Amurka ta ki yarda Poland ta ba Ukraine jiragen yaki
Zelensky na rokon kasashen Turai su taimaka wa Ukraine da jiragen yaki
Amurka ta ki amincewa kasar Poland ta tura jiragen yakin da take son ba wa Ukraine domin yaki da kasar Rasha, tana mai cewa hakan zai kara rura wutar rikicin.
A yayin da Ukraine ke rokon kasashen Turai su taimaka mata da jiragen yaki, Amurka ta ki yarda da bukatar Poland na girke jiragen yankinta kirar MiG29 da za ta ba wa Ukraine a sansanin sojin Amurka da ke kasar Jamus.
- Birtaniya ta kwace wa attajiri dan kasar Rasha jirgi
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 19 a Kebbi
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce zai ci gaba da yaki da Rasha har sai abin da hali ya yi.
Ga karin abun da ke faruwa a rikicin na Rasha da Ukarine:
An dauke wutar lantarki a Ukraine
An dauke wutar lantarki a masana’antar nukiliya ta Chernobyl ta Ukraine, cibiyar da aka samu fashewar nukiliya mafi muni a duniya a 1986.
Hakan ta faru ne bayan Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta ce an daina samun bayanai daga tashar nukiliyar da Rasha ta kwace a mamayar da ta yi wa Ukraine.
Ga karin abubuwan da suka faru a rikicin Rasha da Ukraine:
– Tsagaita wuta na sa’a 12 –
Rasha da Ukraine sun amince a tsagaita wuta na tsawon awa 12 domin fararen hula su samu ficewa daga wasu wurare shida da yakin ya fi shafa ciki har da Kyiv, babban birnin kasar Ukraine, da kuma birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwa a Kudancin kasar, inda aka kana tara babu ruwa da watar lantarki.
– An kashe mutum 10 a Severodonetsk –
Akalla mutum 10 sun rasu bayan sojojin Rasha sun bude wuta a kan wasu gidade da gine-gine a garin Severodonetsk da ke Gabashin Ukraine.
– Yakar Tattalin Arzikin Rasha –
Amurka ta kaurace wa sayen danyen man Rasha, “babbar hanyar samun kudaden shigar Rasha.”
Birtaniya ta ce za ta bi sahu kafin karshen wannan sheraka, kasashen Tarayyar Turai kuma sun rage sayen iskar gas din Rasha da kashi biyu bisa uku.
Rasha dai na zargin Amurka da yakar tattalin arzikinta.
– Banda jiragen yaki –
Amurka ta yi watsi da bukatar Poland na tura jiragen yakinta kirar MiG-29 zuwa sansanin sojin Amurka da ke Jamus domin mika su ga Ukraine.
Amurka na fargabar cewa hakan zai kara rura wutar yaki da Rasha, saboda zai “hai haifar da mummunar matsala”.
Amma Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya roke su da cewa, “Gaskiya muna cikin yanayin yaki! Ku turo mana jiragen yaki.”
– EU ta kara wa mukarraban Putin takunkumi –
Tarayyar Turai ta sanya wa sanatocin Rasha 146 da wasu mutum 14 makusantan gwamnatin kasar a jerin mutanen da ta kakaba wa takunkumi.
A yunkurinta na kassara sufurin jiragen ruwan Rasha kuma, tarayyar ta hana tura kudade ta hanyar kudaden Cryptocurrency.
Birtaniya kuma ta kwace wani jirgin sama na kashin kai mai alaka da Eugene Shvidler, wani makusancin Gwamnatin Putin.
– Rasha za ta ki biyan bashi –
Cibiyar Fitch mai bibiyar alkaluman bashi ta ce bisa dukkan alamu Rasha ba za ta cika alkawarinta na biyan bashi ba.
– Zelensky ya turje –
A jawabinsa ga ’yan majalisar dokokin Birtaniya, Zelensky ya bi sahun tsohon Fira Ministan Birtaniya, Winston Churchill, inda ya lashi takobin yin “yaki har zuwa karshe”.
– ‘Nord Stream 2 ‘ta mutu’ –
Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya ce aikin bututun iskar gas na Dala biliyan 12 da ake takaddama a kai, wato Nord Stream 2 ya zama matacce.
– Coke, McDonald’s da Starbucks sun fice –
Manyan kamfanonin abincin makulashe na McDonald’s, Starbucks da Coke sun rufe harkokinsu a Rasha.
Hakazalika kamfanin kade-kade na Universal Music da kumama kamfanin giya na Heineken.
– Putin ya fusata –
Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka ya ce Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya fusata kuma yana iya tsananta hare-harensa a Ukraine, wanda kuma zai shafi fararen hula.
– An kashe sojojin Rasha 2,000 –
Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta ce an kashe dakarun Rasha 2,000 zuwa 4,000 a kusan mako biyu. A ranar 2 ga watan Maris Rasha ta ce sojojinta 498 aka kashe.
– Mutun miliyan 2.15 sun tsere –
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da suka tsere a cikin awa 24 ya kai, wanda ya sa yawan masu gudun hijira karuwa zuwa miliyan 2.5, kusan rabinsu zuwa kasar Poland.
– An cire Rasha daga Vogue –
Madaba’ar Conde Nast ta dakatar da Vogue da sauran wallafe-wallafenta a Rasha saboda dokar haramta labaran karya da gwamnatin kasar ta sanya kan yakin, dokar da ta tanadi hukuncin daurin shekara 15 ga masu saba dokar.