Amurka na ci gaba da farautar Joseph Kony

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta tura jiragen saman soji da kuma dakarun musamman a ci gaba da yunkurin da take na farautar madugun mayakan tawayen Uganda, Joseph Kony. Ta tura jirage hudu kirar Cb-22 Osprey da wasu  jiragen da zasu yi masu jigilar mai da suke bukata, sai kuma dakaru 150 da za […]

Amurka na ci gaba da farautar Joseph Kony

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta tura jiragen saman soji da kuma dakarun musamman a ci gaba da yunkurin da take na farautar madugun mayakan tawayen Uganda, Joseph Kony.
Ta tura jirage hudu kirar Cb-22 Osprey da wasu  jiragen da zasu yi masu jigilar mai da suke bukata, sai kuma dakaru 150 da za su isa kasar ta Uganda nan ba da jima wa ba.
Kotun Manyan Laifuffuka da ke birnin Hague ce ke neman Mista Kony ruwa-a-jallo bisa zargin aikata laifukan yaki. A cikin shekarar 2011 dai Amurka ta tura wasu dakarun musamman su 100 don taimakawa kasashen Afirka su cafke madugun mayakan ‘yan tawayen.
kungiyar ‘yan tawayen da yake jagoranta wato Lord’s Resistance Army ta yi kaurin suna ne gurin kisan mutanen bila-adadin da sassare wa wasu sassan jiki da kuma tilas ta wa yara shiga aikin soji.
kunkiyar ta fara bayyana ne a cikin shekarun 1980 a kasar Uganda, amma zuwa yanzu mayakan kungiyar sun addabi kasashe kamar su Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar  Damukradiyyar Congo.
Dakarun da Amurkan ta tura za a tsugunar da su ne a Uganda, amma za a aike da wasu cikinsu kasashen da ke fama da hare-haren kungiyar.
A bara ne dai Amurka ta bayyana tayin tukwuicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga cafke jagoran kungiyar, Joseph Kony.