Amurka ta goyi bayan Isra’ila kan harin da ya kashe mutum 500 a asibitin Gaza

Shugaban Amurka, Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga matsayar Isra’ila kan harin bom da ya kashe Falasdinawa kimanin 500 a wani asibiti a Zirin Gaza

Amurka ta goyi bayan Isra’ila kan harin da ya kashe mutum 500 a asibitin Gaza

Biden da Netanyahu

Shugaban Amurka, Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga matsayar Isra’ila kan harin bom da ya kasa Falasdinawa kimanin 500 a wani asibiti a Zirin Gaza.

Biden, wanda ya kai wa Isra’ila ziyarar goyon baya a ranar Laraba, ya ce ya yi amannar ba Isra’ila ba ce ta kai hari a asibitin da ke Kudancin Zirin Gaza.

Rundunar Sojin Isra’ila dai ta yi ikirarin cewa wani bom da mayakan Falasdinawa Islamic Brigade suka harba ne ya yi kuskure ya fada a asibitin, kuma za ta gabatar da hujjar da ke tabbatar da hakan.

A loacin da yake ganawa da Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv, Biden ya ce, “Daga abin da na gani, bisa dukkan alama, daya bangaren ne ya kai harin ba ku (Isra’ila) ba.”

Biden ya bayyane kayatuwarsa da abin da Isra’ilawa suka yi wa Falasdinawa a cikin kwanaki 12 da suka kwashe suna zagargazar Zirin Gaza.

Ya ce “Jama’ar Isra’ila — kun burge ni da irin jajircewa da jarumta da kuka nuna.”

Wasu masu sharhi na zargin harin asibitin, shiryayyen abu ne da Isra’ila ta kai, da sani da kuma goyon bayan Amurka. Haka kuma akwai zargin cewa Amurka ce ta kare bom din da aka kai harin da shi.

Tun a lokacin da Sakataren Amurka, Antonyy Blinken ya ce Isra’ila da Amurka sun yi ittifakin aiki tare domin ba da damar kai kayan agaji a Zirin Gaza.

Hukumomin lafiya a Zirin Gaza sun ce mutane da bom din ya kashe mutum sama kimanin 300 a asibitin, inda suke zaman mafaka a yankin, bayan sojojin Isra’ila sun umarci Falasdinawa su koma Kudancin Gaza, gabanin samamen da ke shirin kaiwa a Arewaci.