Amurka da Birtaniya sun taya Shugaba Sisi murnar lashe zabe
kasar Amurka da Birtaniya sun aika sakon taya murna ga sabon Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al- Sisi bisa nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a farkon makon jiya.kasashen biyu sun ce za su yi aiki tare da shi, amma ya dace ya mutunta ’yancin da kuma damar bayyana ra’ayi daga dukkanin […]

kasar Amurka da Birtaniya sun aika sakon taya murna ga sabon Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al- Sisi bisa nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a farkon makon jiya.
kasashen biyu sun ce za su yi aiki tare da shi, amma ya dace ya mutunta ’yancin da kuma damar bayyana ra’ayi daga dukkanin bangarorin siyasar kasar. A wani sako da fadar gwamnatin Amurka ta White House ta fitar a shekaranjiya Laraba ta bayyana fatanta na ci gaba da hulda da sabuwar gwamnatin a bangarori da dama. A ranar Talata ne kuma Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya ya bayyana cewa kasarsa za ta yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Masar don ci gaban kasashen biyu.
Hakazalika, kasashen larabawa ciki har da kasar Saudiyya yawancinsu sun bayyana sakon taya murna ga Mista Sisi. Saudiyya ta yi alkawarin jagorantar wani taro da zai tara wa sabuwar gwamnatin kudi don ta magance kalubalen tattalin arzikin da take fuskantar kasar. Sarki Abdullah bin Abdulaziz ya ce nasarar da Sisi ya samu da kuri’u kashi 96.9 cikin 100 na nuna cewa kasar Masar ta bude sabon babi.