Amsoshin tambayoyi: Hanyoyin kariya daga ciwon sarke-hakora
Ina son a yi mini bayani kan ciwon tatanas wato sarke-hakora. Na ga mafi yawan wadanda ciwon ya kama ba sa kai labari. Shin ba a yin rigakafinsa da zai kai tsawon shekaru ne? Amsa: Eh, kwarai duk da cewa an rage samun aukuwar wannan ciwo, sakamakon allurar rigakafinsa, har yanzu a kan gan shi […]
Ina son a yi mini bayani kan ciwon tatanas wato sarke-hakora. Na ga mafi yawan wadanda ciwon ya kama ba sa kai labari. Shin ba a yin rigakafinsa da zai kai tsawon shekaru ne?
Amsa: Eh, kwarai duk da cewa an rage samun aukuwar wannan ciwo, sakamakon allurar rigakafinsa, har yanzu a kan gan shi jifa-jifa. Ciwo ne mai hadarin gaske kamar yadda ka ce, wanda da wuya wanda ya kama ya kai labari.
Sarke-hakora nau’in ciwo ne da kan iya kama kowa, manya da yara, kuma kwayoyin cuta na bakteriya da ake kira Clostridium tetani ke haddasa shi, kuma suna nan a kowane yanki na duniya. Wadannan kwayoyin cuta a cikin kasa suka fi rayuwa. Idan suka samu suka shiga jiki sai su rika samar da wata guba da kan kama jijiyoyin jiki su hana wurin motsi.
Yadda ake kamuwa da ciwon sarke-hakora
Kwayoyin na shiga jiki ne yayin da mutum ya ji rauni komai kankantarsa (ko yanka ko kujewa ko gyambo ko kuna ko cizon wata dabba), kuma bai dauki matakin wanke ciwon da yin allurar tatanas ba. Shi kuma jariri yakan dauka a jikin abin da aka yanke cibi da shi, in ba mai tsabta ba ne.
Bayan kamar kwana hudu zuwa mako biyu da yanke cibi ko yin rauni, gubar da kwayoyin cutar ke saki ta fara barna, za a ga jariri yana ta amai da zazzabi da yawan kuka da kin karbar mama. Wadannan su ne alamu na farko, in ba a dauki matakin kaiwa asibiti ba, za a ga wani bangare na jikin jariri ko duk jikin gaba daya yana jijjiga, ko yana sandarewa.
A manya kuwa za a fara jin muka-mukai sun cije, hakora sun sarke, sai wuya ya sandare, a kasa hadiyar ruwa ko abinci sanadiyar wannan guba ta kwayoyin cutar. In ba a dauki mataki ba, haka za a ga duk jiki ya sandare daga sama zuwa kasa, wato daga kai har zuwa kafa, mara lafiya na bankarewa. Yawanci wadanda suka fara wannan sandarewa ba sa kai labari ko an je asibiti.
Hanyoyin kariya daga wannan ciwo
Allurar rigakafin kamuwa da ciwon sarke-hakora ita ce hanyar da aka tabbatar za ta kare mutum daga wannan ciwo. Saboda haka:
- Kowa da kowa ya samu a rika yi masa allurar rigakafin sarke- hakora akalla sau daya a cikin shekara goma. Rigakafinta yakan kai shekara 10, sai a rika sabuntawa
- Mata masu ciki su rika zuwa awo domin a wurin ana ba da allurar rigakafin wannan ciwo ga jaririn da ke ciki.
- A rika kai yara allurar rigakafi idan sun tasa domin su samu a kara musu ita
- Idan yaro ko wani babba ya ji rauni, bayan zuwa asibiti an wanke ciwon, an ba da magunguna, to a tabbata an karbi allurar tatanas don yin rigakafi
- A tabbatar ungozoma mai karbar haihuwa a gida tana amfani da sabuwar reza ko aska wajen yanke cibi, ba tsohuwar reza ko aska ba.
- Manoma su ma su rika zuwa karbar wannan allura, su kuma rika amfani da takalman ruwa irin na roba domin kiyaye jin rauni a kafa
Sauran amsoshin tambayoyi
Ta yaya mutum zai gane cewa jini ya yi masa yawa a jiki? Kuma daga iya maki nawa ne ya kamata a fara ba da jini?
Daga K.B
Amsa: Daga maki 40 cikin 100 zuwa sama na awon jini na PCB ana ganin mutum zai iya ba da leda daya ta jini ba tare da ya galabaita ba. Daga maki 50 cikin 100 kuma na awon, ana ganin kamar jajayen kwayoyin jini sun yi wa mutum yawa sai ya je ya bayar da wani kaso a asibiti. Amma bayan ’yan watanni yana da kyau a sake dubawa a gani ko makin ya sake haura wa 50 din. Idan ya sake haurawa sai an yi masa wasu aune-aune domin tantance ciwon yawan jajayen kwayoyin jini wato ciwon polycythemia. Domin shi ne abin da ya fi kawo yawan jini fiye da kima a jiki
Na kasance ba na samun isasshen barci, ko na kwanta ba ya dauka ta, kuma nakan ji jikina yana min ciwo
Daga Mubarak Maccido
Amsa: Abin da ya fi kawo rashin barcin dare shi ne barcin safe ko na rana. Idan kana yawan yin barcin safe ko na rana na tsawon lokaci za ka rika ganin barcinka na dare yana raguwa. Idan a haka ne to wannan ba matsala ba ce.
Amma idan kai kullum ba ka samun barci na dare da na rana to tabbas akwai matsala. Ko dai akwai wani ciwo ko kuma akwai wasu abubuwa da kake sha na kwayoyin magani da kayan shaye-shaye na shayi da kofi da sauransu. Don haka ka binciki kanka. Idan ka kasa gano dalili to sai ka ga likita ido-da-ido.
Shin da gaske ne shaye-shayen coffee da yawa yana sanya bugun jinin mutum wato BP ya hau?
Daga Abdulkarim A. Maiduguri
Amsa: A’a a likitance gado da yawan cin gishiri ne ke sa karfin bugun jini ya hau. Sai dai a wasu lokuta akan iya samu sanadiyar rashin samun isasshen barci da hutu. Idan mutum yana yawan shaye-shayen abubuwan da za su hana shi sakat ya daina samun hutawa ko barci isasshe, to karfin bugun jinin zai iya hawa.
Ni ma ina son a yi mini bayani a kan yawan shan wani shayi na ’yan Nijar, wanda yanzu ba ma sai ’yan Nijar ba, wannan dabi’a ta zama ruwan dare. Ni na kasance idan ban sha wannan shayi ba ba ni da wani sakat.
Daga Umar Abaji, Kebbi.
Amsa: Eh, duk wani abu da aka nace masa ana amfani da shi, har ta kai idan ba a yi amfani da shi ba jiki na samun rashin lafiya, to wannan abu ya zama kwaya, wato ya zama kayan maye. Sai mutum ya san yadda ya yi ya nisance shi. Idan mutum ya kasa magance abin shi kadai, sai ya nemi taimakon likitan kwakwalwa.
Da ma ai haka shan kwaya yake farawa, abu ne ake so a yi amfani da shi sau daya ko sau biyu a rana misali, a’a sai wadansu su mayar da shi kamar ruwa, shi ke nan idan kwakwalwa ta saba da wuya ta so ta rabu da shi. Misalan wadannan har da shayi da su coffee da su gadagi da tiramal da sauransu.
Ni kuma na ga hannuna ne na saba, shin hakan yana nuni da wata matsala?
Daga KSK Pandogari
Amsa: A’a ba wata matsala, yana nufin hannunka na yawan bushewa ne watakila. Yawan shafa mai mai danko kamar basilin zai magance ta.