Amurka ta sa tukwuici kan ‘yan al-Shabab

A shekaranjiya Laraba ne Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana aniyyarta  na bayar da tukwuicin dala miliyan 27 ga duk wanda ya ba ta labarin yadda za ta kama shugabannin kungiyar al-Shabaab guda shida.Tukwuicin da ya fi girma shi ne na dala miliyan daya wanda aka sanya a kan shugaban kungiyar Abu Ubaidah.Ubaidah ya maye gurbin […]

Amurka ta sa tukwuici kan ‘yan al-Shabab
Amurka ta sa tukwuici kan ‘yan al-Shabab

A shekaranjiya Laraba ne Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana aniyyarta  na bayar da tukwuicin dala miliyan 27 ga duk wanda ya ba ta labarin yadda za ta kama shugabannin kungiyar al-Shabaab guda shida.
Tukwuicin da ya fi girma shi ne na dala miliyan daya wanda aka sanya a kan shugaban kungiyar Abu Ubaidah.
Ubaidah ya maye gurbin Ahmed Abdi Godane, wanda harin da jirgin saman Amurka maras matuki ya kai ya yi sanadiyyar mutuwarsa a bara.
Mahad Karate, wanda aka fi sani da Abdirahman Mohamed Warsame na cikin ‘yan kungiyar da aka fi nema ruwa-a-jallo saboda zargin da ake yi masa da hannu a harin da aka kai kan wata Jami’a a kasar Kenya, lamarin da ya kai ga mutuwar akalla mutane 148.
kungiyar al-Shabab na ci gaba da yaki da gwamnatin Somaliya wacce Amurka ke mara wa baya.