Amurka da Isra’ila sun kunna wutar da ba za su iya kashewa ba — Iran
Shugaba Donald Trump, ya ce sun kai harin ne domin kare muradun Amurka.
Ƙasar Iran ta mayar da martani kan sabon hari na “gargaɗi” da ƙasashen Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar mata a safiyar yau Asabar.
Shugaban Kwamitin Tsaron Ƙasa na Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya ce harin da Isra’ila da Amurka suka kai mata tamkar sun kunno wutar da ba za su iya kashewa ba.
- An kama mai POS kan damfarar wata mata Naira dubu 375 a Kuros Riba
- Yadda yaƙi ya ƙazanta tsakanin Pakistan da Afghanistan
Azizi ya ce “mun gargaɗe ku! Amma kuka zaɓi kunno wutar da ba za ku iya kashewa ba” a wani saƙo da ya wallafa jim kaɗan bayan ƙaddamar masu da harin.
Iran ta kai hari a yankin Tekun Fasha
Gwamnatin Tehran ta mayar da martani mai ƙarfi, inda ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila da kuma wasu sansanonin soja a yankin Gabas ta Tsakiya da sojojin Amurka ke aiki a cikinsu.
Hukumomin Iran sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare kan wasu muhimman sansanonin soja na Amurka da ke yankin Tekun Fasha.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, Iran ta kai harin ne kan waɗannan wurare:
Al-Udeid Air Base da ke Qatar
Al-Salem Air Base a Kuwait
Al-Dhafra Air Base a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
US Fifth Fleet Base a Bahrain
Kazalika, AFP ya ruwaito cewa an ji tashin bama-bamai a babban birnin Saudiyya, Riyadh, a ranar Asabar.
Rahoton bai bayar da cikakken bayani kan inda bama-baman suka tashi ko musabbabin lamarin ba, haka kuma ba a tabbatar da asarar rayuka ko barnar dukiya ba zuwa yanzu ba.
Rahoton ya nuna cewa hare-haren na daga cikin martanin Iran kan abin da ta bayyana a matsayin barazana ga tsaronta, duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan irin barnar da aka yi ko asarar rayuka ba.
Bahrain ta yi Allah wadai da harin
Ƙasar Bahrain ta tabbatar cewa an kai harin ne kan wasu wurare da cibiyoyi a ƙasar, inda ta bayyana hakan a matsayin “keta haddin ƙasa da tsaro” na masarautar.
Ta bayyana harin wanda ba ta alaƙanta da kowace ƙasa ba a matsayin mai “haɗari” waɗanda ke zama barazana kai tsaye ga tsaron ƙasar da lafiyar al’umma da mazauna Bahrain, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Qatar News Agency ya ruwaito.
Ma’aikatar Tsaron Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta tabbatar cewa ƙasar ta fuskanci harin makaman masu linzami daga Iran, inda ta samu nasarar kakkaɓo wasu daga cikin makaman.
‘Muna shawartar mazauna Tehran su fice daga birnin’
Kwamitin Tsaron Ƙasa na Iran ya shawarci mazauna babban birnin ƙasar, Tehran, da su fice daga birnin sakamakon halin tsaro da ake ciki.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamitin ya ce: “Saboda yanayin da ake fuskanta a halin yanzu, muna ba da shawara, da ku fice daga birnin Tehran zuwa wasu wuraren, amma a yi hakan cikin natsuwa.”
Hukumomin tsaron sun jaddada muhimmancin ficewa cikin natsuwa tare da ɗaukar matakan kare kai, yayin da ake ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a ƙasar.
Har yanzu dai ana ci gaba da sa-ido kan lamarin, yayin da ƙasashen duniya ke nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar rikicin da ke ƙara ƙamari a Gabas ta Tsakiya.
Muna son kafa sabuwar gwamnati a Iran —Trump
Shugaba Donald Trump yayin wani jawabi da ya gabatar ta faifan bidiyo, ya ce Amurka wadda ke kare muradunta ta fara manyan ayyukan yaƙi a Iran bayan da Isra’ila ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami kan ƙasar.
Ya ce babban burinsu shi ne kawar da ɗaukacin shugabannin Iran tare da bai wa ‘yan ƙasar damar kafa sabuwar ƙasa.
A wannan safiyar ta Asabar ce Isra’ila ta sanar da ƙaddamar da wani sabon hari na gargaɗi kan Iran, kamar yadda Ministan Tsaron ƙasar, Israel Katz, ya bayyana.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce ta kai harin ne a matsayin “hari na rigakafi” domin kawar da wata babbar barazana, inda aka ayyana dokar ta-ɓaci ta musamman a faɗin ƙasar.
Hakan ya biyo bayan ƙarar ƙararrawar gargaɗi a Jerusalem, tare da saƙonnin gargaɗi da aka tura wa jama’a ta wayar salula game da abin da aka kira “mummunar barazana”.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi shirin ko ta kwana da na’urorinta na kariya daga hare-haren sama a yankuna daban-daban na kasar ga yuwuwar saukar makamai masu linzami zuwa Isra’ila a matsayin ramuwar gayya.
Rahotanni daga Iran sun ce an ji ƙarar fashewar bama-bamai da dama a babban birnin ƙasar, Tehran, a ranar Asabar.
Wani jami’in Amurka ya shaida wa Al Jazeera cewa hare-haren da aka kai an yi su ne ta hanyar haɗin gwiwar sojojin Isra’ila da Amurka.
Rahoton ya ce Amurka ta jibge manyan jiragen yaƙi da jiragen ruwan soji a yankin, domin matsa wa Iran lamba ta amince da yarjejeniya kan shirinta na makamashin nukiliya.
Sai dai har zuwa yanzu, ba a tabbatar da takamaiman wuraren da aka kai wa hare-haren ba, kuma hukumomi ba su fitar da bayanan asarar rayuka ko raunuka ba.
Wasu rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin hare-haren ya shafi wani yanki kusa da ofisoshin Jagoran Ƙoli na Addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
A cewar wata majiya da Reuters ta ambata, Ayatollah Khamenei ba ya cikin Tehran a halin yanzu, inda aka ce an sauya masa matsuguni zuwa wani wuri mai tsaro.
Hana tashi da saukar jirage
Ministan Sufuri, Miri Regev, ta bayar da umarnin rufe sararin samaniyar ƙasar baki ɗaya ga jiragen farar hula, a wani yunƙuri na ɗaukar mataki a sakamakon sabon yanayin tsaron da ya taso.
Ita ma Iraƙi ta sanar da rufe sararin samaniyarta, bayan Isra’ila ta tabbatar da kai hare-hare kan Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.
Hukumar labaran Iraƙi (INA) ta rawaito cewa ma’aikatar sufuri ta ƙasar ta fitar da sanarwar rufe sararin samaniyar Iraƙi gaba ɗaya, a wani mataki na kariya sakamakon sabon yanayin tsaro da ya taso a yankin.
An ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen sama, yayin da tashin hankali ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran.
Hukumar Kula da Sufurin Jirage ta Syria ta sanar da rufe wani ɓangare na sararin samaniyar ƙasar.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce, “za a rufe hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama na kudu … daga ranar Asabar ƙarfe 12:00 na rana (0900 GMT) tsawon awanni 12.”