, amma dai magungunan asibiti na antibiotic suna maganceta musamman a farko-farkon ciwon. Amma idan ya kumbura sai an yanka kafin a ba da magani

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50