Amurka ta mika wa bangaren adawa dukiyar kasar Benezuela

Gwamnatin Amurka ta ce ta mika ragamar tafiyar da dukiyoyin kasar Benezuela da ke kimshe a asusun ajiya daban-daban a kasar Amurka ga hannun shugaban ’yan adawa, Juan Guaido, wanda shi ne hukumomin Amurka suka amince da shi a matsayin Shugaban Kasa na riko. Sakataren Al’amuran Cikin Gidan Amurka, Mike Pompeo ne ya sanya hannu […]

Amurka ta mika wa bangaren adawa dukiyar kasar Benezuela

Gwamnatin Amurka ta ce ta mika ragamar tafiyar da dukiyoyin kasar Benezuela da ke kimshe a asusun ajiya daban-daban a kasar Amurka ga hannun shugaban ’yan adawa, Juan Guaido, wanda shi ne hukumomin Amurka suka amince da shi a matsayin Shugaban Kasa na riko.

Sakataren Al’amuran Cikin Gidan Amurka, Mike Pompeo ne ya sanya hannu a takardun umarnin a makon jiya, inda suka amince wa Guaido damar amfani da dukiyar kasarsa da ke ajiye a bankunan Amurka. “Wannan takardar shaida ita ce za ta taimaka wa halattacciyar Gwamnatin Benezuela amfani da dukiyoyin kasar domin amfanin al’ummar kasarta,” inji Jami’in Watsa Labarai na ofishin Sakataren Al’amuran Cikin Gida na Amurka, Robert Palladino.

Hukumomin kasar Amurka dai sun jima suna matsa lamba ga sauran kasashen duniya su raba hanya da Shugaban Kasar Benezuela, Nicolas Maduro, inda suka nuna goyon bayansu ga Guaido a matsayin Shugaban Kasa mai jiran gado.

Har ila yau, a ranar Litinin da ta gabata, Gwamnatin Amurka a karkashin mulkin Donald Trump ta sanar da kakaba wa Gwamnatin Benezuela takunkumi dangane da kamfanin mai na kasar, PDBSA. Wannan takunkumi, an kakaba shi ne ga kasar domin hana hukumomin kasar ta Benezuela kaiwa ga dukiyar kasar da ta kai kimanin Dala biliyan bakwai a matsayin kadarori da kuma wasu Dala biliyan goma sha daya a matsayin kudin shiga da kasar ke tsammanin samu a kan kudin ajiyarta na bara.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta