Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniya

A ranar Talatar da ta gabata ne kasashen Amurka da Rasha suka rattaba hannu a wata yarjejeniyar fahimtar juna domin rage yiwuwar arangama tsakanin jiragen yakin kasashen biyu a sararin samaniyar Siriya, kamar BBC ta bayyana. Hakan ya zo ne bayan Amurkan ta zargi Rasha da gangancin lulawa da jiragen yakin ta kusa-kusa da na […]

Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniya
Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniya

A ranar Talatar da ta gabata ne kasashen Amurka da Rasha suka rattaba hannu a wata yarjejeniyar fahimtar juna domin rage yiwuwar arangama tsakanin jiragen yakin kasashen biyu a sararin samaniyar Siriya, kamar BBC ta bayyana.

Hakan ya zo ne bayan Amurkan ta zargi Rasha da gangancin lulawa da jiragen yakin ta kusa-kusa da na dakarun kawance da ke yaki da kungiyar IS a Siriya.
Kodayake, ba a dai bayyana abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa ba tukuna, amma ma’aikatar tsaro da ke Pentagon ta ce Rasha ce ta bukaci a kulla ta.
An ce yarjejeniya ba ta shafi tsara kai hare hare kan mayakan kungiyar ta IS ba, ko tattara bayanan sirri game da kungiyar ba.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaron Amurka ta ce sharuddan yarjejeniyar sun kunshi bangarorin biyu su bi ka’idodjin lulawa da jirage a sararin samaniyar Siriya, da rashin yiwa juna shisshigi a hanyoyin sadarda bayanai da jirage ke amfani da su.