Amsoshin tambayoyinku (3)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa, amin. Ban hakuri… Daga cikin tambayoyin da ke iso wa wannan fili ta […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa, amin.
Ban hakuri…
Daga cikin tambayoyin da ke iso wa wannan fili ta watsaf da sakon tes da kuma fesbuk, akwai masu nuna bukatar a ba su amsa take yanke ta wadannan kafofi, muna bayar da hakuri gare ku da karin bayanin cewa ta wannnan fili a jarida ne kadai ake amsa tambayoyi. Haka kuma akwai wasu tambayoyin da babu hurumin amsa su a jarida; muna bayar da hakuri ga masu wadannan tambayoyi. Da fatan Allah Ya sama mana mafita a cikin dukan al’amuran rayuwa, amin.
Tunatarwa…
Haka kuma akwai masu aiko da tambayoyi game da kiwon lafiya da neman magani, muna tunatar da masu karatu cewa wannan fili na bayani da amsa tambayoyin da suka shafi auratayya da kyautata zamantakewa tsakanin ma’aurata, mafi alfanun abin yi shi ne zuwa asibiti wajen likita, in ba a dace ba a canja wani asibiti da wani likitan, kuma a dage da addu’a da yawan sadaka har Allah Ya sa a dace.
Wace kwaya mace ya kamata ta yi amfani da ita don kayyade iyali?
Ahmad.
Amsa: Shan kwaya daya ne kadai daga cikin hanyoyin kayyadewa da tsara iyali ko tazarar haihuwa. Akwai wasu hanyoyin daban kamar allura da kwararon roba da azalu da marufin mahaifa da sauransu. Kuma inganci da matsalolinsu sun sha bamban, sannan tasirinsu ya bambanta daga wannan mace zuwa wata, tsarin da ya haifar da matsala ga wata sai ya kasance kuma shi ne mafi sauki ga wata. Akwai malaman tsarin iyali a mafi yawan asibitoci da za su yi bayani gare ku game da dukan hanyoyin, matsala da ingancin kowane sai mace ta zabi wanda ta fi aminta da shi. Don haka sai a ziyarci bangaren tsarin haihuwa na asibiti mafi kusa da ku.
Salam Anti Nabila, me ya kamata na rika ci don jaririna ya yi kiba, na je asibiti an ce lafiyarsa lau.
Wa alaikumus salam. To tunda lafiyarsa lau, sai ki kwantar da hankalinki ki yi ta rainonsa cikin kwanciyar hankali; lafiya ita ce abin so kuma ita ake nema da kiwo a koyaushe, kiba ba dole ba ce, in ba ta cikin tsarin halittar mutum kada a tilasta a ce dole sai ya yi ta. Kamar ki haifi farin yaro ne ki ce dole sai ya koma baki, kin san abin da kamar wuya! Sannan kowane jariri lokacin kibarsa da ramarsa daban da ta wani jaririn. kila zuwa lokacin da ya fara cin abinci lokacin sai ki ga kibarsa ta ciko. Kowa da yanayin lokacin girmansa da cikarsa. Kawai ki dage da cin abinci masu dauke da kyawawan sinadiran gina jiki musamman hatsi, kayan marmari da ganyayyaki. Sannan ki rika dama kunun alkama da garin hulba don karin ruwan nono. Allah Ya sa a dace, amin.
Yarona yana ciwon kankamewar nan da wasu jarirai ke yi, mun je asibitin yara har sau uku amma bai daina ba, ga shi bai cika wata 2 ba; a taimaka mini da shawara.
– Kabir.
Ciwon kankamewa ko fisgar ruwa babban al’amari ne ga sabon jariri, abubuwa daban- daban na iya haifar da haka, mafi yawa daga cikin suna da alaka da kwakwalwa da rashin isasshen sinadaran sanya kuzari a jiki. Duniyar ma’aurata na ba ku shawara da ku nemi sanannen likitan yara wanda ya kware sosai a fanninsa (wato consultant/specialist) don ya duba shi sosai tare da gabatar da dukan gwaje-gwajen da suka dace don gano asalin abin da ke haifar masa da kankamewar. Haka kuma a dage da yawan addu’a da yawan sadaka da nufin samun waraka cikin sauri da fatan Allah Ya ba da lafiya Ya sa a dace, amin.
Don Allah a ba ni shawara ina fama da yadda za a yi maganin gaba na mata.
Zuwa asibiti shi ya fi dacewa domin kwayoyin cututtuka iri daban-daban ne ke haifar da kuraje, dole sai binciken likita ya gano yanayin kurajen sannan a san kwayar cutar da ta haifar da su da irin maganin da ya dace da ita. Don maganin da ya warke wannan cutar ba lallai ba ne ya warkar da wata ko da yanayinsu iri daya ne. Sannan a dage da tsabtar wajen da jiki duka, yin tsarki da ruwan zafi, a kiyaye sosai kada sabulu ya rika isa wajen don hakan na iya kara karfin cutar, haka kada a shafa wani mai a wajen in dai ba likita ne ya yi umarni ba. Shan magungunan Musulunci irin su zuma, zaitun, ruwan zam-zam, bakin algarif na inganta samun waraka cikin sauri da yardar Allah. Da fatan Allah Ya ba da lafiya da waraka mai amfani, amin.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.