Amurka ta janye sojojinta daga Najeriya

Janar Anderson ya ce an kammala aikin da aka tura dakarun domin yi, saboda haka aka mayar da yawancinsu Amurka.

Amurka ta janye sojojinta daga Najeriya

Amurka ta sanar da janye yawancin dakarunta da ta tura Najeriya domin taimakawa a yaƙi da ƙungiyar ISIS da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke yankin Tafkin Chadi.

Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka a Turai da Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ta intanet bayan kammala Taron Manyan Hafsoshin Tsaro na Afirka na shekarar 2026.

A watan Fabrairun 2026 ne Amurka ta tura kimanin sojoji 200 zuwa Najeriya domin tallafa wa rundunar sojin ƙasar da bayanan sirri, sa ido da kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci.

Janar Anderson ya ce an kammala aikin da aka tura dakarun domin yi, saboda haka aka mayar da yawancinsu Amurka.

Sai dai ya tabbatar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da bai wa Najeriya goyon baya ta hanyar musayar bayanan sirri da sauran taimakon da gwamnatin Najeriya ta buƙata.

Ya ce haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya taimaka wajen kawo cikas ga ayyukan ISIS, kuma ya haifar da nasarar wani samame da aka kai a watan Mayun 2026, wanda ya yi sanadin kashe Abu-Bilal Al-Minuki, mataimakin jagoran ƙungiyar ISIS na biyu, a maɓoyarsa da ke Jihar Borno.

A cewarsa, rundunar sojin Najeriya tana da ƙwarewa da ƙarfin da za ta iya tunkarar matsalolin tsaro, yayin da Amurka ta bayar da gudunmawa ta fuskar bayanan sirri da wasu fasahohi na musamman da suka taimaka wajen samun wannan nasara.

Ya ƙara da cewa abin da aka cim ma ya nuna muhimmancin musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe, maimakon dogaro da zaman dakarun ƙasashen waje na dogon lokaci.

Janar Anderson ya kuma buƙaci ƙasashen Afirka su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri domin yaƙar ta’addanci, fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke ƙetare iyakoki.

Ya ce irin wannan haɗin gwiwar ya taimaka wajen kama wani jirgin ruwa da ke ɗauke da tan 31 na hodar iblis da aka taso da ita daga Kudancin Amurka ta bi ta gabar tekun Yammacin Afirka, lamarin da ya kafa tarihi a matsayin mafi girman kame miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi a teku.

A cewarsa, ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka, ƙasashen duniya da kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen inganta tsaro, bunƙasa tattalin arziki da jawo ƙarin zuba jari a nahiyar.