Amurka da Turkiyya sun sasanta kan izinin shiga kasashen biyu

A cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Ankara ta wallafa a shafin ta na intanet, ta ce ta sassauta matakan haramta wa juna ba da takardar shiga kasashen biyu bayan samun tabbacin ingancin tsaro. Wannan matakin sassauta matakai na musanyar samun damar shiga kasashen biyu na zuwa ne kwana guda bayan […]

Amurka da Turkiyya sun sasanta kan izinin shiga kasashen biyu

A cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Ankara ta wallafa a shafin ta na intanet, ta ce ta sassauta matakan haramta wa juna ba da takardar shiga kasashen biyu bayan samun tabbacin ingancin tsaro.

Wannan matakin sassauta matakai na musanyar samun damar shiga kasashen biyu na zuwa ne kwana guda bayan ganawar Fira-ministan Turkiyya, Bin-Ali Yildirim a birnin Washington, tare da Mataimakin Shugaban kasar Amurka, Mike Pence. A baya dai Yildirim ya nuna takaici kan irin tsamin dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu ke shafar harkokin diflomasiyya ainun.

kasashen Turkiyya da Amurka da ke zama mambobi a kungiyar tsaro ta Nato, sun kasance cikin takun saka da juna bayan da hukumomin Turkiyya suka rika kame ‘yan Amurka da ke shiga kasar bisa zargin alaka da kungiyar malamin addinin nan kan kasar Turkiyya da ke samun mafaka a Amurka, Fethullah Gulen, malamin da gwamnatin shugaba Raccep Tayyib Erdogan suka dora wa alhakin yunkuri juyin mulki a shekarar 2016. 

Turkiyya kasa ce wacce bangarenta na yamma wanda ya fi girma ke cikin yankin yammacin Asiya, yayin da daya sashen ke yankin kudu maso yammacin Turai. kasar na da iyaka da Iran da Iraki da Armeniya da Azarbaijan da Jojiya da Bulgeriya da kuma Girka. Kasancewarta tsakanin Turai da Asiya ya ba ta muhimmanci a fannin diflomasiyya da cinikayya.