Amsoshin tambayoyinku ta imel da tes (3)
Assalamu alaikum. Malam barka da ibada. Ina karanta wani littafi ne mai suna “The Final Dibine Religion Islam”, sai na ci karo da wadannan kalmomi: “Hydrogen,” da “Helium,” da “Tons of gas,” da kuma “Tons of Substance and Mass.” Ina neman bayani kansu. Wa alaikumus salam, barka da warhaka. Wadannan kalmomi suna ishara ne […]
Assalamu alaikum. Malam barka da ibada. Ina karanta wani littafi ne mai suna “The Final Dibine Religion Islam”, sai na ci karo da wadannan kalmomi: “Hydrogen,” da “Helium,” da “Tons of gas,” da kuma “Tons of Substance and Mass.” Ina neman bayani kansu.
Wa alaikumus salam, barka da warhaka. Wadannan kalmomi suna ishara ne ga nau’ukan sinadaran da Allah ya samar a ciki da wajen wannan duniya da muke rayuwa a cikinta. Kalmar “Hydrogen” na nufin wani nau’in iska ne mara launi, wanda ba shi da dandano wajen shaka – wato babu wani wari ko kamshi da makamantansu – kuma tana da saurin daukar wuta da zarar an gitto shi kusa da ita. Ma’ana idan aka bijiro da iskar Hidirojin kusa da wuta, nan take take kamawa. Sinadari ne mai matukar mahimmanci wajen hada abubuwan amfani daban-daban – daga amfanin rayuwa zuwa kera makamai. Akwai nau’in makamashin nukiliya da ake kerawa da wannan nau’in iska na Hidirojin (Hydrogen).
Kalmar “Helium” ita ma na ishara ne ga wani nau’in sinadarin iska, wadda ita ce mafi kankanta wajen rashin nauyi daga cikin jerin sinadaran da take da dangantaka da su. Kalmar “Tons of Gas” kuma na nufin tarin dandazon sinadarin iska ne. Asalin kalmar “Ton” (wanda jam’inta shi ne: Tons) na nufin tarin abu ne mai yawa; dandazonsa. Amma a fannin kimiyyar lissafi har wa yau ana amfani da ita wajen auna nauyin abu. Ton guda na nauyi daidai yake da kilogiram 1,016. Haka ma kalmar “Tons of Substance and Mass”, tana ishara ne ga tari ko dandazon wani irin nau’in sinadari wanda ke dauke da makamashi masu kamanceceniya da juna, masu yawa. Asalin kalmar “Substance” na nufin hakikanin abu ne; wajen siffa ko kama ko samuwa. Kalmar “Mass” kuma a ilimin fannin kimiyya na nufin yawan abu ne, musamman sinadarai ko makamashi, misali. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum, don Allah, mai sunana, bayanin Tekun Atlantika zurfinsa da ake cewa, ya kai zurfin mita dubu uku, a sanar da ni kamar tsayin kilomita nawa ke nan a tsaye?
Wa alaikumus salam, barka ka dai. Lallai kamar yadda ka karanta a baya, cewa zurfin Tekun Atlantika ya kai mita 3,926, kusan mita 4,000 dai ke nan a takaice. Idan aka kwatanta da nisa a kasa ko a tsaye kamar yadda ka bukata, daidai yake da kilomita 3.926, ko kuma kilomita 4 dai kenan. Domin a ka’idar lissafi a fannin kimiyya, mita 1,000 shi ne kilomita 1. Ke nan, mita 3,926 zai zama daidai da kilomita 3.926 ke nan. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Da fatan kana lafiya, tare da dukkan iyalanka baki daya. Don Allah Baban Sadik, ina son ka taimaka mini da bayani kan yadda ake dora hotuna a shafin Twitter? Kuma me ake nufi da kalmar “Fabourite” a shafin Twitter? Na gode. Daga Dauda Shu’aibu Luti, Jihar Bauchi. 08036907090. 08056907090.
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Dauda. Da fatan kana cikin koshin lafiya. dora hoto daskararre (Still image/picture) ko mai motsi (bideo) ba wani abu ba ne mai wahala a shafin Twitter. Idan ka shiga shafinka, sai ka je inda ake rubuta sako, wato inda aka rubuta: “What is happening?” Da zarar ka gama rubuta sakonka, sai ka matsa alama ko tambarin da ke kasan inda ka rubuta bayanan, na farko daga hagu ke nan, mai take: “Media” nan take za a budo maka ma’adanar waya ko kwamfutarka mai dauke da inda aka ajiye hotuna ko bidiyo, sai ka zabi hoto ko bidiyon da kake son makalawa ko dorawa. Shi ke nan ka gama. Ga misalin nan cikin hoton da ke wannan shafi na kawo maka, wanda na dauko daga shafina da ke Twitter. Hatta a waya na tabbata haka tsarin yake. Ba abu ba ne mai wahala.
Dangane da ma’anar kalmar “Fabourite” kuma, wannan kalma ba wai a Twitter kadai ba, a duk inda ka ganta a na’ura ko hanyar sadarwa ta zamani, tana nufin “shafi ko abin da kake so” ne a ranka, na gani ko na karantawa. A kan manhajar lilo kuma (Browser) tana iya nufin jakar bayanin da ke dauke da shafukan da ka taskance wadanda kake son karantawa a wasu lokuta na gaba. Da fatan ka gamsu.
Salaamun alaikum Abban Sadik. Hoton jirgin Titanic, shin, ainihin wanda yayi hatsarin ne na fim ne? Daga Adamu Zaria
Wa alaikums salam Malam Adamu. Ban san wanne ne ka gani ba daga cikin hotunan. Domin kasidar ta kai kashi wajen 4, kuma kowanne daga cikinsu akwai hoton dake da alaka da bayanin da ake yi. Amma duk da haka, hotunan da na lika shafin sadda nake rubutun sun kasu kashi biyu ne. Akwai wadanda hotunan fim din ne, masu dauke da Jaruman fim din. Sannan akwai hotunan da suka shafi lamarin gaba dayansa. Su wadannan hotuna an zano su ne daga hotunan wancan jirgi a sadda lamarin ke faruwa. Shi ya sa za ka ga launinsu baki da fari ne, babu launi. Wanda hakan ke nuna dadewa ne. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum, ina son a yi mana bayanin wai shin, akwai kasashen da ba su da amfani da fasahar Intanet ne a duniya? Na gode: Hassan Isah Tk, Katsina
Wa alaikumus salam, Malam Hassan barka ka dai. Dangane da kasashen da ba su amfani da fasahar Intanet a duniya, ina iya cewa babu wata kasa a duniya da fasahar Intanet ba ta kutsa ba. Illa dai ya danganci karancin masu amfani da fasahar ne; ko dai sanadiyyar talauci ko dokokin kasa da hukumomin gwamnatocin kasashen ke kan gaba wajen fasahar, don karya kadarin tasirinta ga al’ummarsu saboda wasu dalilai na siyasa ko al’ada ko addini.
A halin yanzu an kiyasta ana da mutane sama da biliyan bakwai masu rayuwa a wannan duniya. Cikin wannan adadi, kashi 40 ne kadai ke ta’ammali da fasahar Intanet. Sauran kashi 60 cikin 100 din suna cikin duhu har yanzu. Daga cikin wannan adadi na kashi 40 na masu amfani da fasahar Intanet, idan aka kasa su kashi 100 kuma, kashi 78 na kasashe masu duniya ne – tsakanin Amurka da Turai da wani bangaren Asiya – sauran kashi 32 cikin 100 kuma na kasashe talakawa.
Duk da haka, babu wata kasa da ba’a ta’ammali da wannan fasaha kamar yadda na sanar a sama, sai dai karancin masu amfani da ita. Don haka sai dai a ce kasashe masu karancin masu ta’ammali da fasahar Intanet. Masu dalilan talauci da karancin ci gaban fasahar sadarwa da tattalin arzikin kasa, galibi suna kasashen Afirka ne, musamman ta Yamma. A kasar Guinea misali, kashi 1.6 ne kadai na jama’ar kasar ke ta’ammali da fasahar Intanet. Bayan ita akwai kasashen Saliyo (Sierra leone), da kasar Afirka ta Tsakiya (Central African Republic) da kuma kasar Liberia. A wadannan kasashe duk, masu ta’ammali da fasahar Intanet ba su kai mutum dubu 200 ba. Wadannan kasashe dai ana ganin babban dalilin samuwar karancin masu ta’ammali da fasahar bai wuce talauci. Amma a kasashe irin su Kiyuba (Cuba) da Myammar (Bama), bayan talauci, akwai dalilan siyasa da al’adu. Daga cikin kasashe 207 da a ke da alkaluman masu amfani da Intanet a cikinsu, Najeriya ce ta 9 a yawan masu ta’ammali da Intanet a duniya, domin tana da mutane sama da miliyan sittin da rabi, kashi 38 ke nan na yawan ‘yan kasar wadanda suke ta’ammali da fasahar Intanet. Da fatan ka gamsu.