Amurka ta gana da sojojin da suka yi wa Bazoum juyin mulki a Nijar

Abu ne mai wahala a samu mafita. Sun yi tsayin-daka game da manufarsu.

Amurka ta gana da sojojin da suka yi wa Bazoum juyin mulki a Nijar

Wata babbar jami’ar diflomasiyyar Amurka ta je Yamai babban birnin Nijar ranar Litinin inda ta gana da manyan jami’ai na sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Victoria Nuland, Mataimakiyar riko ta Sakataren Harkokin Wajen Amurka ta shaida wa manema labarai cewa ta gana da mutumin da yake bayyana kansa a matsayin shugaban rundunar tsaro ta sojojin da suka yi juyin mulki, Moussa Salaou Barmou da wasu kanar-kanar guda uku.

Sai dai ba a bar ta ta gana da jagoran juyin mulki Abdourahamane Tchiani da kuma hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.

Ta kara da cewa ba a samu ci-gaba a ganawa “mai wahala” da ta yi da sojojin ba.

Nuland ta ce Washington ta bayar da shawarar yadda za a dawo da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar amma sojojin ba su nuna wata sha’awa ta bayar da hadin kai ba.

Hasalima ta kai ziyarar ce a yayin da sojojin suka nada tsohon Ministan Kudi na kasar Ali Mahamane Lamine Zeine a matsayin sabon Firaiminista.

Ta bayyana cewa ta gaya wa sojojin cewa za su iya fuskantar takunkumin kan tattalin arziki sannan Amurka ta janye tallafinta ga kasar idan ba su koma bariki ba.

“Tattaunawar da muka yi ta keke-da-keke ce sannan a wasu lokutan mai wahala, saboda, muna so a samu mafita. Abu ne mai wahala a samu mafita. Sun yi tsayin-daka game da manufarsu, kuma babu zancen dawo da tsarin mulki a shirinsu,” in ji Nuland.

Nuland ta je Yamai ne a yayin da kasashen duniya ke ci gaba da matsa lamba kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da su mayar da hambararren Shugaba Bazoum.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo