Amurka na yi wa tsinke, inji yaron da ya makale a kwandon tayoyin jirgin sama zuwa Legas

Yaron da ya makale a kwamdon tayar jirgin sama aka yi tafiyar sa’a daya da shi daga Benin zuwa Legas ya bayyana aniyarsa cewa Amurka ya yi wa tsinke, ita ma mahaifiyarsa ta bayyana yadda danta ya shagaltu da kallon fina-finai a talabijin. kuma ta tabbata fina-finan ne suka cusa masa ra’ayin tafiya kasashen duniya […]

Amurka na yi wa tsinke, inji yaron da ya makale a kwandon tayoyin jirgin sama zuwa Legas

Yaro tare da mahaifiyarsa tana amsa tambayoyiYaron da ya makale a kwamdon tayar jirgin sama aka yi tafiyar sa’a daya da shi daga Benin zuwa Legas ya bayyana aniyarsa cewa Amurka ya yi wa tsinke, ita ma mahaifiyarsa ta bayyana yadda danta ya shagaltu da kallon fina-finai a talabijin. kuma ta tabbata fina-finan ne suka cusa masa ra’ayin tafiya kasashen duniya a jirgin sama, kamar yadda kanensa ya bayyana. Domin ya sha gaya masa cewa ‘wata rana zai tafi kasashen waje a jirgin sama.’
A lokacin da wannan yaro ya fice daga gidansu, mahaifiyarsa ta tafi wurin ’yar uwarta da ta haihu, ta kuma bar shi da yayarsa da kannensa, inda suka yi fada da yayar tasa a kan kallon talabijin.
“Na yi matukar girgiza da na ji cewa dana ya bata, amma da na tambayi ’yata, sai ta bayyana mini cewa sun yi fada da shi ne a kan kallon fim cikin tsakar dare. Har na yi shirin kai rahoton batarsa, sai surukata ta bugo mini daga Jamus, cewa labarin dana ya bazu a shafuykan sadarwa na intanet,” injita.
“daya daga cikin kannen Daniel ya ce ya gan shi lokacin da yake cire litattafansa daga cikin jakar makarnata. Sai na tambayi makwaftana ko wani cikinsu ya ganshi, sai suka ce  wajen karfe biyar sun ji motsi, a lokacin da yake bude kofa, amma ba su yi tunanin dana ba. Bai cika fita waje ba. Abin da kawai na sani game da shi, shi mai yawan kallon fina-finai ne, amma ba shi da abokai,” a cewarta.
Yaro dai bai taba bayyana wa wani burinsa ba, sai wani kanensa, wanda ya sha ji daga bakinsa cewa ‘wata rana zai tafi kasar waje a jirgin sama.
Ya shammaci jami’an tsaro da ma’aikatan filin jirgin sama, aka yi tafiyar sa’a da rabi da shi daga Benin zuwa Legas, a jirgin Arik Air, ranar Lahadin da ta gabata.
Yaron da ya makale a tayar jirgin samaDaniel Ihekina ya shammaci jami’an tsaron filin jirgin sama, inda ya buya a inda tayoyin jirgi ke shigewa, kafin a tashi, a cewar mai magana da yawun kamfanin safarar jiragen sama na  Arik Air, Ola Adebanji, a hirar da ya yi da manema labarai.
Fasinjoji sun ga yaron ya fito daga gidan tayoyin jirgin a Benin, don haka suka ankarar da ma’aikatan jirgin.
“Kan yadda aka yi ya shiga cikin tayoyin jirgin, wannan al’amari ne da ya rage ga hukumomi su gudanar da bincike,” a cewar Adebanji. “Ya yi sa’a da ya rayu. Mafi yawan wadanda suka kwatanta irin wannan ba su rayu ba,” inji shi.
Ya ce jirgin ya tashi sama ne da nisan kafa dubu 21, saboda tafiyar ba mai nisa ba ce, al’amarin da ya taimaka wa yaro ya tsira da ransa, a cikin iska mai sanyi.
Adebanji ya ce har yanzu ’yan sanda na binciken Ihekina, kuma ya bayyana cewa iyayensa ne ke azabtar da shi.
Har yanzu dai bincike bai gano sirrin yadda aka yi wannan yaro ya shammaci jami’an tsaron filin jirgin sama da ama’aikatan Arik Air ya buya a cikin tayoyi.