Amurka da Rasha za su hada hannu don yakar IS

kasashen Amurka da Rasha sun bayyana cin ma wata yarjejeniya don musayar bayanan sirri a fafutukarsu yaki da kungiyar Daular Musulunci ta IS. kasashen biyu sun cin ma yarjejeniyar ne bayan wani taro ranar Talata, wanda shugabannin sojin kasashe fiye da 20 suka halarta a kasar Amurka don lalubo hanyoyin da za a kawo karshen […]

Amurka da Rasha za su hada hannu don yakar IS
Amurka da Rasha za su hada hannu don yakar IS

kasashen Amurka da Rasha sun bayyana cin ma wata yarjejeniya don musayar bayanan sirri a fafutukarsu yaki da kungiyar Daular Musulunci ta IS.

kasashen biyu sun cin ma yarjejeniyar ne bayan wani taro ranar Talata, wanda shugabannin sojin kasashe fiye da 20 suka halarta a kasar Amurka don lalubo hanyoyin da za a kawo karshen kungiyar IS.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa yana cikin damuwa matuka saboda abin da ya kira nasarar da kungiyar IS take samu a lardin Anbar da kuma garin Kobane da ke yankin kurdawa a Iraki. Ya kuma ce Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare ta sama wanda hakan ya sa aka iya dakile kungiyar daga karbe iko a garin Erbil da kuma Mosul.
“Wannan yaki ne da za a kwashe lokaci mai tsawo ana yi,” kamar yadda ya ce, amma ba tare da ba da haske kan hanyoyi da dabarun sojin da ake amfani da su a yanzu, wadanda suka ta’allaka da hare-hare ta sama.
Kodayake, wani jami’in sojin Amurka ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters bayan kammala taron, cewa suna sane da nasarar da kungiyar IS take samu ta kasa, duk da farmakin da ake kai mata ta sama. Kuma jami’in ya bayyana ta da nasarar wucin-gadi, inda a gaba reshe zai juye da mujiya.