Amsoshin tambayoyin daban-daban: Ko za mu iya cin abincin da dabba ta ci ko ta sha?
Shin ko za mu iya cin abincin da dabba ta ci ko ta lasa? Daga Ashiru M, Katsina Amsa: Amsar tambayar kai-tsaye ita ce a’a. Domin kuwa dabbobi za su iya kasancewa suna dauke da kwayoyin cuta a bakinsu ko miyansu wadanda za su iya mana illa. Kwayoyin cuta irin wadanda muka sani da […]
Shin ko za mu iya cin abincin da dabba ta ci ko ta lasa?
Daga Ashiru M, Katsina
Amsa: Amsar tambayar kai-tsaye ita ce a’a. Domin kuwa dabbobi za su iya kasancewa suna dauke da kwayoyin cuta a bakinsu ko miyansu wadanda za su iya mana illa. Kwayoyin cuta irin wadanda muka sani da wadanda ba mu sani ba akwai su da dama a baki da miyan dabbobi, kuma duk yawancinsu za su iya mana illa a jiki, duk da kamar ana ganin dabbar lafiyayya ce. Wato kamar a jikinmu ne akwai kwayoyin cuta da ba sa mana illa, to haka ma adabbobi akwai kwayoyin cuta da ba sa yi musu illa, amma mu da sun taba mu sai ciwo.
Manyan misalan irin wadannan kwayoyin cututtuka su ne na kwayar cutar ciwon haukar kare wadda akan dauka idan kare ko wata dabba mai ciwon ta ciji mutum. To da yake kwayar cutar a miyau take, a wasu lokutan masana sun tabbatar ko a abincin da kare ko wata dabbar daji mai dauke da kwayar ta lasa, za a iya dauka.
To ban da wannan akwai kwayoyin cuta iri-iri da su watakila ba sa yi wa dabbar komai, amma za su iya mana illa. Ko a kwanan nan ana samun labarai na wadanda karen gida a Amurka ya lashe musu hannu ko kafa, ya sa musu wata bakuwar kwayar cuta, hannayen da sai dai yanke su aka yi. Kai wadansu ma har mutuwa suka yi a Amurkar sanadiyar lashe-lashen da suke bari kare ke musu.
Kuma ba kare ba, wannan har kyanwa da sauran dabbobi ba a so a ci abinci idan sun taba. Musulunci ma ya sanar da mu wannan tuni, abin da su sai yanzu mutanen Yamma wadansunsu suka sani; aka ce kwanon abinci idan kare ya lasa to a wanke shi sau bakwai, idan kuma tufa ce wanki daya ya yi ko? To ai duk saboda irin wadannan kwayoyin cutar ne.
An ce mu mutane ba mu cika ci ba saboda ba mu da tumbi kamar na dabba. Shin ina gaskiyar haka?
Daga Rabe Bera, Bagiwa
Amsa: Eh, to kusan haka ne. Mu mutane tumbinmu daya ne, amma dabbobinmu kamar tumaki da shanu su tumbinsu hudu ne, wanda ya hada da na farko babba wanda ya fi na dan Adam girma. A nan suke tara duk abin da suka ci, sai ya jiku, ya tsimu, sai su koma gefe bayan sun gama kiwo kuma su rika dawo da shi baki suna sake tauna suna hadiyewa, wanda shi kuma zai wuce tumbi na uku kai-tsaye, kafin ya isa na hudu, wanda shi ne kamar ciki, wato kamar tumbi irin namu, inda daga nan sai dai a tsotse abinci a karamin hanji
Ni kuma cikina ne yake yawan ciwo, inda sai in yi kwanaki ina yi. Na je asibiti an ba ni magani bai daina ba. Me ke kawo haka?
Daga Haruna U. Hadeja
Amsa: Abubuwa da dama, tun daga olsa da kwayoyin cuta kamar typhoid da matsalar borin hanji da sauransu za su iya kawo haka. A bahasinka sauranka abu daya, wanda shi ne bincike. Ba ka nuna alamar an bincike ka ta hanyar aune-aune da gwaje-gwaje ba. Idan ka samu asibiti mai kyau inda ake wadannan, ina ganin za a gano ko mene ne a magance shi.
Ni ma hakarkarina ne gefen dama ke mini ciwo sai ya rika suka, idan na yi mika sai in ji ya yi sauki. Ya fi yi da dare. Ko me ke sa haka?
Daga Hamza A. Gombe
Amsa: Kai ma abubuwa da dama tun daga sanyin kashi, yawan sinadarin gishirin uric acid, ko wata tsohuwar buguwa duk za su iya sa wannan. Ka samu ka je a binciki dalili.
Yatsun kafata ce suke yawan mini alamun kafar kaza. Shin wannan matsala ce?
Daga Dantanin Yelwa
Amsa: Eh, matsala ce, alama ce ta cewa akwai wani sinadari ko ma’adini wanda ya yi karanci a jikinka. Wani lokaci a ’yan yatsun hannu, wasu lokuta a na kafa. Ka samu ka je a auna a gani. Idan ka yi wasa sinadarin ya yi kasa sosai zai iya sa suma ko wani abu mai kama da haka.
Irin rubutun nan da ake gani akan wasu magunguna kamar kafso, shin tawada ce ko me, ba su da illa?
Daga Shehu Karami
Amsa: A’a ba wata illa. Yawanci da ruwan inki, wanda ba ya da illa ga ciki ake yi, wato edible ink. Irin dai wanda wadansu ke zane da shi a kan abinci kamar su kek. Ka gaskata kawai duk abin da za a yi amfani da shi a yi rubutu a kan magani mai tsabta ne ba zai yi illa ba.
Ni iyayena da ’yan uwana ba gajeru ba ne, amma ni gajere ne. Ko akwai wani magani da zan sha?
Daga Muhammad I. Katsina
Amsa: Ashe dai ba ka karanta bayaninmu a kan bambancin halitta ba na wancan mako. Ai wannan shi ne bambancin halittar, wadansu a yi su dogaye, wadansu matsakaita, wadansu gajeru. Inda muka ce wadanci (dwarfism), ba gajarta ba ita ce matsala ko ciwo. Idan kai wada ne to tabbas akwai magunguna da akan iya ba wada, amma fa tun suna yara, ta yadda za su dan yi tsayi. Idan ka tuna ai da dan kwallon kafa na kasar Ajentina Messi wada ne, amma tun yana da kuruciyarsa aka rika ba shi magunguna da allurai har ya kara girma. Kuma kai a yanzu idan ka gan shi ba za ka ce masa dogo ko matsakaici ba, domin har yanzu kamar gajere yake duk da ya sha magunguna, amma kuma ka ga yanzu ba wada ba ne.
Akwai wata ’yar uwata hakoranta na gaba guda biyu rabinsu akwai cin-zuma. Ko akwai yadda za a yi a wanke?
Daga M.B Rafin Kuza
Amsa: Eh, wannan sai an tuntubi likitan hakori ya gani, shi ne zai tantance ko mai goguwa ne ko kuma a’a