Amurka: Kara da kiyashi ce
Gwamnatin Amurka ta umurci ofishin huldar jakadancinta da ke Najeriya ya tsara dabarar tattaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram don ceto ‘yan matan kwalejin da aka wafce a Chibok, a kudurinta na kuma daukan taimaka wa Gwamnatin Najeriya murkushe ta’addancin da ke wanzuwa fiye da shekaru biyar a wasu sassan kasar nan. Hakan kuwa ya […]
Gwamnatin Amurka ta umurci ofishin huldar jakadancinta da ke Najeriya ya tsara dabarar tattaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram don ceto ‘yan matan kwalejin da aka wafce a Chibok, a kudurinta na kuma daukan taimaka wa Gwamnatin Najeriya murkushe ta’addancin da ke wanzuwa fiye da shekaru biyar a wasu sassan kasar nan. Hakan kuwa ya biyo bayan umurnin da Shugaba Barack Obama na kasar Amurka ne ya bai wa Sakataren hulda da kasashen waje, John Kerry don sanar da Shugaba Goodluck Jonathan cewa Amurka ta amince da tayin agaji da ya yi mata don kawo karshen tashin-tashinar da ta’addancin da Boko Haram ke haddasawa a Najeriya da kuma aikata dukkan abubuwan da za ta iya yi don magance matsalarsu dungurungun.
To muddin dai hakan zai iya kawo karshen ta’addancin da ya yi sanadiyyar fatattaka wasu sassan Arewa, ya kuma janyo dalilan da suka haddasa dimbin hasarar rayuka da dukiyar bayin Allah, da kuma rashin ‘yan uwa da ‘ya’ya da mazaje, sai a yi marhaban da wannan mataki, domin idan aka mika takobi ga wanda ruwa ya ciwo, haka nan zai danke ta, komai kaifinta kuwa, don ya kubuta daga halaka. Jama’ar yankunan da wannan masifa ke ta addaba sun kosa su ga an kawo karshen tashin-tashinar da ke rage wa rayuwarsu armashi, wacce kuma ta dabaibaye su, tana hana su gudanar da ibadarsu yadda ya kamata, ko aiwatar da harkokin zumunta da na kasuwanci akan kari.
Yawan tashe-tashen hankula da kashe-kashe sun sa al’umomin jihohin Barno da Yobe da kuma Adamawa kidimewa, har suka fice daga kyakkyawan hayyaci, musamman ganin yadda ‘ya’yansu ba su iya zuwa makaranta. A jihar Yobe ‘yan ta’adda sun kai hare-hare har sau hudu a makarantun sakandare, kuma hakan ya yi sanadiyyar rasuwar dalibai 137 a garuruwan Damaturu da Mamudo da Gujba da kuma Fataskuma, daga watan Yunin 2013 zuwa na Fabrairun 2014.
A yanzu haka yawancin manyan makarantu a shiyyar Arewa-maso-Gabas duk a kokkone suke, wasu kuma a rurrufe. Sa’annan kuma sace ‘yan matan wata makaranta a Chibok, kudancin Jihar Barno a kwanakin baya, ya kara sa al’amarin tabarbarewa, jama’a kuma na ta fatan Allah ya kawo musu dauki domin gwamnatocin Najeriya sun kasa kare makarantu da dalibai daga hare-haren ‘yan ta’adda.
To amma ya wajaba a yi taka-tsantsan game da haka domin kada a haifi da mara idanu bayan gayyato Amurka ido rufe. Ita Amurkan da Shugaba Jonathan ke son yayowa, da sunan taimako don yakar ‘yan ta’adda, sananniya ce ga ‘yan Najeriya, kuma kaidinta da kiyayyar da take yi wa wasu jinsin ‘yan Najeriya ba boyayyu ba ne. Ana iya cewa mai nema ne a duhu sai kawai ya samu a sarari. Saboda haka da zarar Amurka ta samu gindin zama a kasar nan, sakamakon wannan sabuwar manufar, to ba fa iyakacin ta taimakawa ne don kawar da ta’addancin da ake ta riritawa a halin yanzu ba, a’a, za ta yi sabuwar shimfidar aiwatar da wata ta’asa ce can daban don biyan burinta, walau wanda ya jibanci yaki da addinin da wasu suka yi imani da shi ko haddasa yamutsin da zai ba ta damar zama dirshan, ta mike kafa, sai Mahdi ya zo, ya ture. A takaice dai Amurka ba tana son zuwa don agaza wa Najeriya ba ne, sai dai don ta tatse arzikinta ne karkaf. To tilas ne a dauki kwararan matakan hana ta baje kolinta yadda take so yayin da ta kutso Najeriya.
Yanzu babu abin da ‘yan Najeriya ke matukar bukata illa samun sa’ida daga wadannan bala’o’in, su kuma samu su dan sarara daga bala’o’in da ta’addancin ke haddasawa. Anya kuwa hakan ba zai zame wata ishara ce ba ga kasashen duniya cewa Gwamnatin Najeriya ba ta iya kare ‘ya’yanta, kuma ba za ta iya samun galba kan ‘yan ta’adda ba sai ‘yan wata kasa sun taimaka? Abin kunya ne a ce Amurka ta fi nuna damuwa game da gwamnatin Najeriya don kare rayuka da dukiyar ‘yan kasarta, domin kuwa ta rigaya ta karaya, ta nuna cewa ba za ta iya da masu son kai kasar kasa ba.
Dukkan alamu na nuna cewa Najeriya ta gaza, ta kuma hau turbar daidaicewa, musamman ma saboda ganin cewa rikice-rikicen da ke haddasa zaman lafiya a sassan Arewacin kasar nan sun gawurta, duk da haka nan kuma gwamnatin tarayya ta kasa tashi haikan don magance matsalolin tsaron da ke barazanar wargaza ta. To idan har ba gwamnati ta tashi tsaye ne ba don gano bakin zaren warware wannan al’amarin da kanta, zai yi wuya wasu kasashe su yi mata haka nan cikin ruwan sanyi. Amurka da kawayenta sun haddasa rikice-rikice da yawa a wasu kasashen duniya, sun kuma yi tsalle guda sun shiga-uku game da haka, sun kuma yi tsalle fiye da sau dari, sun kasa ficewa.
Barazanar banza da wofi ce wadannan kasashe ke yi game da taimakon Najeriya, domin su ma akan Najeriyar suke dogara don taya su yakin zaluncin da sukan tsokano a wasu kasashen. Kallon kitse Najeriya ke yi wa rogo. Amurka dai huhun ma’ahu ce, kuma sai a yi hankali domin kara da kiyashi ce, Jonathan na sane da haka, ga shi nan kuma ya dauka.