Amurka ta gargadi Najeriya kan sake dage zabe

Kwamitin Harkokin Wajen Majalisar Walilan kasar Amurka ya ja kunnen gwamnatin Najeriya akan duk wani yunkuri na kara dage zabe. Matakin ya samu goyon bayan dukkanin ’yan kwamitin, inda kuma suka bayyana mahimmancin zaben da kuma barazanar daukar mataki idan aka kara dage zaben. Sun ce duk da rikicin Boko Haram wanda ya haifar da […]

Amurka ta gargadi Najeriya kan sake dage zabe
Amurka ta gargadi Najeriya kan sake dage zabe

Kwamitin Harkokin Wajen Majalisar Walilan kasar Amurka ya ja kunnen gwamnatin Najeriya akan duk wani yunkuri na kara dage zabe.

Matakin ya samu goyon bayan dukkanin ’yan kwamitin, inda kuma suka bayyana mahimmancin zaben da kuma barazanar daukar mataki idan aka kara dage zaben. Sun ce duk da rikicin Boko Haram wanda ya haifar da damuwa kan gudanar da zaben, har ila yau ’yan majalisar sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta yi dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da ta gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali.
Har ila yau, ’yan majalisar sun yaba wa kungiyar Tarayyar Afirka saboda goyon bayan da ta nuna da kuma yadda ta aika da dakarun da za su yaki ’yan boko Haram. Sai dai bayan cimma wannan kudirin ne Shugaban Kwamitin ya ce, “ Akwai alamu sosai da suka sa ake kiran kungiyar Boko Haram da sunan kungiyar IS din nahiyar Afirka.”
A karshe ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ci gaba da aiki tare da kasar Amurka da kuma makwabtanta wato kasahen Chadi da Nijar da kuma Kamaru domin ganin bayan kungiyar. Kuma ya ce ya dace gwamnatin Najeriya ta bai wa dakarun hadin gwiwar da ke yaki da Boko Haram dukkannin goyon bayan da suke bukata.