Amurka da Iran za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Juma’a

Wannan yarjejeniyar wucin gadi ta yi sanadiyyar faɗuwar farashin mai a kasuwanni, sai dai ta bar batun makaman nukiliyar Iran ga tattaunawar gaba.

Amurka da Iran za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Juma’a

Jami’an Amurka da na Iran sun ce sun amince da wani tsari don kawo ƙarshen yaƙinsu, da toshe teku da Amurka ta yi wa Iran, da kuma sake buɗe mashigin ruwan Hormuz.

Wannan yarjejeniyar wucin gadi ta yi sanadiyyar faɗuwar farashin mai a kasuwanni, sai dai ta bar batun makaman nukiliyar Iran ga tattaunawar gaba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na dandalinsa na Truth Social da misalin ƙarfe 5 da rabi na yamma agogon Washington, wato ƙarfe 9 da rabi na dare ken an agogon GMT wannan Lahadi, inda yake cewa an kammala yarjejeniya da Iran.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, wanda ƙasarsa ta kasance mai shiga tsakani, ya sanar da cewa an cimma yarjejeniyar da sanyin safiyar wannan Litinin agogon yankinsa. Kuma an tsara za a sanya wa yarjejeniyar hannu a hukumance ranar Juma’a a ƙasar Switzerland.

Kodayake bai bayyana takamaime ko ilahirin sharuɗan wannan yarjejeniya ba, Sharif ya wallafa a shafinsa na X cewa yarjejeniyar ta ƙunshi kira ga gaggauta dakatar da ayyukan soja baki ɗaya a dukkan fuskoki, har da Lebanon.

Lebanon ta kasance lamarin da ke kawo tsaiko a yayin tattaunawar, inda Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah suka yi kunnen uwar shegu da kiran da Trump da sauran shugabanni suka yi musu na su dakatar da kai wa juna hare-hare a makonnin baya-bayan nan.

A cikin wata sanarwa, Sakatariyar Majalisar Ƙoli ta Tsaron Iran ta bayyana cewa za a kawo ƙarshen yaƙi da ayyukan soja gaba ɗaya a dukkan fuskoki, har da Lebanon, tun daga daren Litinin wannan Litinin.