Amurka ta karbe wani bene manlakin Iran
kasar Amurka ta karbe wani bene mai hawa 36 da ke birnin New York wanda ta ce manlakin kasar Iran ne kuma kasar na amfani da shi wajen yada manufofinta a Amurka.A martanin da ta mayar kan matakin, Iran ta ce wannan ba dai-dai ba ne kuma ya saba ‘yancin bin kowane addini da mutum […]
kasar Amurka ta karbe wani bene mai hawa 36 da ke birnin New York wanda ta ce manlakin kasar Iran ne kuma kasar na amfani da shi wajen yada manufofinta a Amurka.
A martanin da ta mayar kan matakin, Iran ta ce wannan ba dai-dai ba ne kuma ya saba ‘yancin bin kowane addini da mutum yake ra’ayi wanda Amurkan ke ikirarin karewa. Amma ma’aikatar shari’ar Amurka ta fitar da wata sanarwa cewa za ta sayar da ginin, kuma kudin da aka saye shi za ta raba wa mutanen da hare-haren ta’addancin da ke samun goyon bayan Iran ya shafa.
Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce karbe ginin wanda yake gudanar da ayyukan agaji ga jam’a ya jefa shakku a zukatan wadanda suke wa ma’aikatar shari’ar Amukar kallon wata ma’aikata da ke wa jama’a adalci.
A shekarar da ta gabata ne dai wata babban kotu a kasar ta yanke hukuncin cewa ta kwace ginin wanda a cewarta yana dauke da kadarorin Iran ne kuma wanda hakan ya saba wa matakan takunkumin da Amurka ta kakaba mata.
Takaddama ta baya-bayan nan tsakanin kasashen biyu dai ita ce wanda ta biyo bayan sanya hannu da Shugaba Barack Obama ya yi a wata doka da ta hana Jakadan Iran Hamid Aboutalebi shigowa kasar, a matsayinsa na Jakadan kasar a zauren Majalisar dinkin Duniya da ke birnin New York sakamakon zarginsa da hannu a wata garkuwa da aka yi da wasu Amurkawa da aka yi a kasar ta Iran a shekarar 1979.