Amsoshin tambayoyi: Me ya sa ba a iya gane rubutun likitoci?

Tambaya nake game da rubutunku na likitoci. Idan wani likita ya rubuta magani ko kwararren mai magani na pharmacy ba zai iya karantawa ba. Shin a wurin koyarwar ba a karantar da rubutu mai kyau ne? Amsa: Eh, ba a koyar da rubutu mai kyau a tsarin karatun likitanci, domin rubutu mai kyau tun a […]

Amsoshin tambayoyi: Me ya sa ba a iya gane rubutun likitoci?

Tambaya nake game da rubutunku na likitoci. Idan wani likita ya rubuta magani ko kwararren mai magani na pharmacy ba zai iya karantawa ba. Shin a wurin koyarwar ba a karantar da rubutu mai kyau ne?

Amsa: Eh, ba a koyar da rubutu mai kyau a tsarin karatun likitanci, domin rubutu mai kyau tun a firamare ya kamata a ce an koyar da shi a irin littafin nan mai layin ja da shudi. Mu a makarantar likita ma sai dai a rika yi maka bayani a wurin lacca da sauri ana cewa kuma ka yi sauri ka rubuta.

To a wurin irin wannan rubutun na aji ne fa za ka ga rubutu iri-iri. Har kirkiro rubutu yankakke ake yi. Shekara da shekaru idan ana irin wannan sai hannu ya koma haka, rubutu ya zama watsattsale.

To amma a wurin darasin magunguna ana jan hankali sosai wajen tabbatar da an rubuta magani yadda ya dace, wato sunansa ya fito baro-baro. Makinsa na karfi ya fito kuru-kuru da wa’adinsa duka dole su bayyana a fili.

To amma duk da haka da gaske ne za ka ga wasu takardun magungunan ko wanda ya rubuta su idan aka mayar masa sai ya yi da gaske kafin ya sake karantawa. To ka ga kuwa ina amfani.

Hanyar da ake bi a wannan zamani a magance wannan matsala a yanzu ita ce ta rubutu a na’urar kwamfuta a buga sunan maganin da na’urar dab’i ta printer. Wato kwamfuta ce a dakin likitan idan ya gama duba marar lafiya zai ba shi magani sai ya rubuta a kwamfuta a tura wa dakin magani kai-tsaye, idan babu maganin a can dakin maganin, za a iya buga takardar a je waje a nemo.

Duk kasashen da suka ci gaba, kai har ma asibitocin da suka ci gaba a nan kasar,  yanzu za ka ga takardar magani rubutun kwamfuta ne ba na hannu ba, domin kada a kasa gane rubutun a je a yi kuskuren ba wa marar lafiya maganin da bai dace da shi ba.

Idan na zauna a kan benci ko wata kujera mai tsayi inda kafata za ta rika lilo sai kafata ta hagu ta fara ciwo da zafi. Ko mene ne haka?

Daga Fatima A.S, Maiduguri

Amsa: Watakila kina danne jijiyoyi masu kawo jini kafafuwan ne shi ya sa take zafi. A wasu lokuta ma ba zafi za ki ji ba, za ki ji kafar ta yi tsami ne.

Wai shin kona almakashi da masu yankan farce suke yi yana da wani alfanu ne?

Daga Abba Hassan Kano

Amsa: Eh mana, ai yana taimakawa ne wajen kashe kwayoyin cuta da ke zaune a kan almakashin wadanda aka kwasa daga wani, don kada a sa wa wani. Fadakarwar da ake ta yi a irin wadannan kafafen watsa labarai na tsawon shekaru ne ya sa aka samu karbuwar al’adar. Kafin a rika konawar a shekarun baya Allah kadai Ya san ire-iren cututtukan da aka yada a tsakanin al’umma ta almakashin yankan farce da sauran ire-irensu kamar askar wanzamai da rezar ungozoma da sauransu.

Idan na sha ruwa da safe bayan na karya kumallo sai jikina ya mutu, sai na yi dan barci sa’annan jikina ke min dadi. Ina mafita?

Daga Usman 440 Malumfashi

Amsa: Ba wani abu, watakila kana shan tsimi ne mai dan bugarwa wato kayan da aka yi da jikakken gero, sukan sa haka, tunda idan aka jika gero kwana guda zuwa kwanaki a matsayin kamu, aka sha a kunu ko koko ko a fura zai iya sa barci. Amma akasin haka kayan karyawa irin su shayi da kofi sai dai su sa wartsakarwa.

Cikin bakina ne ke yawan tsagewa har kuraje su fito a wurin. Shin me yake kawo wannan?

Daga Haruna Hukuma, Hadeja

Amsa: Watakila ba ka samun cimaka mai cike da sinadaran bitaman sosai, domin karancin bitaman irin su bitaman na rukunin B da C sukan sa haka. Don haka sai ka dage da cin kayan itatuwa da ganyayyaki a kullum, nau’ukan yau daban na gobe daban, za ka ga bambanci.

Ko da gaske yawan cin namijin goro yana haddasa ciwon hanta?

Daga Sulaiman Abuja da Babangida Baba, Gombe

Amsa: Eh, tunda kun ce yawan ci, watakila zai iya yi wa hanta illa, tunda daci ne. Idan daci ya yi yawa kuwa hanta ita ce za ta galabaita, tunda aikinta ne tace daci da duk wata guba daga abinci.

Koyaushe ina dafa citta da kanamfari da tafarnuwa in sha. Ko hakan na da wata illa?

Daga Maman Khadija, Gusau

Amsa: A’a ba za a ce akwai illa kai-tsaye ba, amma da kika ce koyaushe shi ne matsalar, ba a san ko sau nawa a rana ko a mako kike sha ba, Yawaita abu shi ne ba a so a cimaka, a dauki wani nau’in abinci a yi ta ci kamar shi kadai ne a duniya.

Ko shan ruwan zobo na iya kara jini?

Daga Isa Usman, Tumu

Amsa: A’a kawai don ka gan shi ja kamar jini? Babu sinadarai masu karin jini a cikin zobo sosai, wato sinadarai irin su iron, sai dai a jikin korayen ganyayyakin da muke ci, ka ji wani iko na Allah.

Me ke sa wa kafar mutum ta yi kafar kaza, kafar mutum ta rike?

Daga Aliyu Muhammad, Yobe

Amsa: Shi ma karancin wani sinadari ne na calcium wanda ake samu a kayan abinci kamar madara da nono da cukwi da saransu. Zai iya faruwa a kafa ko a hannu.

Me ya sa idan na ci abinci can an jima kuma sai in ji kamar ban ci ba? Me ke kawo haka?

Daga G.B.A

Amsa: Mu da ma a kimiyance idan aka ci abinci mai sinadarin carbohydrate wato mai kara kuzari, cikin awa daya da rabi wato minti 90 komai ya narke, amma idan aka hada da mai gina jiki wato protein sai ka kai awa uku zuwa hudu ba ka ji yunwa ba. To na farko ke nan.

A da can a yarinta kuma idan mun ce muna saurin jin yunwa bayan mun ci abinci sai a ce ko macijin ciki ke cinye mana abincin. To wannan ma akwai kanshin gaskiya a ciki. Yana da kyau kowa ya rika shan maganin wanke macijin ciki kamar sau daya a shekara.

Ko gaskiya ne za a iya gadon mutuwa da wuri kuwa?

Daga A.S Idris, Ikara

Amsa: A’a ba wani abu ko wasu kwayoyin halittu na DNA da aka sani da za su iya sa a gaji mutuwa da wuri. Za dai a iya gadon ciwo mai kisa da wuri, kamar ciwon kiba da na suga da na hawan jini da na daji da sauransu. To amma a wadannan din ma ba wani tabbas, tunda da dama wadanda ba su da wadannan cututtukan wadanda ake gani lafiyayyu ne sukan mutu haka kawai ta wasu hanyoyin daban.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno