Amurka da Birtaniya na ƙoƙarin lalata alaƙarmu da Nijeriya — Rasha

Rasha tana taya Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai.

Amurka da Birtaniya na ƙoƙarin lalata alaƙarmu da Nijeriya — Rasha

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin

Gwamnatin Rasha ta yi zargin cewa Amurka da Birtaniya da sauran ƙasashen Yamma na ƙoƙarin lalata alaƙarta da Nijeriya.

Rasha ta yi wannan zargi a yayin da take nesanta kanta da zanga-zangar da aka yi kan tsadar rayuwa ranar 1 ga watan Oktoba a Nijeriya.

A cewarta, ƙasashen yamma na ƙoƙarin lalata alaƙarsu da Nijeriya ta hanyar dangantasu da abubuwan da ke faruwa a ƙasar

Rasha ta yi wannan zargi ne cikin wata wasiƙa da Sakataren Watsa Labaran Ofishin Jakadancinta, Yury Paramonov ya aike wa Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya.

A bayan nan dai ana zargin ƙasar Rasha da hannu kan dambarwar siyasa a ƙasashen Mali da Burkin Faso da Nijar, ƙasashen da sojoji suka karɓe akalar jagoranci daga hannun farar hula.

Ana iya tuna cewa, a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar farkon watan Agusta a Nijeriya, an ga yadda jami’an tsaro suka riƙa cafke masu ɗaga tutar ƙasar Rasha, inda rundunar soji a ƙasar ta ce hakan tamkar laifin cin amanar ƙasa ne.

Wannan lamari ya janyo damuwa kan ko akwai sa hannun wasu daga ƙasashen waje kan zanga-zangar da ke gudana a ƙasar.

Sai dai ƙasar Rasha ta zargi Amurka da Birtaniya da Ukraine cewar suna alaƙantata da zanga-zangar domin lalata kyakykyawar alaƙarta da Nijeriya, inda ta shawarci gwamnatin ƙasar ta yi watsi da alaƙantasu da ake yi da zanga-zangar.

“Bayanan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da tsohon daraktan Ofishin Jakadancin Birtaniya a Nijeriya, David Robert da Ambasadan Ukraine a Nijeriya, Ivan Kholostenko suka yi babu kunya kuma ba tare da wata hujja ba na cewar ɗaga tutocin Rasha lokacin zanga-zanga a Nijeriya na nuna yadda ƙasar ke da hannu kan wannan lamari tare da yin gargaɗin cewar hakan zai ci gaba da faruwa.

“Ofishin Jakadancin Rasha na amfani da wannan dama domin fitowa ƙarara ya yi watsi da duk waɗannan zarge-zarge, tare da jaddada cewar Rasha ba ta da hannu kan zanga-zangar da ta faru a Nijeriya ko kuma wadda ake tunanin za ta faru a nan gaba.

“Har kullum Rasha na mutunta kasancewar Nijeriya a matsayin ƙasa mai cikakken iko na cin gashin kanta.”

Sakataran Ofishin Jakadancin na Rasha a Nijeriya, Yury Paramonov ya kuma miƙa saƙon taya murna daga Shugaban Rasha Vladimir Putun zuwa ga Shugaba Bola Tinubu kan zagayowar ranar samun ’yancin kan Nijeriya.