Amsoshin tambayoyi: Mene ne amfanin hamma ga lafiya?

Ina so ne a yi mini bayani a kan hamma, amfaninta ga jikin dan Adam, ko rashinta kan iya zama matsala ga jiki. Kuma me ya sa idan mutum ya yi hamma za ta yiwu na kusa da shi ya kamu? Amsa: Hamma na daya daga cikin halayyar dan Adam da ba mu da wani […]

Amsoshin tambayoyi: Mene ne amfanin hamma ga lafiya?

Ina so ne a yi mini bayani a kan hamma, amfaninta ga jikin dan Adam, ko rashinta kan iya zama matsala ga jiki. Kuma me ya sa idan mutum ya yi hamma za ta yiwu na kusa da shi ya kamu?

Amsa: Hamma na daya daga cikin halayyar dan Adam da ba mu da wani katabus ko iko a kai. Wato irin wadannan halaye kwakwalwa ce kan ba da umarnin yin su ko mun shirya ko ba mu shirya ba, ko mun sani, ko ba mu sani ba. Sauran halayyar dan Adam irin wadannan da ba mu da iko a kai wadanda ake kira inboluntary actions sun hada da tari da atishawa da gyatsa da kyafta idanu da sauransu. Jarirai sun fi manya yawan irin wadannan halaye domin su ko da halayyar rike wa mutum hannu a yayin da aka taba su, kwakwalwa ce ke sa wa, ba tare da sun sani ba.

Hamma na daya daga cikin halayyar da aka dade ana karantawa a kimiyyance amma ba a gama karatunta ba har yanzu. Misali har yanzu ba a san cikakken dalilin da ya sa ake hamma ba, duk da dai ana tunanin tana iya nuni da gajiya ko yunwa. Wadansu masana kuma suka ce a’a wartsakarwa take sa wa, da sauran dalilai da dama. Kuma har ila yau ba a tabbatar da abin da yakan sa idan wani ya yi hamma, wani na kusa kan kamu ba, amma dai an binciko cewa kowane dan Adam yana yi, har dan jariri na cikin ciki, ba kamar yadda ka tambaya ba wai ko akwai wadanda ba sa yi. Kai ba dan Adam ba, har wasu dabbobi ma kamar zaki da damisa da biri da kyanwa da doki duk suna yi.

Babban abin da aka fi alakantawa da hamma shi ne cewa idan aka yi ta, ana tunanin dole akwai dalili, ko dai na yunwa, ko na gajiya, ko wani matsi, kuma hakan na nufin kwakwalwa na son a samu a huta idan an gaji ko a ci abinci idan ana jin yunwa. Domin an lura idan aka fara hamma saboda wani dalili, da an yi maganin dalilin hammar kan tsaya. Misali idan yunwa ake ji, idan aka ci abinci hamma na tsayawa, idan aka ji gajiya ko barci, da an yi barcin an huta an tashi za a daina hammar.

Babu laifi mutum ya yi hamma biyu uku zuwa ma hudu ko biyar jefi-jefi a rana, amma da zarar an ga hamma ta fara wuce misali, to da alamun babu lafiya, domin akwai cututtukan kwakwalwa masu sa yawan hamma, misalansu su ne kamar tsiro a kwakwalwa ko farfadiya ko bugun jini a kwakwalwa.

Shekaruna sun haura 60, to sai kaina ke yawan bugawa na je asibitin Kauran Namoda amma ba wani canji

Daga Abubakar Garba Kaura

Amsa: Ai ya kamata da ka yi bayanin abubuwan da aka maka a can da wadanda ba a yi maka ba, an yi maka gwaje-gwaje da aune-aune kafin a ba ka magani ko kuwa, ko ba a ba ka ba, an yi maka bayanin matsalarka, ko kuwa ba a yi maka ba, duk wadannan ba ka yi bayani ba, su ne za su sa a gane ko asibitin gaske ne ko na bogi. Idan ba ka gamsu ba za ka iya zuwa ka nemi wani na gaba da shi.

Me ke sa a rika yawan ganin jiri idan an dade a tsaye na tsawon lokaci?

Daga Damagari S.

Amsa: Eh, dadewa a tsaye za ta iya kawo jiri mana. Jin jiri yayin mikewa daga zama ko kwanciya shi ne ba lafiya ba, wato ita ce matsala.

Me ke kawo kuraje a baki idan mutum ya yi zazzabi?

Daga Danlami Chahe

Amsa: Wannan ita ake kira huciyar zazzabi. Yawanci karancin sinadarin bitaman ne ke nunawa a baki ko gefen baki bayan an yi ’yar mashasshara. Wani lokaci zazzabin kansa kan iya sa haka, a wasu lokuta kuma magungunan kashe kwayoyin da suka sa zazzabin ne ke haifar da haka.

Shekaruna ba su fi 19 ba amma ina yawan yin fitsari. A rana sai in yi kamar sau hudu zuwa biyar, haka ma da dare. Ko hakan matsala ce?

Daga Harisu, Dutse da Bilkisu Sulaiman

Amsa: Eh, matsala ce da ya kamata ku samu lokaci a je asibiti a binciki dalili.

Ko gaskiya ne akasarin asibitocinmu ba sa tantance jini mai dauke da ciwon kanjamau kafin su sa wa mutane?

Daga Aminu Sulaiman

Amsa: A’a karya ce, domin akasarin asibitocin da na sani suna tantance jini daga cututtuka da dama har da kanjamau kafin su ba wa wani. Irin wannan sai dai idan a asibitocin bogi ne na cikin layi, wadanda suna nan da yawa.

Ni kuma mahadin hannuna ne ke yawan gocewa idan na motsa shi da karfi. Misali idan na harba hannu kamar zan kai naushi. Na yi magani har na gaji. Ko shin akwai maganin wannan?

Daga Hassan Usman Abuja

Amsa: Eh, akwai mutane wadanda sukan samu yawan gocewar kasusuwan gwiwar hannu ko na kafa idan suka yi wani motsi mai karfi ko idan suka bugu a wurin. Haka nan akan haifi irin wadannan mutane. Ka ce ka yi magani ka gaji, amma ba ka bayyana wane irin magani ka yi ba. Akan iya gyarawa a asibitin kashi amma dai watakila akwai ’yar tsada kadan.

Shin da gaske ne shan ruwan rijiya yana iya haifar da ciwo?

Daga A’isha Bauchi

Amsa: Eh, da gaske ne in dai rijiyar budaddiya ce kuma marar zurfi. Rijiyar burtsatse wato mai zurfi kuma rufaffiya mai kan tuka-tuka din nan na karfe ita ce za a iya cewa za a iya shan ruwanta lami-lafiya, ita ma idan ba ta yi kusa da salga ko sokawe ba.

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50