Amurka ta jefa bama-bamai 23,144 a yankunan Musulmi a bara
Wani mai bin diddigin al’amuran hulda da kasashen waje na Amurka mai suna Micah Zenko ya bankado yadda kasar Amurka ta jefa bama-bamai a wasu kasashe, inda ya ce daga ranar 1 ga Janairun bara zuwa karshen shekara Amurka ta jefa bama-bamai dubu 23 da 144 a kasashen Musulmi da suka hada da Iraki da […]
Wani mai bin diddigin al’amuran hulda da kasashen waje na Amurka mai suna Micah Zenko ya bankado yadda kasar Amurka ta jefa bama-bamai a wasu kasashe, inda ya ce daga ranar 1 ga Janairun bara zuwa karshen shekara Amurka ta jefa bama-bamai dubu 23 da 144 a kasashen Musulmi da suka hada da Iraki da Syria da Afghanistan da Pakistan da Yemen da kuma Somaliya.
Jaridar AlterNet da ake bugawa a Intanet ce ta bayyana haka a fitowarta ta ranar 10 ga Janairun nan.
Mai bin diddigin wanda ya gabatar da wani jadawali da ya nuna irin yadda Amurka ke tafka barna a wasu kasashen, ya ce ba tare da lura da dacewa ko rashin dacewar kai hare-haren ba, wannan ya nuna ywadda Amurka take ruguza kasashen Musulmi.
Jadawalin ya nua cewa Amurka ta jefa bama-bamai dubu 22 da 110 a kasashen Syriya da Iraki a bara, sai guda 947 a Afghanistan da 11 a Pakistan da 58 a Yemen da 18 a Somaliya, jimilla dubu 23 da 144.
Rahoton ya ce duk da Amurka ta jefa bama-bamai 947 a Afghanistan a bara, nazari na baya-bayan nan da Mujallar Harkokin kasashen Waje ta kasar ta fitar ya nuna kungiyar Taliban ne take rike da mafi yawan kasar Afghanistan tun shekarar 2011, kuma ga shi Amurka ta shiga shekara ta 16 duk da alkawarin da Shugaba Barack Obama ya sha yin a janye dakarun Amurka daga kasar.
A watan Oktoban bara ne Shugaba Obama ya canja ra’ayinsa, inda ya ce sojojin Amurka za su ci gaba da zama a Afghanistan har zuwa karshen badi.