Amurka ce babbar kanwa uwar gami a rikicin Rasha da Ukraine — China
Ya ce Amurka na son ganin bayan Ukraine ne ta hanyar yakin
Jakadan kasar China a Rasha, Zhang Hanhui, ya zargi Amurka da zama babbar mai rura wutar rikicin Rasha da Ukraine.
Ya kuma zargi Amurkar da yunkurin murkushe Rasha ta hanyar ci gaba da fadada rundunar kungiyar kawancen tsaro ta NATO da kuma yunkurin mayar da Ukraine ’yar lelen Tarayyar Turai a maimakon Rasha.
- An kama mai shekara 70 kan luwadi da yaro mai shekara 12
- An sace surukar Ango Abdullahi da jikokinsa 4
A wata zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Rasha, TASS, jakadan ya ce, “A matsayinta na ummul’aba’isu kuma babbar kanwa uwar gami a rikicin Ukraine, Amurka ta ci gaba da kakaba wa Rasha takunkumai sannan tana ba sojojin Ukraine gudunmawar makamai.
“Babban birninta shi ne ta yi amfani da yakin wajen ganin bayan Rasha,” inji Zhang.
Kalaman jakadan na China sun zo daidai da dalilan da Rashar ta bayar na fada wa Ukraine da yaki, wanda ya kai ga asarar dubban rayuka da kuma raba miliyoyin ’yan kasar da muhallansu.
A yayin tattaunawar dai, jakadan na China ya ce dangantaka tsakanin kasarsa da Rasha ba ta taba yin armashi irin yanzu ba, yana mai cewa akwai fahimtar juna a tsakaninsu matuka.
Ko a watan Fabrairun da ya gabata dai sai da Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ziyarci takwaransa na China, Xi Jinping, a daidai lokacin da kasarsa ke shirin afka wa Ukraine da yaki.