Amsoshin tambayoyi (II)

Salam, barka da yau.Ina da wata tambaya ce. Ni na kasance ina mai amfani ne da wayar hannu wajen shiga facebook. Ina ganin wasu in sun rubuta sako a shafinsusaisunanwayar ya bayyana. Ni kumawaya ta Samsung ce,amma na kamfanin at&t. Shin, zai yiwu ni ma in na rubuta sako sunan wayar ya bayyana ga abokaina […]

Amsoshin tambayoyi (II)
Amsoshin tambayoyi (II)

Salam, barka da yau.Ina da wata tambaya ce. Ni na kasance ina mai amfani ne da wayar hannu wajen shiga facebook. Ina ganin wasu in sun rubuta sako a shafinsusaisunanwayar ya bayyana. Ni kumawaya ta Samsung ce,amma na kamfanin at&t. Shin, zai yiwu ni ma in na rubuta sako sunan wayar ya bayyana ga abokaina kuwa? Ka huta lafiya.  – Hashim Yusuf
Wa alaikumus salaam Malam Hashim. Wannan abu da kake gani ba na tunanin masu rubuta sakonnin ne ko kuma wayar, sai dai irin masarrafar Dandalin Facebook da suke amfani ita wajen shiga shafinsu, wanda ko dai da wannan masarrafar ne wayar tazo da ita, ko kuma saukar da masarrafar suka yi daga baya.  Akwai masarrafai (Apps) na shiga facebook (Facebook Apps) da wayoyin salula ke zuwa da su da yawa, sannan akwai wadanda wasu suka gina suka zuba a cibiyoyin kasuwanci da wayoyin salula ke zuwa da su, irin su “Store” a wayoyi masu babbar manhajar “Windows Phone,” da “Play Store” ko “Google Store” ga wayoyi masu dauke da babbar manhajar “Android” da dai sauransu.  Ba wai wani abu bane da masu wayar keyi wajen shigarwa.  Misali da zan baka shi ne nau’in masarrafar shiga Dandalin Facebook da wayoyin Blackberry ke zuwa da ita.  Galibi, idan ka shiga Dandalin Facebook da ita, har ka yi rubutu a shafinka (wato “Wall” ke nan) nan take masarrafar za ta nuna sunanta a karkashin rubutunka, misali: “Using my Blackberry 9700.”  Wannan rubutu da kake gani, wanda ya kirkiri masarrafar ne da kanshi ya tsara mata, cewa: “A duk sa’adda aka yi rubutu a shafi, ki rubutu: ‘Using my Blackberry 9700’ a kasan sakon.”  Wannan, a ilimin gina manhajar kwamfuta ana kiransa “Automated message.”  Mai wayar ko ita kanta wayar salular ba su da hakkin sanya wannan rubutu sai dai masarrafar da aka yi amfani da ita wajen rubuta sakon da zuba shi a inda aka zuba shi.  Masarrafar ce ke dauke da sakon ba wayar ba.  Ita wayar kawai aikinta shi ne ta baiwa masarrafar damar aiki kamar yadda aka gina ta.  Don haka ba zan iya ce maka ga irin nau’in wayar da za ka yi amfani da ita wajen yin wannan ba, domin ya danganci wace irin masarrafa ce: mai dauke da wannan tsarin ne, ko wata ce daban.  Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan ka wuni lafiya.  dazu na kalli shirin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Sunna Tb, shi ne na samo adireshinka a Dandalin Facebook.  Yanzu haka na zama mamba na shafinka.  Naji dadi sosai Allah ya saka da alheri bisa wannan kokari da kake yi wajen wayar da kan Musulmi da ma duk mai jin harshen Hausa.  A karshe, ina so ka dan yi mini karin bayani game da wasu manhajoji  na Google Store.  Idan ina so in sayi manhaja, sukan tambaye ni “Credit Card Number,” idan nasa sai abin yaki yi; alhali katin ATM di na nau’in Mastercard ne.  Yaya zan yi ne?  – Nafiu Sabo Katata, Azare, Bauchi State
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Nafi’u. Ina godiya da addu’o’inku, Allah karba, ya kuma saka muku da alheri baki daya.   Dangane da batun sayen hajoji kamar su masarrafai ko manhajoji ta cibiyar cinikayya na Google Store ko Play Store misali, dole ne ya zama ka taskance bayanan katinka a wayar, ta hanyar manhajar da kake amfani da ita wajen kaiwa ga wadannan manhajoji.  Ma’ana, idan ka fara amfani da waya mai dauke da Android, kafin ka shiga Play Store sai ka sa adireshin Imel dinka, da kalmar shiga (Password).  Daga nan za a riskar da kai zuwa inda manhajoji suke.  Akwai wata ‘yar karamar manhaja  mai suna Google Wallet da ke dauke cikin tsarin Android.  Da ita za ka yi amfani wajen shigar da sunanka, da adireshinka, da kuma bayanan da suka shafi katinka.  
A duk sa’adda ka tashi sayen wata haja, nan take za a riskar da kamfanin da zai sayar maka da hajar zuwa wannan lalita ta Google, wato Google Wallet, don ya dauki bayanan da suka shafi katinka kafin a aiwatar da cinikin.  Idan kuma baka taskance wadannan bayanai a Google Wallet ba, to shi ne dalilin da ke sa idan ka tashi sayen haja, sai a bukaci ka sake sa kalmomin sirrinka (Password) na Imel, sannan a bijiro maka da dan karamin fam da ake son ka sa lambar katinka na ATM, da kuma lambobi guda uku ko shida da ke bayan katin.  Wadannan lambobi su ne ake son ka shigar da su a inda aka rubuta “CSb” misali.
Bayan ka shigar da bayanan katinka da sunanka, nan take za a tuntubi kamfanin da ya bayar da katin (misali, Mastercard, ko bisa).  Idan kamfanin ya tantanceka ba matsala, sai kuma kamfanin da kake son sayen hajarsa ya sako maka hajar, a daidai lokacin da kuma ake cire farashin hajar da ka saya. Kusan lokaci guda za ka samu hajar da kuma sakon sanarwa daga banki cewa an cire Dala kaza daga taskarka.  Domin cinikayya a wannan yanayi yana faruwa ne cikin Dalar Amurka ba nairan Najeriya ba.
A wasu lokuta kuma kana iya cike wadannan bayanai gaba daya, amma a ce maka cinikayya ba za ta yiwu ba.  Manyan dalilai guda biyu ne ko uku.  Na farko, watakila babu isassun kudi a cikin taskarka da za ta iya sayen hajar.  Idan akwai isasshen kudi da zai iya sayen hajar, amma cinikayya ya ki yiwuwa, sai dalili ba biyu.  Shi ne, ta yiwu kamfanin da ya buga katinka ba shi daga cikin kamfanonin da ake karbar katukansu wajen cinikayya a wannan mahalli.  Idan yana daga cikin kamfanonin da ake karbar katukansu, amma kuma cinikayya ba ta yiwu ba, to, ta yiwu kamfanin da zai sayar maka da hajar ba ya karbar kwastomomi daga Najeriya.  Domin ba dukkan masu sayar da hajoji ta Intanet ‘yan kasuwa ke yarda da masu sayen haja daga Najeriya ba, saboda dalilan tsaro, kamar yadda na san ka sani ba sai na yi wani karin bayani ba.  Domin bai wuce shekaru biyar da suka gabata ba da aka fara yarda da ‘yan Najeriya a yanar gizo wajen harkar kasuwanci.
Assalamu alaikum, Allahya gafarta wa Malam. Inada tambaya! Tayaya kamfanin sadarwa wato (Telecom network) suke gane kalar wayar da mutum yake amfani da ita, kuma har suke turo wa mutum sakon Settings na Intanet?  –  Uzairu Abdullahi
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Uzairu. Ina godiya matukka da addu’a. Allah saka da alheri.  Da farko dai, sabanin yadda ka fada, kamfanonin waya ba su iya gane kala ko launin wayarka, sai dai nau’in wayar.  Wannan kuma na faruwa ne daga irin na’urar da suke amfani da ita wacce ke aikin sadar da mutane ta hanyar lambobinsu, da kuma tsarin da na’urar ke amfani da shi mai suna USSD, wajen aiwatar da sadarwa tsakanin kamfanin waya da mai waya.  Misali, idan ka bukaci  sanin balas dinka, da zarar ka latsa *556# a MTN misali, nan take wannan na’ura za ta cillo maka yawan kudin da ya rage a layinka.  Haka idan ka bukaci  wani abu daban ta hanyar shigar da wasu lambobi da kamfanin waya ya bayar, wannan na’ura ce ke da alhakin maido maka da jawabi.
Ita wannan na’urar, an gina ta ne ta yadda duk wata wayar salula idan tana dauke da katin wayar kamfanin waya, nan take wannan na’ura za su fahimci juna tsakaninta da wayar, kai mai rike da waya ba za ka sani ba.  Sannan kuma tana iya taskance bigiren da kake dauke da wayar, wanda ke dauke da layin kamfanin wayar.  Shi yasa, da zarar ka tura lambobin bukatar tsarin mu’amala da Intanet, wato Configuration Settings, nan take sai wannan na’ura ta yi amfani da bayanin nau’in wayarka, ta zabo wanda ya dace da ita, ta cillo mata.  Idan wayar da kake dauke da ita ba ta daga cikin jerin wayoyin da ke iya karbar sako daga kamfanin waya, nan take wannan na’ura za ta sanar da kai.  Amma a wannan karon, maimakon ta cillo maka tsarin, sai dai ta sanar da kai cewa: “Wannan waya ba zai iya karbar sakon tsarin mu’amala da fasahar Intanet ba.”  Da fatan dai ka gamsu.
Assalamu alaikum Malam, ni shawara ce nake so in baka wadda za ta taimaka wa alummar Arewacin Najeriya. Malam, ya kamata ka bude makarantar koyon kwamfuta.  Domin ci gaban mu matasa na wannan yanki. – Umar Musa Barde
Wa alaikumus salam, Malam Umar wannan shawara ce mai kyau, kuma duk da cewa ina da wannan kudiri, amma a halin yanzu ba abu ba ne mai yiwuwa a gare ni.  Akwai mai gidana mai suna Malam Salisu Webmaster da ke garin Kaduna.  Ya bude makaranta na musamman wacce ke tallafa wa matasa maza da mata wajen tabbatar da wannan kudiri.  Don haka, duk wanda ke da sha’awa yana iya tuntubarsa; ko dai ta shafin Facebook ko kuma ta inda makarantar take. Allah sa mu dace, amin.
Assalamu alaikum, ina gyaran kwamfuta ne, amma na kasa shigaSet Up naToshiba.Na yi amfani da F2 da F12 ammaina! Kuma ba laifinallon shigar da bayanai ba ne.Don Allah a taimaka  –  Musa KB
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Musa KB. Sabanin yadda ka ce ka yi amfani da maballan “F2” da “F12” amma abin ya ki, galibin kwamfutocin Toshiba ana iya shiga BIOS Setup dinsu ne ta hanyar matsa maballin “F1” ko “esc” a daidai lokacin da ta fara kunnuwa.  Idan kuma nau’in “Toshiba Ekuium” ce sai ka matsa maballin “F12.”  Wadannan shahararrun maballan da ake amfani dasu wajen shiga BIOS Setup na kwamfuta nau’in Toshiba ke nan.  Bayan haka, yana da kyau ka san cewa, galibin kamfanonin kera kwamfutoci a yanzu sukan canza tsare-tsaren da suke yi wa kwamfutoci daga wadanda aka sani a baya zuwa wasu daban.  Don haka, idan sabuwa ce kana iya duba kundin da ta zo da shi, wato System Manual, don ganin yadda ake shiga.  Idan kuma tsohuwa ce ko mai matsakaicin shekaru, sai ka yi amfani da maballan da na zayyana a sama. Allah sa a dace, amin.  
Assalamu alaikum, don Allah malami na bukatar a yi mini cikakken bayani game da yadda ake“Boost” din “Post” a cikin Shafi (Facebook Page) din da mutun ya hada na kansa.  Domin idan na yi post mutane da yawa ba su gani.  Sai a ce mini: “Boost this post,”idan na shiga sai a ce mini in sa lambar kati bisa da dai sauransu. – Abdullahi Garba Shalos: [email protected]
Wa alaikumus salam Malam Abdullahi, barka da warhaka. Kalmar “Boost Post” na ishara ne ga wani tsari da hukumar Dandalin Facebook ke amfani da shi wajen “habaka” sakonnin da masu shafin facebook (Facebook Page) ke rubutawa a shafinsu, don baiwa mutane da dama ganin sakon, da karanta shi ko ba shi mahimmanci.  Wannan tsari na habaka sakonni ba kyauta suke yinsa ba.  Sai ka biyu kudi, shi yasa kake ganin bayani kan bisa Card da dai sauransu.
A ka’ida, idan ka bude shafi a Facebook, kana iya gayyatar dukkan abokanka don su “So” shafin, wato “Like” ke nan.  Iya yawan wadanda suka so shafin iya yawan wadanda za su rika ganin sakonka idan ka rubuta.  Idan mutane miliyan daya ne suka so shafinka, to, wannan na nuna cewa da zarar ka yi rubutu ka cilla a shafin, akwai tabbacin mutum miliyan daya za su ga sakon ke nan.  Ba su kadai ba, hatta abokansu suna iya ganin abin da su suka so, wanda kuma hakan ma wani tsari ne da ke bai wa shafinka damar samun karin “Masoya” a araha babu ko kwabonka.  To amma hakan ba abu ba ne mai sauki a aikace.  Kafin mutane masu dimbin yawa su so shafinka cikin dan kankanen lokaci yana bukatar jajircewa a bangarenka, wanda kuma ba kowa ke da wannan hikima, da basira, da fasahar nemo mutane su so shafinsa ba.  
Wannan tasa hukumar Facebook suka bullo da tsarin “Boost Post.”  Kare da kudinsa, in ji Hausawa, ya sha rubutu.  Idan kana son a rika habaka maka sakonninka cikin sauki ka biya kudi, sai ka matsa wannan alama ta “Boost Post,”  nan take za a kaika wani shafi, inda za ka zabi yawan mutane, da farashin da kake son a aiwatar maka da aikin.  Kudin ana biyansu ne a tsarin Dalar Amurka ba Nairar Najeriya ba.  Don haka, idan ka zabi iya lokaci (daga kwana daya ne zuwa shekara idan kana so), sai a kai ka inda za ka shigar da lambar katin ATM dinka, da nau’insa – bISA ne ko MASTERCARD.  Sannan a can kasa za ka zabi ko kana son idan lokacin da ka diba ya kare, a sake yanko wani lokaci irin sa ba tare da sai ka bukata ba (wato “automatic resubscription” ke nan).  Da zarar ka gama cikewa, nan take za su zare kimar kudin, bankinka zai turo maka sako kan adadin kudin da wannan hidima ya hadiye.  Sauran bayani kuma sai ka saurare su.  Su suka san yadda za su rika tallata maka shafinka, kana samun “masoya” cikin sauki, har zuwa kadadar lokacin da ka diba.  Da fatan ka gamsu da wannan dan takaitaccen bayani.