Amurka ta juya wa Isra’ila baya a taron MDD kan tsagaita wuta a Gaza

Ran Netanyahu ya ɓaci bayan amincewa da ƙudurin kwamitin sulhu na MDD kan tsagaita wuta a Gaza.

Amurka ta juya wa Isra’ila baya a taron MDD kan tsagaita wuta a Gaza

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da ƙudirin neman a tsagaita wuta a Gaza nan take.

Wannan shi ne a karon farko da aka aka amince da ƙudirin tun bayan barkewar rikicin a yayin da Amurka ta ƙauracewa hawa kujerar naƙi.

An samu nasarar amincewa da ƙudirin ne bayan Amurka ta ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a a zaman kwamitin na ranar Litinin, saɓanin yadda ta saba yi a baya.

Kwamatin ya sha fama da rikita-rikita bayan ɓarkewar yaƙin tun daga watan Oktoba, inda ya kasa yin kiran a tsagaita wuta.

Matakin ya nuna irin lalacewar alaƙa tsakanin Isra’ila da babbar ƙawarta Amurka game da yaƙin da take yi a Gaza.

A baya dai Amurka ta sha ƙin amincewa da kiran tsagaita wuta tana mai cewa yin hakan zai kawo wa tattaunawar da ake yi cikas game da sakin mutanen da ake garkuwa da su.

Ƙudirin wanda ya samu goyan bayan ƙasashe 14, ya bukaci tsagaita wuta a Gaza nan take albarkacin watan ramadan tare da sakin ilahirin mutanen da hamas ke garkuwa da su.

Hawa kujerar naƙin wani gagarumin sauyin manufa ne daga bangaren Amurka, wacce ke amfani da matsayarta ta me kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wajen hawa kujerar naƙi a kudirori 3 da aka zartar a baya na neman tsagaita wuta a Gaza.

Matakin ya biyo bayan karuwar matsin lambar da gwamnatin Shugaba Joe Biden ke fuskanta daga cikin jam’yyarsa, da ma kawayen Amurka na kasa da kasa, akan cewa dole Amurka ta ƙara yin matsin lamba akan Isra’ila ta takaita hare-haren da take kai wa Gaza.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da adadin waɗanda suka mutu a Zirin Gaza ya zarta mutum dubu 32 kuma fiye da mutane miliyan guda ke daf da faɗawa cikin ja’ibar yunwa.

A baya Amurka ta yi karan tsaye ga kudirorin MDD da ke neman tsagaita wuta nan take har sau uku, har ma da wanda gamayyar ƙasashen Larabawa suka gabatar a watan da ya gabata, inda ta kasance kasa ɗaya tilo daga cikin mambobin Kwamitin Tsaron MDD 15 da ta hau kujerar naƙi.

Amurka ta soki Isra’ila game da ƙaruwar Falasɗinawan da take kashewa a Gaza, wanda akasarinsu mata da ƙananan yara – saboda hare-haren Isra’ila, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.

‘Firaiministan Isra’ila Netanyahu ya ji takaici’

Ran Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ɓaci bayan amincewa da ƙudurin kwamitin sulhu na MDD kan tsagaita wuta a Gaza, in ji Sanata Bernie Sanders.

“Ran Netanyahu ya ɓaci. Ya soke zuwan wata tawaga birnin DC saboda Amurka ta ƙaurace wa ƙudurin da ke neman tsagaita wuta,” in ji Sanders a X.

Ya ƙara da cewa, “amma takaicin da ya jin bai kai yadda zai ƙi karɓar dalar Amurka biliyan 3.3 na masu biyan haraji ba da nufin tallafa wa yaƙinsa na rashin ɗa’a.

“Ba za a sake bai Netanyahu kuɗaɗen da zai kashe yaran Falasdinawa da yunwa ba.”