Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

Trump zai tabbatar da korar duk wasu baƙi da ke zaune a ƙasar ba bisa ka’ida ba.

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

Shugaban Amurka Donald Trump wanda aka rantsar a yau Litinin, ya ce gwamnatin ƙasar jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance saboda haka babu wani mata-maza.

Trump ya faɗi hakan ne a yayin bikin rantsar da shi a matsayin Shugaban Amurka na 47 wanda aka gudanar a Majalisar Tarayyar Amurka ta Capitol.

Da yake jawabi, Donald Trump ya ce zai zartar da ƙudirin cewa gwamnatin Amurka jinsi biyu kawai ta sani a hukumance, Namiji da Mace.

Haka kuma a cikin jawabin da Trump ya yi jim kaɗan bayan rantsar da shi, ya zayyano manyan ƙudirorin da zai mayar da hankali a gwamnatinsa, inda ya sha alwashin dawo da martaba da daraja da ƙima ta Amurka a idon duniya.

Ya bayyana alfaharinsa da cewa kwana guda kafin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa an tsagaita wuta a yaƙin da ake gwabzawa a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana cewa abu na farko da zai mayar da hankali a kai sh ine tabbatar da korar duk wasu baƙi da ke zaune a ƙasar ba bisa ka’ida ba.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC