Amsoshin tambayoyin daban-daban: Shawarwari ga masu sayar da kifi
Ni sana’ata sayar da danyen kifi wato ice-fish. Wace hanya zan bi domin kare lafiyata daga matsalolin wannan sana’a? Daga Aminu Maikifi Malumfashi Amsa: Ka yi tambaya mai ma’ana Malam Aminu. Domin sau da yawa masu sana’ar kifi sukan samu matsalolin kiwon lafiya dalilin wannan sana’a. Da yake yawancinku ba ku ne masuntan kifin ba, […]
Ni sana’ata sayar da danyen kifi wato ice-fish. Wace hanya zan bi domin kare lafiyata daga matsalolin wannan sana’a?
Daga Aminu Maikifi Malumfashi
Amsa: Ka yi tambaya mai ma’ana Malam Aminu. Domin sau da yawa masu sana’ar kifi sukan samu matsalolin kiwon lafiya dalilin wannan sana’a. Da yake yawancinku ba ku ne masuntan kifin ba, za mu wuce kai-tsaye ga ku masu dillancin kifin. (Domin duba shawarwari ga su masuntan, duba rubutunmu a kan shawarwari ga masu sana’o’in cikin ruwa).
Da farko ya kamata a ce hukumomi sun samar muku kasuwa taku ta kanku, domin yawanci inda ake sayar da danyen kifi za ka ga bakin titi ne ba a cikin kasuwar kifi ba, ko a kasuwar kayan miya, wato ko ma a cikin kasuwa ne, za ka ga ba taku ba ce ku kadai. Dalilin neman kasuwa taku ta kanku kuwa shi ne a irin wannan kasuwa taku ta kanku ne za a samar muku wurin ajiyar kifinku naku na kanku, wato gidan sanyi, inda ko kifi ya yi mako babu abin da zai yi, sabanin irin kankarar da za ku je ku sawo ku rika fasawa kuna dorawa a kan kifi don kada ya lalace. Ban da wannan, samun kasuwa taku ta kanku zai taimaka muku wajen samar da rumfuna don kada a bar kifi rana na dukansa. Haka nan zai samar muku da wajen ajiyar kayan aiki da na sa wa na musamman da wurin wanka da zagawa naku na kanku domin tsabtar jikinku. Kuna ma iya haduwa da masu gashi ko soyawa ko bandashewa da busarwa, ta zama dai kasuwar kifi cikakkiya. Za ku iya neman wannan kasuwa ta hanyar kungiya ko kuma idan ba ku da kungiya, ta hanyar hadin kan abokan sana’a, inda za ku je ku nema wajen hukumomin karamar hukuma ko wakilan da kuka tura majalisu. Ba wai dole sai babbar kasuwa ba, dan gini mai dauke da wuraren da aka lissafa zai wadatar.
Abu na gaba game da hanyoyin kare kai daga matsalolin wannan sana’a shi ne tsabta. Duk yadda aka ce kai mai sana’a mai tsabta ne to kusan ka samu kariya daga cututtuka a wajen sana’arka. Tsabta ta hada da tsabtar tufafi da ta jiki da ta wurin sana’a.
-Tsabtar tufafi takan kunshi saye da ware tufafi na zuwa kasuwa na musamman, wato ka samu tufafi na wurin sana’a wadanda suka bambanta da sauran tufafinka na zaman gida. A cikin wadannan tufafi dole ya kasance akwai riga da wando da apron (wata ’yar shara ta leda da ake sa wa a saman tufafi) da safar hannu (don kada sanyin kankara ya rika ratsa hannayenka) da takalmin roba da tubarau (don kada fallatsin jini ko kaya su shigar maka ido idan kana sarar kifi).
Da an tashi aiki ka cire ka rataye a shago ka yi wanka ka sa tufafin gida ka wuce gida. Idan ka yi haka ko uwargida za ka ga ta canja maka miya, domin watakila ba ta gaya maka kana kwaso karni kana dawowa da shi gida ba. Ba ku kadai ba, duk masu sana’a a wurin da ake kwaso wani kanshi marar dadi sai suna yin haka. Mu kanmu likitoci akwai lokutan da iyalan wadansunmu sukan ce suna warin asibiti (karnin jini ko izal ko datal da sauransu), idan ba su dora katuwar farar riga kan kayan gida ba.
-Tsabtar jiki kamar yadda muka ce a sama ita ce ta yawan wanka. Masu sana’ar kifi dole ne su rika wanka akalla sau biyu a rana, na fita kasuwa da na dawowa gida. Wannan yana da muhimmanci kwarai ga kiyaye lafiyar jikinka.
-Tsabtar wurin sana’a, ta hada da sharewa ko biyan wasu su rika share wurin sana’a lokacin shiga kasuwa da bayan an gama da tabbatar da wanke jini da yadin abin da aka bari a kan tebura da kuma kasa kan siminti, domin kada kuda da kyankyasai da beraye su damu kasuwar taku. Amma dabbobi irin su kyanwa kusan ba yadda kuka iya da su sai dai kawai ku ware musu daro.
A wasu lokuta nakan ga sha-zimami a cikin sukarina a leda. Ko akwai wata cutuwa da mai shan irin wannan sukari da sha-zimami ya sha?
Daga Hamza Abubakar Gombe
Amsa: Eh, za a iya samun cutuwa domin sha-zimami suna bi ta kasa su iya kwasar kwayoyin cututtuka da kafafuwansu kafin su shiga ledar sukarin taka. Kuma ba ka san daga ina suka fito ba. Don haka abin da ya fi idan ka gan su sai dai ka bar musu ka sayi wani, ko idan ba hali ka yade sama-saman da suka hau ka zubar, amma idan sun riga sun shiga can can-ciki to a hakura. Za ka iya kare shigar sha-zimami cikin sukarinka ta hanyar samun mazubi mai marufi (airtight) domin leda za su iya huda ta. Abin da za ka iya ci idan sha-zimami suka hau su ne abubuwan da za ka iya wankewa ko yanke wurin da wuka, ko barewa, kamar lemo, mangwaro ayaba da sauransu in dai sun hau lokacin suna rufe ne.
Me ke kawo kaikayin jiki bayan an yi wanka?
Daga Ja’afar Garba
Amsa: Sai an duba ka an yi maka ’yan tambayoyi za a san mene ne ke kawo maka wannan kaikayi
Ina da hakiya a ido, na je asibiti an duba an ba ni magunguna amma ba sauki, kuma sai kara girma take. Ko magunguna na warkar da ita?
Daga S. A. Daura
Amsa: Mu ma dai a likitance tiyata muka sani ana wa hakiya, ko a sa dan ruwan gilashi na lens, sai dai idan ba ta nuna ba, shi ne za a ce ka dawo bayan wasu lokuta. Amma ai akwai asibitocin ido wadanda suke gaba da naku na Daura a garuruwa makwabta inda za ka samu likitan ido sosai.
Mai ciwon suga zai iya cin walaha da dankalin Turawa ko ya sha fura da nono?
Daga Hassan S.Garin Zariya
Amsa: Ba fa hana cin abinci masu sukari aka yi ga mai ciwon suga ba, domin kusan duk abincin da mukan ci akan samu stachi wato sukari a ciki. Idan likitanka ne ya ga sukarin jininka yana kyau zai iya gaya maka abincin da za ka iya ci ko da suna da sukari sosai, amma idan sukarin naka bai da kyau ba zai bari ba.
Karin Bayani: Duk masu tambayoyi da suka jibinci ganin likita su daure su je likita ya duba su. Masu kaikayin fata su je likitan fata, masu ciwon ido su nemi likitan ido, masu yawan tunani ko fushi ko son barin kwaya su ga na kwakwalwa, haka. A nan ba za mu iya duba su ba, sai dai mu ba su shawarwari ko karin bayani kan abubuwan da likitoci suka rubuta.