Amurka ta bukaci ’yan kasarta su fice daga Libya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bukaci ’yan Amurka mazauna Libya da su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba, saboda halin rashin tabbas da kuma tashe-tashen hankulan da ke faruwa a can.Sanarwar ta ce saboda halin da Libyar ta fada kowai na ina faruwa da su. Wannan ya sa, a ranar Talata, gwamnatin […]
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bukaci ’yan Amurka mazauna Libya da su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba, saboda halin rashin tabbas da kuma tashe-tashen hankulan da ke faruwa a can.
Sanarwar ta ce saboda halin da Libyar ta fada kowai na ina faruwa da su. Wannan ya sa, a ranar Talata, gwamnatin Amurkar ta aika da sojan ruwanta guda 1000 don gudanar shirye-shiryen dawo da Amurkawan gida.
Ana ci gaba da bayyana damuwa kan Libyar ne saboda hare-haren da bijirarren Janar Khalifa Haftar ya kaddamar kan masu kaifin kishin addinin Musulunci a biranen Benghazi da kuma Tripoli.
A cikin makon jiya ne, Janar Khalifa ya bukaci ma’aikatar shari’ar kasar da ta nada gwamnatin da za ta gudanar da sabon zabe domin gwamnati mai ci ta na taimakawa ayyukan ta’addanci. Wasu ’yan kasar na goyon bayan wannan matakin nasa, amma gwamnatin kasar ta bayyana matakin da kalmar “juyin mulki” kuma ta umarci kama duk wani wanda ke da hannu a ciki.