Amsoshin tambayoyin ku ta imel da tes (2)
Salaamun alaikum Baban Sadik, shin me ake nufi da ‘tag’, da ‘poke da kuma ‘pending’ da ke sahen sada zumunta na Facebook? Zan so ka turo min amsa ta imel di na da ke: [email protected]. Mun gode. Sani Shuaibu, Potiskum, Yobe State Wa alaikumus salam, barka Malam Sani Master. Wadannan kalmomi suna ishara ne ga […]
Salaamun alaikum Baban Sadik, shin me ake nufi da ‘tag’, da ‘poke da kuma ‘pending’ da ke sahen sada zumunta na Facebook? Zan so ka turo min amsa ta imel di na da ke: [email protected]. Mun gode. Sani Shuaibu, Potiskum, Yobe State
Wa alaikumus salam, barka Malam Sani Master. Wadannan kalmomi suna ishara ne ga abubuwa daban-daban da suka shafi nau’unta tsari da hanyoyin sadarwa da samar da nishadi a Dandalin Facebook. Kalmar “Tag” na nufin dayan abubuwa biyu ne; na farko dai sunan wata karamar manhaja ce da ake amfani da ita wajen tarayya da wani aboki ko abokiyar kawance a dandalin facebook, cikin sakon rubutu ko hoto da mai shi ke son dorawa a shafinsa. Idan ka loda hoto ko wani sako a shafinka, bayan ka gama, a kasa akwai inda za ka latsa don shigar da sunayen Wadanda kake son su yi tarayya da kai wajen yada wannan hoto.
Abu na biyu da kalmar “Tag” ke nufi shi ne, lika sunan wani aboki ko kawa a kan hoto ko sakon rubutu da ka yi a shafinka. A nan mun dauki kalmar da ma’anar aiki ne kenan. Duk wanda ka lika sunansa ta hanyar “Tag” a sakon da ka rubuta ko hoton da ka loda, wadannan sakonni za su bayyana a shafinsa kai tsaye, kuma dukkan abokansa, ko da sun kai dubu biyar ne, za su iya ganin sakon kai tsaye. Wadanda baza su iya gani ba sai Wadanda ka toshe su daga shafinka, ko shi ya toshe su daga shafinsa, wato: “Block”, ko kuma wadanda ka killace su a kasan sakon bayan ka gama rubutawa ko lodawa. Su kam wadannan ba za su iya ganin sakon ba.
Kalma ta biyu, wato: “Poke”. Ita ma tana nufin sunan manhaja ce, sannan idan muka dauki kalmar da ma’anar aiki, tana nufin yin amfani da manhajar “Poke” dake dandalin Facebook.
Wannan manhaja daya ce daga cikin hanyoyin samar da raha a dandalin Facebook. Idan aka ce: “Sadik poke you” misali, ana nufin ya tsikareka ke nan. Manhaja ce da ake amfani da ita wajen tsikara, don jawo hankalin aboki ko wanka ake kawance da shi ko ita. Kuma da zarar ya maka nan take za a sanar da kai. Daga nan kai ma kana iya mayar da martani. Duk da cewa ba kowa ba ne ya san ma’anar wannan manhaja, wanda hakan ya sa wasu ke amfani da ita fiye da kima, amma wannan shi ne dalili da ma’ana ta asali da suka samar da wannan tsari.
Kalmar karshe, wato: “Pending” na ishara ne ga aiki ko wani abin da ba a karasa shi ba, ko ake jira wani ya aiwatar da wani abu a kan shi. Wannan ya fi shahara a zaurukan Facebook, wato Groups. A takaice dai kalmar “Pending” na nufin jira ne, ko sauraron aiwatar da wani abu kafin direwa wani wuri ko aiwatar da wani aiki. Da fatan ka gamsu.
Salamun alaikum, daga mai kaunarka. Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka amin. Don Allah ka amsa min tambayata; Mene ne “Email”, sannan ya ya ake bude Imail, kuma mene ne amfaninsa da rashin amfaninsa? Bayan haka, a cikin nau’ukan manhajar Imel Wanne ne ya fi dadin sha’ani? Wassalam.
Daga dan uwanka: Abdullahi Aliyu Alkas, Bauchi State 09030103444
Wa alaikumus salam, barka ka dai takwarana. Da fatan kana cikin koshin lafiya. Da farko dai, idan aka ce Imel ana nufin “Wasikar hanyar sadarwa ta Intanet” ce, wacce ke dauke da adireshi mai hawa biyu; da sunan mai akwatin Imel da kuma sunan kamfanin da ke dauke da manhajar Imel din. Idan aka kasa manhajar Imel dangane da hanyoyin mu’amala, sun kasu kashi biyu ne; akwai Manhajar Imel ta Intanet, wacce ake kira “Internet Email Programme” kenan. Ire-irensu su ne: Yahoo! da Gmail da Hotmail da dai sauransu. Sai nau’i na biyu wanda ake iya amfani da ita a gajeren zangon sadarwa, ko da kuwa babu Intanet a wurin. Su ma akwai su da dama. daya daga cikinsu ita ce manhajar Imel na kamfanin Microsoft mai suna: Outlook.
Amfanin Imel yana da dimbin yawa, ya danganci iya sanayyarka da manhajar. A takaice dai, ana amfani da ita wajen aiwatar da sadarwa cikin gaggawa, cikin sauki. Kana iya aika hotuna da sauti da bidiyo duk ta amfani da Imel. Sannan kana iya amfani da adireshin Imel wajen karbar sakonni. Kana iya amfani da ita wajen bude shafin Facebook, da MySpace, da Twitter da galibin wuraren nishadi a Intanet.
Daga cikin matsaloli ko kalubalen da ke tattare da mallakar Imel akwai kamuwa sakonnin bogi, da sakonnin ‘yan zamba cikin aminci (Yahoo Boys) masu amfani da wannan hanya don yaudarar mutane da karbe musu kudi.
Dangane da abin da ya shafi inganci ko nagarta tsakanin wadannan nau’uka na manhajar Imel kuwa, ya danganci dandanonka, da abin da ka saba da shi. Amma wadanda suka fi shahara dai su ne
Yahoo Mail, da Google Mail ko Gmail da kuma Hotmail ko Windows Libe Mail. Daga cikin wadannan ukun kuma manhajar Imel na Gmail ta fi shahara, musamman ganin cewa dukkan wayoyin salula na zamani masu dauke da babbar manhajar Android suna tilasta mallakar akwatin Imel na Gmail kafin fara amfani da su, musamman ganin cewa babbar manhajar Android din damar ta kamfanin Google ce, wadda kuma ita ce take mallakar manhajar Gmail din. Abin ya zama tuwo-na-mai-na ke nan.
Shawarata a nan ita ce, idan kana da wayar salula mai amfani da babbar manhajar Android ce, kana iya zabar Gmail, sabo da saukin mu’amala, da samun manhajar Imel na wayar salula mai saukin mu’amala a kan wayar salularka, don sarrafa sakonninka cikin sauki. Da fatan ka gamsu.
Allah sa a dace, amin.