Amurka ta kakaba haramcin biza kan wadanda suka kawo hargitsi a Zaben 2023
Amurka na goyon bayan Najeriya wajen karfafa dimokuradiyyarta.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya ce ya dauki matakin haramta wa wasu ’yan Najeriya shiga kasarsu, saboda rawar da suka taka wajen kassara dimokuradiyya a lokacin zabukan 2023 da suka gabata.
Wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka ya fitar, ta ce sun dauki matakin ne domin karfafawa tare da nuna goyon bayan Amurka ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya da ma duniya baki daya.
- Isra’ila da Falasdinu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
- Matashi ya kone gidan iyayen budurwarsa saboda yaudara
Sanarwar ta ce “Mun dauki matakin kakaba haramcin bayar da biza ga wasu mutane a Najeriya da suka taka rawa wajen yi wa dimokuradiyyar kasar zagon kasa musamman a lokacin zabukan 2023.
Sai dai Ofishin Jakadancin Amurkar bai zayyana sunayen mutanen da matakin hana su shiga Amurkan ya shafa ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa an dauki matakin ne kan wasu tsirarun mutane, ba wai al’ummar kasar ko gwamnati ba.
“A karkashin dokokin kasarmu, wadannan mutanen ba su cancanci samun biza zuwa Amurka ba, sakamakon rawar da suka taka wajen yi wa dimokuradiyyar Najeriya zagon kasa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ce mutanen sun aikata laifukan da suka kunshi razanar da masu kada kuri’a ta hanyar yi musu barazana, da tayar da hargitsi, da canza sakamakon zabe da sauran laifukan da suke yi wa dimokuradiyyar kasar zagon-kasa.
Matakin kamar yadda sanarwar ta yi bayani na zuwa ne don nuna goyon bayan da Amurka ke bai wa Najeriya wajen karfafa dimokuradiyyarta.