Amsoshin tambayoyinku (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani da zai amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko game da yanayin sha’awar mace da ta namiji. Tambaya: “Assalamu alaikum Malama Nabila. Na ga dukan […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani da zai amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko game da yanayin sha’awar mace da ta namiji.
Tambaya:
“Assalamu alaikum Malama Nabila. Na ga dukan bayananki sun karkata ne a kan cewa maza ne ke bukatuwa zuwa ga mata, to shin su mata ba su jin sha’awa ne?”
Amsa: Akwai bambanci mai girman gaske a tsakanin sha’awar uwargida da ta maigida, suna kadai suka tara. Amma yanayinsu ba daya ba ne kusan ta kowace fuska, haka kuma abin da ke motsar da su da yanayinsu a lokacin da suke faruwa akwai bambanci mai fadin gaske.
Duk lokacin da idon namiji ya ga wata siffa ko kira ta mace da ta yi masa dadi a rai, ko wata murya ko wani kamshi mai dadi, wannan dadin shi zai zaburar da wani bangare na tsibirin hypothalamus a kwakwalwa, wanda zai sa a saki sinadarin sha’awa cikin jini domin ya motso da sha’awar namiji. Amma ita ’ya mace, shaukin da namiji zai nuna mata game da ita, da halayen da namiji irin wadanda take so, sun fi motso da sha’awarta fiye da siffar halittarsa. Don haka magana mai dadi, musamman ta yabo, kirki da kyautatawa, suke motsar da sha’awar ’ya mace ba wai siffar halitta ko kwalliyar maigidanta ba.
Sha’awar Maigida mai girma ce kuma tabbatacciya ce, ana jin ta kamar yadda ake jin yunwa kuma koyaushe a kurkusa take. Amma sha’awar ’ya mace mai walkiya ce, ba ta da tabbas, in an ga ta yau gobe sai a neme ta a rasa, kuma abin da ya motso da ita yau ba lalle ba ne shi zai motso da ita gobe, sannan wata sa’ar tana da wuyar samowa, ko sai an lalubo ta kuma ta kubce.
Sha’awar da namiji kamar busashshen kara ne da aka kunna masa wuta, nan da nan zai kama gaba daya da karfinsa. Haka kuma nan da nan zai cinye ya zama toka; ta ’ya mace kuwa kamar wutar jikakken itace ne, sai an sa mata ’yan makamashi da ’yan dabaru, sannan a yi ta hurawa tana mutuwa, amma da ta yi karfi kuma sai ta dade ba ta mutu ba. ’Yan dabarun da ke kunna wutar sha’awar mace su ne kamar yadda na fada a baya: kirki da kyautatawa, jiyar da ita dadi da nuna so da kauna, sannan makamashinta shi ne wasannin soyayya kafin gabatar da ibadar aure da sauransu.
Bukatuwa da samun biyan bukatuwar sha’awa na da girman matsayi a rayuwar namiji, ta yadda rayuwa za ta yi daci da wuya sosai ga mafiya yawan maza in aka ce babu bukatuwar ko samun biyan bukatuwar sha’awa a rayuwarsu. Amma mafi yawan mata za su iya rayuwarsu ta tsawon lokaci ba tare da samun biyan bukatar sha’awarsu ba, kuma wannan bai cika damunsu ba.
Namiji ya san sha’awarsa, ya fahimce ta, ya san irin abin da ya fi so game da ita da abin ke motso masa ita, kuma kusan dukan maza yanayin dabi’un sha’awarsu iri daya ne. Amma mafi yawan mata ba su fahimci sha’awarsu ba, ba su san abin da ke motso musu da ita ba. Sannan kamar yadda kowace mace yanayin dabi’un al’adarta, daukar ciki da yanayin haihuwarta suka sha bamban da na ’yar uwarta, to haka nan yanayin dabi’un sha’awarsu suka bambanta. Kowacce tata daban da ta ’yar uwarta.
Yanayin halittar ’ya mace da yanayin sinadaran matantaka da ke kai-kawo koyaushe cikin jininta saboda al’amarin sakin kwai daga jakarsa zuwa mahaifa (obulation) da jinin haila, suna taka muhimmiyar rawa wajen rashin tabbas din sha’awarta. Wata sa’ar wasu al’amura game da halittar ’yan matancinta na iya zama cikas ga jin motsuwar bukatuwarta, haka nan al’amuran haihuwa, daukar ciki da shayarwa. Ga al’amarin al’ada duk wata da lokacin al’adar mace ya matso, takan ji karuwar sha’awarta sosai saboda wannan lokaci shi ne daidai lokacin daukar ciki.
Yanayin rashin tabbas din sha’awar ’ya mace kamar yanayin yadda mai ciki kan ji tana son wani abu yanzu, amma da an jima kadan ta ji ko sunansa ba ta son ji. Murmushi na musamman da maigida ya aike ga uwargidansa na iya zama sanadin motsuwar sha’awarta a yau, amma gobe in ya yi mata shi, sai ta ji ko son ganin wannan irin murmushin ba ta yi in dai ta fuskar sha’awa ce, wani abin kuma take so daban.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.