Amsoshin tambayoyinku
Assalamu alaikum, ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya sa mu amfana da bayanan da za su zo cikin sa, amin. A wannan karon ga amsoshin tambayoyinku wadanda suka danganci bayanin da muka kare kan ladubban ibadar aure:Abubuwan da suka haramta ga mai janaba:Don Allah malama ki yi mana […]
Assalamu alaikum, ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya sa mu amfana da bayanan da za su zo cikin sa, amin. A wannan karon ga amsoshin tambayoyinku wadanda suka danganci bayanin da muka kare kan ladubban ibadar aure:
Abubuwan da suka haramta ga mai janaba:
Don Allah malama ki yi mana bayanin abubuwan da suka haramta mai janaba ya aikata su, domin ni dai yana min wahala yin wanka nan take kamar yadda na ji cikin bayaninki, kuma na ji kamar an ce wai ko abinci bai halarta mutum ya ci ba har sai ya yi wanka?
-Daga Bauchi
Abubuwan da suka haramta mai janaba ya aikata su lokacin da yake cikin halin janaba sun hada da: salla da karanta wani sashe na al-kur’ani ko taba al-kur’anin da shiga masallaci da kuma duk wani aiki na ibada. Amma cin abinci ko shan abin sha ko yin barci da kara gabatar da ibadar aure ba laifi aikata su. Duk da haka dai ya fi alfanu nesa ba kusa ga ma’aurata su guji kasancewa cikin halin janaba na lokaci mai tsawo ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, yin haka yana iya zama zunubi, sannan ga hadarin da ke tattare da hakan; domin Annabinmu SAW Ya sanar da mu cewa mala’i’uku ba su shiga gidan da yake akwai kare ko hoto ko mutum-mutumi da kuma gidan da ke dauke da mutum mai janaba.
Don haka ‘yan uwa ma’aurata a daure a rika gaggauta wankan janaba don samun kwanciyar hankali da fitar da kai da iyakancewar da janaba ke sawa, don babban tashin hankali ne a ce mutum ya mutu mala’ikun rahma ba su kusanci gawarsa ba, ko a ce ba su da masauki cikin gidansa, saboda kasancewarsa cikin janaba, to in kuwa ba Mala’ikun Rahma a kusa, sai shaidanu su yi ta shagalinsu ke nan? Da fatan Allah Ya bamu ikon kiyayewa, amin.
Sai na sake wanka?
Wata sa’in takan faru gare ni bayan nayi wankan, sai in sake ganin wani maniyyin ya fito ba tare da na ji motsuwar sha’awa ba, ko hakan na nufin sai na sake wani wankan?
-A.Y Shagamu
Fahimtar malamai ta bambanta game da wannan al’amari, wani bangaren na dukkan wani fitar maniyyi, ko da sababinsa ba sha’awa ba ne, to ya wajaba a yi wanka, yayin da wasu ke ganin fitar maniyyi ta dalilin wani abin daban ba sha’awa ba ne, kamar daukar wani abu mai nauyi ko motsa jiki da sauransu, to wannan ba sai an yi wanka ba sai dai a gabatar da alwalla kawai, a dalilin haka fitowar ragowar maniyyin ibadar auren da aka riga aka yi wa wanka, bai sai an sake wankan ba tun da sababinsu daya ne da wancan na farkon da ya fito, a fahimtar wannan bangaren ke nan. Don kauce wa irin haka, sai ma’aurata su fitar da fitsari bayan gabatarwar kowane ibadar aure, domin yin hakan zai fito da duk wani sauran maniyyin da ka iya ragewa tun da kwararo daya suke bi wajen fita. Amma in har ko da an yi fitsarin kafin yin wankan, sannan bayan wankan kuma aka ga wani maniyyi ya fito, to wannan na nufin ba sauran na ibadar aure ba ne wani ne daban, don haka don samun natsuwar zuciya ya fi kyau kawai a sake wani wankan, da fatan Allah Ya sa mu dace da aikata daidai cikin ibadunmu, amin
Yawaitar kwararowar ruwan maziy
Matsalata ita ce duk lokacin da na je ga matata, ba na wuce minti goma sai in yi inzali, sannan ga yawan zubar maziyyi, duk lokacin da na yi wasa da iyalina to sai na lalata abin da nake sanye da shi, ya zan magance wannan? Ina fatan za ki yi wani rubutu a kan hakan don na san akwai irina da yawa.
-A. Tsafe
Hanyar magance matsalar fitar maniyyi da wuri mun yi bayaninta, kuma mun kara maimaitawa a wannan fili, sai dai ga wanda bai same shi ba sai ya duba a duniyar ma’aurata a shafin facebook don samun bayanin da ya gabata.
Maziyyi na fita ne lokacin da motsuwar sha’awa ya game jiki, amfaninsa shi ne, fitar da ragowar fitsari daga kwararon hanyar da maniyyi zai fita, don yana iya yin lahani ga kwayayen halitta kafin su isa ga mahaifa; sannan kuma yana yin aikin kamar irin wanda lemar ‘yammatancin mace ke yi. Abubawan da ke yawaita zubarsa sun hada da yawan yin zinar hannu kafin aure; jin tsananin lazzar sha’awa, da kuma tattara hankali da tunani gaba daya ga wannan sha’awa lokacin da aka ji ta.
Hanyoyin magance wannan matsala: sai a daure a rika raba hankali biyu zuwa ga wani abin da bai danganci da sha’awa duk lokacin da ka ji ta motso; sannan kuma aje asibiti a yi ma likita bayani, akwai magunguna da akan sha wadanda suke rage yawan fitar ruwa daga cikin jiki (antihistamine); sannan akwai magungunan rage yawan sinadarin DHT a cikin jini, wanda yake da tasiri ga tsibirin sinadaran da ke sarrafa ruwan maziyyi.
Shin dole sai tsumma?
Bayan gabatarwar ibadar aure, ko za a iya amfani da tishu (tissue paper)maimakon tsumma?
Ba lallai sai tsumma ba, ana iya amfani da duk abin da zai iya goge wajen, indai mai tsarki ne, sai yi da tsummar koyi ne da magabatan Sahabbai RA, domin Ummuna Aisha RA ta ce “mace me wayau da hankali ita ce wacce za ta tanadi tsumma, don taba mijinta ya goge jikinsa, sannan ita ma ta goge”