Amsoshin tambayoyinku

A wannan makon za mu kawo muku wasu muhimman tambayoyi biyu da masu karatu suka aiko filin Kimiyya da kere-kere. Tambayoyin suna da nasaba da daukacin darussan da muka saba gabatarwa a wannan shafi/. Don haka muna sauraren sauran tambayoyin, ta yadda a wasu makonnin za su jero tare da bayar da amsarsu. Ta farko […]

Amsoshin tambayoyinku

A wannan makon za mu kawo muku wasu muhimman tambayoyi biyu da masu karatu suka aiko filin Kimiyya da kere-kere. Tambayoyin suna da nasaba da daukacin darussan da muka saba gabatarwa a wannan shafi/. Don haka muna sauraren sauran tambayoyin, ta yadda a wasu makonnin za su jero tare da bayar da amsarsu. Ta farko ta kunmshi yada manufa ko talllata haja a sshafukan intanet; ta biyun kuwa kan yadda za a tura sakonn ta wayar salula ko GSM. Ga yadda amsoshin tambayoyn suka askance:

Tambaya ta farko

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Yaya aiki?  Don Allah ta yaya zan iya tallata makaranta ta a Intanet, ta yadda kowa zai ganta?   Allah ya yi maka jagora.  Abba Adam Ja’en

Wa alaikumus salam, Malam Abba Ja’en barka ka dai.  Tallata makarantarka ta Intanet ba abu ba ne mai wahala idan ka bi matakan da suka kamata.  Da farko dai ya kamata ka san cewa akwai hanyoyi da dama da za ka iya amfani da su wajen yin hakan.  Wadannan hanyoyi dai sun danganci bukatunka ne, da aljihunka, da lokacinka, da kuma ra’ayinka.

Hanyar farko dai, kana iya amfani da shafukan sada zumunta, irin su Facebook da Whatsapp da kuma Twitter, ta amfani da yaren wadanda kake son su sani.  Idan da Hausa ne, ya zama galibin abokanka da ke dandalin Hausawa ne ko a kalla suna jin harshen Hausa.  Wannan hanya ba ta da wahala ko kadan; abin da kake bukata shi ne shafi na musamman, da kuma lokacin da za ka zauna don rika yada bayanan da suka shafi makarantarka.

Hanya ta biyu kana iya amfani da gidan yanar sadarwa na kanka, wato ka gina shafi na musamman a Intanet, dauke da bayanai kan abin da makarantar ta kunsa, da tsarin daukan dalibai da kuma nau’ukan darussan da ake koyarwa a makarantar.  Wannan hanya ce mai kyau.

Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da za ka iya amfani da su wajen tallata makarantarka a Intanet. Da fatan ka gamsu.

Tambaya ta biyu

Salamun alaikum Baban Sadik, bayan gaisuwa, shin, wayar GSM za a iya amfani da ita wajen tura sakon Fad?  Kuma wane layi ne a cikin layukan nan ya fi inganci wajen tura Fad?   Daga Kabiru Kurnawee Kano 

Wa alaikumus salam, Malam Kabiru.  Lallai akwai wayoyin salula da za a iya amfani da su wajen aikawa da sakon Fad.  Da farko dai, sakon Fad nau’i ne na hanyar aikawa da sakonni ta amfani da siginar rediyo dake jikin na’urorin sadarwa, musamman tarho irin ta da, wa kuma wasu daga cikin wayoyin salula na zamanin yau.   Hakan na yiwuwa ne ta hanyar dora takarda ko wasikar da ake son aikawa da ita, a kan na’urar Fad da a asali ake amfani da ita wajen aikawa da sakon, sai a shigar da lambar wayar wanda zai karbi sako, wato wanda za a aika masa ke nan, sannan a tura.  Da zarar an aika, wannan takarda za ta shiga cikin wannan na’ura sannan ta fito ta can baya, tare da sakon shaidar aika sako, wato “Acknowledgement Copy” ke nan.

A tsarin wayar salula kuma, kana iya saukar da manhajar aikawa da sakon Fada wayarka mai dauke da babbar manhajar Android ko Ios na kamfanin Apple ke nan.  Idan ka bincika, muddin akwai wanda ya dace da nau’in wayarka, nan take za ka gani, sai ka saukar.  Amma wadannan manhajoji na kyauta suna da nakasa, ma’ana bai wuce ka iya aikawa da sako sau daya ko sau biyu a lokaci daya.  Idan kana bukatar wacce za ka iya aika kowane adadin sakonni ne, sai ka sayi manhajar tukun.  

Da fatan ka gamsu da wannan gajeren bayani.